*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_1⃣1⃣ - 1⃣2⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlightenment and Exhortation our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_*Ina mika sakon gaisuwa ta ga Ahmad (Deedat) da Abdulmalik. Allah ya cigaba da taimaka musu. Allah yasa su gama lafiya. Ameen!*
Aisha kuwa a ranta sai tunanin irin son da sukewa juna suke wanda suka kasa gane suna son junan nasu. Dan yadda ya damu da ciwon nan nata kamar a jikin sa yake. Yana zuwa gida ya kira ta dan ba zai iya fushi da Yasmeen ba. Kusan wannan weekend din anan yayi musu ya cika su da siyayyar kayan yar dubiya. Satin sa uku ya fara shirin tafiya.
Ana ya gobe zai tafi yayo mata waya akan cewa zai zo yai mata sallama tace sai ya zo. Aisha ta kalla ta fadawa idon ta na cika da kwalla dan ko a gida in zai tafiya sai tayi kuka. Hararar ta Aisha tayi tace
"Ki zauna ki kashe kanki wallahi."
Ta mike zata fita. Yasmen ta kamo hannun ta tace
"kiyi hakuri yanzu yaya zanyi?"
"Ki fada masa kawai."
Shiru tayi sai hawaye. Aisha ta juyo taga tana kuka nan ta hau lallashin ta
"Yasmeen ina baki shawara ne dan ina son ki, in yazo ki fada masa kawai."
Shiru tayi can ta gyada mata kai. Nan Aisha tace
"Yanzu kafin yazo ki tashi ki shirya komai daga baya sai ki sanar masa. Yau ba zai zo ba duk yadda kukai kya fada min."
Nan ta mike ta shiga tai wanka ta fito ta shirya cikin sea green din arabian gown tayi kyau sosai da ita. Batai kwalliya ba daga powder sai turare da man lebe ta taje gashin girar ta tai wani irin kyau. Tana zaune taji kiran sa kan cewa yazo. Mikewa tayi ta kalli Aisha. Aisha tace
"Allah bada sa'a."
"Ameen!"
Ta fada tana ficewa.Tinda ta taho hango ta wani abu yaji ya bugi kirjin sa ya buga mai bai taba ganin tai masa kyau irin na yau ba. Ido ya lumshe bai san lokacin da ta shiga motar ba sai da ta tafa hannun ta sannan ya bude idon sa tace
"Bacci kake ne?"
"No ba bacci nake ba."
Ya tsare ta da idanun sa da suke mata kwarjini nan take tai kasa da kanta. Murmushi yayi yace
"Zanje gidan su Billy daga nan ko mu tafi tare ne?"
Kai ta girgiza masa tana jin kirjin ta na bugawa. Kallon ta yayi a ransa yace
"Ya Salam shin me nake ji game da wannan kanwar tawane. Hakika akwai wani boyayyen al amari a tsakanin mu sai dai na kasa gane menene shi. Ko duk tausayin ta da nake ji ne? Bazance so ba dan a yanzu Billy kawai nake mafarki a matsayin matata..."
Wayar sa ce ta dawo dashi daga tunanin da yake. Marzuk ne dan haka ya dauka yana fadin
"Friend yane?"
Yai shiru kana yace
"Wallahi friend ina cikin tsaka mai wuya na kasa sanar da ita abinda ke zuciya ta."
Yai shiru yana jin abinda Marzuk ke fada masa. Yasmeen kuma bugun zuciyar ta ne ya dadu dan bata gane inda zance sa ya dosa ba dan haka yace
"Ka tayani da addu'a yanzu zanje gun ta so nake kwana kusa na aure ta na huta."
Suka cigaba da waya wacce daga nan bata kara jin abinda yake fada ba dan ta lula tunani son ta gano wa yake so. Ta duba ta hanga taga alamar ba da ita yake ba dan cewa tayi zai je gun ta daga nan. Dan haka bata san lokacin da tace
"Wa kake so big bro?"
Juyowa yayi ya kashe wayar yana ganin zallar kishin shi kwance a cikin idon ta, da tsananin sonta. Ido ya lumshe dan bai taba lura da hakan ba. Yaushe Yasmeen ta fara son sa. Yasmeen yarinya ce dan har yanzu batai shekara ashirin ba. Ido ya bude ya sauke akan ta yaga yadda lokaci daya ta sauya masa.
"Billy ce."
Ya fada jikin sa a matukar sanyaye.
"Allah ya sanya alheri."
Ta fada tana bude kofar mota. Tace
"Ina da class Allah kiyaye hanya!"
Ta fice ba tare da ta kara juyowa ba. Da ido ya bita, tana fita wani kuka ya kwace mata da gudu ta karasa hostel dinsu ta fada kan gado tana mai rusa kuka. Aisha dake zaune tana karatu ta mike ta iso gun Yasmeen tana fadin
"Lafiya Yasmeen!"
Cikin kuka tace
"Aisha na fada miki Yaa Fauwaz ba sona yake Billy yake so,"
Ta fashe da kuka.
"Me ya faru?"
Aisha ta fada, cike da tashin hankali. Nan ta kwashe duk yadda sukai ta fada mata ta fashe da wani irin kuka wanda har sai da taji nunfashin ta na daukewa. Kan gado ta fada tana mai danne zuciyar ta dan yadda taji zuciyar ta na mata zafi. Cikin wannan halin take fadin
"Yaa Allah kai ka dauran son yaa Fauwaz, Yaa Allah ina mai addu'a akan ka ciren min shi, nasan ubangiji bazai kunyata ni ba. Kai maji rokan bayin ne...."
ta fada tana mai kara fashewa da kuka. Aisha tace
"Kiyi hakuri nima zan tayi miki addu'a amman wallahi Yaa Fauwaz na sonki sai dai idon sa ya rufe a wani abun ne, amman nasan akwai lokacin da zai zo ya fada maki..."
Da sauri Yasmeen ta tari numfashin ta tana fadin
"Aisha bana son ki kwantar min da hankali akan abin da kika san ba zai faru ba. Kawai ki tayani da addu'a bana son sa Kuma bazan kara sa son sa a raina ba."
dafata Aisha tayi tace
"Addu'a sai iya inda karfi na ya kare."
Dagowa Yasmeen tayi tana murmushin da yafi kuka ciwo wanda dimple din ta suka lotsa nan ta rungume Aisha tana mata godiya. Ita ma Aishan murmushi take idon ta na zubar da hawaye. Haka suka cigaba da kuka. Aisha tace
"Nagodewa Allah da yasa kime fahimta ce da wata ce binsa zatai tayi yana wulakanta ta kuma na kuma ganin kafar sa anan."
Abin sai ya bawa Yasmeen dariya. Aisha tace
"Ke ai ba abar ki bace kalle ki fa. Ai wallahi duk da bansan billyn nan ba nasan kin fita komai dan duk wacce tafi ki wani abu wallahi ba kyau zatai ba. Kiga yadda samari baga dalibai har lectures ke son ki kin tsaya kina kin kula su. Wallahi ki tsaya kiyi zaben da zai rikita Yaa Fauwaz."
Nan ma dariya tayi dan Aisha badai abin dariya ba. Dan haka sai ta dan fara jin sanyi.Fauwa kuwa duk jikin sa ne yayi sanyi dan daga nan gida ya koma ya kasa zuwa wajen Billy. Shin me Yasmeen ke nufi ji yai kwakwalwar sa duknta doke. Har washe gari jikin sa a sanyaye yake, ya so yaje yaga a halin da take amman tafiyar safiyya ce. Dan ko Billy sai waya sukai. Zuciyar sa na fada masa Yasmeen son sa take amman sai karya tata yake dan shi Billy yake so. Duk da yasan da wuya Yasmeen din son sa take. Da yai trying number ta ma duk a kashe yake jin su. Bai san a black list ta saka shi ba. Da ya sauka a inda zai je ma yai ta kiran ta taki shiga dole ba yadda zai yi ya hakura. Sai Billy ya kira suka taba hira.
Yasmeen kuwa hankalinta ta maida kan karatun ta sosai ga addu'a ba dare ba rana, azumi ma duk Monday and Thursday sai tayi ga sallar dare sosai taji santi da raguwar abinda ke damun ta. Inda ta cigaba da karatu ba wasa. Yanzu haka suna level 300. Sun gama exam lafiya sun dawo gida sai data dawo gida ne ma take jin labarin sa, hutun da ta samu tayi ziyara dan gidan yan uwa duk taje har maiduguri taje ta gaida kakanin ta sunji dadi sosai tana dawowa ta fara shirin komawa ckul. Ranar Friday Aisha ta dawo dan haka a gidan su Yasmeen ta sauka dan zasu koma ran Monday gaba daya. Kwana sukai suna hira har gidan Anty Bintu duka je da yan uwa. Kuma Aisha tace tayi kiba dan yanzu ba wannan ramar Mommy ma taji dadin yadda taga ta sake ta danyi kiba.
Billy kuwa har ta gama service ta samu aiki a gidan TV kullun cikin shiga take ta kara wayewa da gogewa. Fauwaz kuwa kullum Yasmeen na ransa amman jin ya kira be samun ta duk yabi ya damu sun gama wasan su wanda ko da ya samu hutu be dawo ba umarah ya zarce.
Karatun Yasmeen sai kara gaba yake tun da gashi yanzu har sun fita asibiti . Duk farmakin da samari ke kawo mata bai sata bada fuska ba tace suyi hakuri karatu take yi. A gida ma ba a takura mata dan duk tunanin su da Fauwaz za'a hada su aure. Sai da Fauwaz yai shekara bai zo gida ba, duk da billy na binsa duk wata kasar da zasu buga wasa, yanzu haka ma suna kusa da final dan a Nigeria za'ai final. Inda da suka buga Nigeria ta cinye dan haka Billy har Party ta shirya masa Dad din ta har da gift ya bashi. Wannan abun yayiwa Fauwaz dadi sosai.
Washe gari suna gidan Marzuk bayan sun gama cin abincin rana Marzuk yake tsokanar sa kai dai kaki kayi aure ko gashi nan Madam na da ciki na uku. Dariya Fauwaz yayi. Marzuk yace
"Ga dan iskan ci. Allah ya taimaka Yasmeen tasan halin ka na gun ci zata iya amman da wata ce da an shiga uku dan kuwa zatayi abincin zaka cinye bazata samu ba."
Fauwaz yace
"Me kake fada ne wai wacce Yasmeen din?"
Marzuk da bai gane ba yace
"Ur priness mana."
Dariya Fauwaz yayi yace
"Me kake nufi ne? Wa ya fada maka Yasmeen zan aura da har kake cewa ta saba."
Marzuk sakin baki yayi yana kalon ikon Allah dan shi har ga Allah ya zata Yasmeen, Fauwaz yake so, dan rannan da ya kawo masa maganar ma ita ya kawo zai sanar wa yana son ta. Fauwaz yace
"Ni son yan uwan taka nakewa Princess bana aure ba ko soyayya ba."
Marzuk yace
"Wallahi Fauwaz karya kake. Ko a kwayar idon ka akwai son yasmeen."
Dariya Fauwaz yayi yace
"Son Billy dai."
Ido Marzuk ya zaro yace
"What? Wacce Billyn?"
"Wacce Billyn ka sanni da ita."
Fauwaz ya fada a fusace. Sassauta murya Marzuk yayi yace
"Friend ka tsaya kai tunanin irin uwar da zaka zabawa ya'yan ka. Ban ce kar ka auri Billy ba amman kasan Yasmeen na son ka kuma in har ka'kita ka zalince ta dan ka hanata kula kowa gashi ka korar mata masoyan ta. Duk a tunani na son ta kake ashe ba haka bane. Yarinya mai hankali ga nutsuwa ga ilimi both. Ni dai ka tausayawa Yasmeen."
Murmushi Fauwaz yayi yace
"Ita tace maka tana sona."
"Ai ba sai ta fada ba."
Mikewa Fauwaz yayi yace
"To ta san da zancen Billyn ma, kuma tasan ita zan aura dan haka ka rabu dani."
Mikewa Marzuk yayi yace
"Aboki na bana son kayi asara. Dan in har ka rasa yasmeen nasan kayi babbar asara wallahi."
"Sai anjima!"
Cewar Fauwaz ya fice a dakin. Da kallo Marzuk ya bishi yace
"Ikon Allah ni kam zan tayaka da addu'a Akan Yasmeen dan in ka rasa ta kunyi rashi babba."Don't forget to vote nd comment
Antty ce!!!

YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasyLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.