73-74

517 30 0
                                    

*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_

7⃣3⃣ - 7⃣4⃣

Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*

Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and  Exhortate our readers)_*

Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_

*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy na da Mommy nah)*


Da suka koma gida, kwanciyya kawai tayi dan sam bata jin dadin jikin ta. Ai kam tasha bacci.
Kan ta tashi har an hada mata ruwan wanka da abinci kala kala. Wanka tayi tayi sallah sannan ta fito nan taci abinci ta sha maganin ta sai sannu suke mata. Yadda taga sun tada hankalin su yasa ta danne komai da bawa kan ta kwarin gwiwa ta cigaba da addu'a akan al amarin nata.

Sosai take shan maganin ta amman ita ciwon kamar dada mata ake yi. Dan haka sosai ta kara mikewa wajen kai kukan ta ga Allah.

Ai kam ta dan samu sassauci ba laifi dan tana fitowa yanzu falo su sha hira ganin yadda kannen Mamin ta da Ya'yan su suke akan ta yasa ta kara warewa tasake a cikinsu dan akwai sa'anin ta sosai. Sai yan samari da wasu na da aure wasu kuma ta girme su. In ka gansu kamar yadda suke dasu Yaa Ishaq haka suke abin sha'awa dan da bata da lafiyar nan tare suke jinya.

Satin ta daya ta watsake sosai dan haka, ta fara shirin kai ziyara gidan yan uwan su. Gidan Anty Yagana suke je nan suka hadu da yan uwan ta yan mata dan haka sun ji dadin gidan. Anan taga yadda suke zuba soyayya da samarin su sai ta tuna da wayar ta dake cikin jaka rabon ta da ta kunna tin ranar da sukai waya da Ahmad. Mikewa tayi ta dauko wayar.

Messages ta gani na shigowa ba adadi bata bi ta kansu ba ta kira Aisha. Haka suka gaisa suka sha hira amman sam bata kawo mata zancen Ahmad ba itama haka. Suna gamawa ta kira Mommy nan suka gaisa Mommy tace tana kiran ta taki shiga tace wallahi Mommy ina cikin hada hada ne.

Mommy tce
"Ki sake yan uwan kine kinji Yasmeem! Ki gaishe min dasu dukka."
"Zasu ji?"

Sukai sallama. Ta kira Mie Mie sannan ta kira Ummi itama cewa take ta sake yan uwan tane fa. Bayan sun gama ta kira Mama tana mata shagwaba wai tayi misisng nata. Mama tace
"yar nema ai ga wata innan taki nan anan. Suna lpy?"

"Lafiya lou!" Ta bawa Anty Yagana suka gaisa. Sannan sukai sallama. Ta ajiye wayar. Bata jima da ajiye wayar ba sai ga kiran Yaa Fauwaz nan wanda kullum sai ya kira wayar baya samu duk ya shiga damuwa ya rame dan ya rasa sukuni akan Yasmeen.

Dauka tayi tace
"Yaya na ya kake ya gida?"

"Alhamdulillah Yasmeen princess I miss you."
Murmushi tayi tace
"Yasu Anty na?"

Dan tsaki ya saki yace
"Tin biki na koma. tana nan!"

"Ayya kace missing din Anty ne yai maka yawa ko?"
"Princess ni banyi missing din Anty ki ba, missing dinki nayi!"

"Yaa Fauwaz kenan! Ya garin da kake?"
"Uhmm ina maganar nayi kewar ki kina tambayata wani garin da nake. Meyasa kike kashe wayar ki ne? Yana daga cikin abun da ya saka ni a damuwa na rashin Jinki."

Ni da Yaa FauwazWhere stories live. Discover now