*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_8⃣9⃣ - 9⃣0⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and Exhortate our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy na da Mommy nah)*
------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Sosai Fauwaz ke jin jiki, wanda Marzuk yace zai fada a gida yace kada ya fada ya bari a gama bikin sai su sani amman yanzu hankalin duk zai tashi. Haka suka zauna kullum Marzuk na gun Fauwaz maganin yake sha amman kamar ba sha yake ba dan jiki yaki gaba yaki baya.++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++
Abbas kuwa ana can ana ta murna Yasmeen ta zama tashi. Duk da Hajiyar sa tace ba sai yayi komai ba amman sai da ya hado kayan lefe wanda suka ci gidan wanda hajiya ta hada kuma Hajiya tace akai musu kawai. A lokacin kuma aka aika da kayan lefen Yasmeen. Akam an musu tukwici dan suma dukiya mai yawa suka kawo. Nan aka tafi ana fadin sai biki kuma.*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*
Sauran sati biyu suka gama exam dan haka suna dawo wa aka tafi maiduguri da ita dan za ai mata gyara. Batun anko kuwa duk Aisha ce ta fitar ta rabawa course mate din su, sannan yanzu da suka gama ckul anan gidan su Yasmeen ta zauna dan zasu rabon kati nan biki da jiran lokacin biki.Kwanan su Yasmeen goma suka dawo in kaga yadda ta koma sai ka zata gyaran jikin watanni akai mata. Tayi kyau ta dada haske ga wani kamshi dake tashi a jikin ta ko yaya ta motsa. Mommy da ta ganta sai masha Allah take fada. Aisha kuwa sai yabon kyan da tayi take.
Sam bata da damuwa sai guda daya tin da taje Maiguduri take kiran Yaa fauwaz bata samun sa yanzu ma haka sai abin ya dame ta da ta zauna sai tunanin ko yana ina ko lafiya amman sai ta zata ko yana can wata kasar amman fa tana yawan mafarkin Yaa Fauwaz wanda duk yake kashe mata jiki.
Dan haka ranar da suka dawo da daddare ta saka driver ya kai ta gidan sai dai maigadi yace mata Billyn bata nan da tace mai gidan fa? Sai yace gaskiya yana jin baya garin dan yau kusan sati baya gida dan haka suka juya jikin ta a sanyaye.
Yadda suka tsara bikin ranar laraba za ai bridal shower sai alhamis za ai kamu Friday ayi dinner, asabar a daura aure ayi yini akai amarya.
Sam bata jin dadi don zuciyar ta har wani nauyi take mata ga wata faduwar gaba da take fama da ita. Daurewa kawai take yi yan gida kuwa sai hada hadar biki suke yi dan ji suke kamar yanzu zasu fara biki a family din ko da yake ita ce 'ya macen da za a fara aurar wa. Dan haka sai rawar jiki suke akan bikin da tsare tsare dan an gama tsara komai da komai lokaci ake jira kawai. Mommy kuwa uwar Amarya sosai ta tashi akan gyara yar ta.
Ana ya gobe bridal shower, zaune take a falon Anty Binta gidan Marzuk yar garin su Yasmeen Maiduguri ce ke mata lalle wanda tare suka zo dasu Asabe da ya'yan kannen Mamin ta. Dakin cike yake da su Asabe da su Aisha ana ta hirar bikin da ta duniya abin sha'awa kasan yanmata in an hadu. Gyaran jiki aka gama yi mata aka saka jan lalle bayan yayi aka daura baki bakuga yadda yayi kyau ba da yake fatar takara kyau haske da tsantsi kamar ka tafa ta fashe dan yadda tai taushi. Lallen ya zanu dan duk wanda ya gani yasan amarya ce da kanta. Gashin kan ta an gyara shi batai shampoo ba an wanke sai kamshi yake ya bazo a gadon bayan ta.
Wani abu Anty Binta ta miko mata tayi gun bakin ta dashi dan an mata bakin lalle a hannun ta baza ta iya rikewa ba. ta bata fuska tace
"Ni dai dan Allah kiyi hakuri!""Kaniyar ki wallahi zan fadawa Momny!"
Baki ta turo ta bude bakin ta bata ta shanye ta bar wajen. Baki take tabewa na alamar bata so. Kullum sai an bata abubuwa kala daban daban ta sha wani ma a toilet take zubar wa in ta faki ido su Mommy da Aisha, Aisha tai dariya tace
"Yar banza gaba da kanki zaki na nema!"Asabe tace
"Ni banga wanda akewa gata yake gudar masa ba.""Ke dai bari Anty Asabe yadda Yaa Abbas ya kagu nasan Anty Yasmee...."
Shiru tayi saboda wani kallo da taga Yasmeen na mata."Tashi ki bamu waje!"
Yasmeen ta fada. Sim sim ta mike ta fita.Aisha tace
"Ke Yasmeen menene haka?""Baki ji me take fada bane?"
Yasmeen ga fada."Hmmm raina ta kikai dan kinga kanwar kice ko? To wallahi kila ta fiki sanin dawar garin!"
Share maganar Yasmeen tayi tace
"Antu Asabe yaushe zaki min kitson ban son tarewa kai na ba kitso wallahi!""Saboda me to?"
Aisha ta fada
"Wanka mana!"
Yasmeen ta bada amsa.Ido Aisha ta zaro tace
"Yau na shige su yasmeen har kin shirya kenan!"Murmushi Yasmeen tayi tace
"Hmmm lallai kada na shirya kenan ko? Hmmm ai kamar yadda Siyama take fada ne Abbas ba zai kyale ni ba. To wai akai ka gidan ka a zamanin nan miji bai nemeka ko ya saka ka wanka ba ai ka tuhumi kanka. Ni wallahi na saddakar dan yadda Abbas ke rawar kan nan ina tausayin kaina wallahi!" (Hhhhh My besty statement kenan! Indo nah how far?)Shewa yan dakin sukai ta dan harari kannen ta dake dankin su Aisha da Anty Asabe da wata kawar Anty Asabe tace
"Kai Anty!""Lallai Yasmeen wallahi kinyi gaskiya kace in muka zo ran Sunday komai ya wakana!"
Shiru tayi wa Anty Asabe kawai. Dariya tayi yace
" 'yar kanwa ta kenan. Zan wa Abbas kashe din kada ya baki wahala yabi dake a sannu!"Ido ta zaro tace
"Dan Allah kada kiyi masa!"
Dan tasan tsab zata aika fa."Oh wahalar kike so kenan ko?"
Anty Asabe ta fada."Ba haka bane. Ki gane dai kwai!"
Tayi dariya tace
"Wai sai yaushe zasu zo ne?""Yau zai baro Can yaje garin su Adamawa daga can gobe zasu taho nan ai."
"Allah kaimu toh!"Amin!"
Suka amsa gaba dayan su.Nan suka cigaba da hira Anty Asabe na daga gefen Yasmeen na kara koya mata abubuwa a haka har ta mike zatai sallah yasmeen ta jingina a kujera ta lumshe ido.
Ba wanda take son gani sai Yaa Fauwaz, shin ina. Shiga amman kila tasan suzo yau ko gobe. Tana jingin nan ta ce a ranta
"Oh wai ni Yasmeen ni zanyi aure! Allah nagode maka."Kirjin ta ne taji ya buga ras abinda yasa ta bude ido kenan tana kallon yan dakin dake ta hirarsu. Aisha ta kalle ta tace
"Har kin fara tunanin first night din ne?"Murmushi kawai tayi. Nan mai lallen tazo tana kan kare mata tana gamawa ta mike ta shige bedroom din Anty Binta tai wanka ta dauro alwala. bayan ta fito ta saka riga ta hau kan sallaya tayi sallah da batayi ba tana nan zaune sai ga Aisha nan ta shigo dakin rike da wayar ta tana fadin ana ta kiran ki na shigo kina wanka an miki text. Amsa tayi. Aisha ta zauna a kusa da ta tace
"Yasmeen lafiyar ki kuwa? Duk kin canja ko dai duk tsoron haduwar ku kike?"Murmushi Yasmeen tayi ta shafa addu'a ta dauki wayar ta bude. Abbas ne ya kira ta sau uku sai Text da yayo mata. A ranta tace
"Sun sauka kenan!"Zata bude text din kenan sai ga kiran sa ya shigo wayar murmushi tayi ta dauka. Da sallama.
"Maryama!"Ya kira sunan ta muryar sa a rikice. Gaban ta taji ya fadi krjin ta ya tsanan ta bugu kan a hankali ta amsa da
"Na'am! Kun isa lafiya!"Ji tayi kamar yana sheshekar kuka dan haka tace
"Lafiya?"*Antty ce!*

YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasyLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.