35-36

604 39 0
                                    

*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_

3⃣5⃣ - 3⃣6⃣

Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*

Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and  Exhortate our readers)_*

Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_

Acan ma Billy tayi kyau cikin irin shaddar Yaa Fauwaz amman tata blue ce ta saka farin mayafi da takalmi ba karamin kyau tayi ba an musu hotuna sai karfe daya suka bar gidan suka tafi can gida.

A gida kuwa tinda Yaa Fauwaz ya fita take jin wata faduwar gaba amman haka ta danne, lokacin da ta tabbatar an daura auren kuwa da yake gidan a cike yake ban daki ta fada ta sha kukan ta san ranta sannan ta fito ta shiga cikin mutane kamar ba ita tai kuka ba.

Yan uwa ana ta mata Allah sanya alheri dan ance in an mata kamar shi akai wa dan yadda suke. Ta fito daga gidan Abba kenan sai ga su Yaa Fauwaz sun dawo tinda ta daura idon ta akan sa ta dauke kai dan wani haushin sa take ji a yanzu kawai dan gani tayi daga daura auren da akai sai wani washe baki yake. Kai ta dauke zata shige ciki ya kwada mata kira. Ba yadda zatai ta juyo tazo gun sa. Nan ta gaisar da abokan sa a ciki har da Abbas da ya kafe ta da ido ya kasa ko motsi. Da me camera suka zo dan haka ya yafito shi yace yai masu. Sai da yai musu wajen kala goma sannan tace ya isa ya shiga gida aka dinga yi da iyaye mata da yan uwa.

Karfe uku za ai yinin gida a babban compound din duk an gyara wajen anyi decoration an zuba kujeru har jama'a an fara zuwa. Yasmeen kuwa tana can ana mata kwalliya duk ranta a cunkushe dan har ga Allah dan Mommy ta nace sai anyi ne. Tayi kyau iya kar kyau ta saka wani less army green wanda akai wa adon pink da milk aka daura mata wani pink din head ta yafa pink din mayafi tai kyau dan in ka ganta ka zata amarya ce.

Haka aka fara yini ana ta hidima da mutane. Tana cikin yan uwa anan ta hidima (kada ku manta daga gidan Alhaji Babba da Alhaji Karami ba 'ya mace daga Yasmeen sai siyama sai yar da Ummi ke goyo yanzu dan haka dukkan su maza ne sai 'kanin Baba da yake da jikoki mata da maza.)

Shigowar sa gidan ya ganta cikin yan uwan ta maza ana ta dariya nan suka saka shi a gaba suna ta tsokanar sa Ango. Ita dai tana gefe ganin wani jikan kanin kakan su Abubakar yana mata magana har da dariya ya bata masa rai. Wannan yasa yai cikin bangaren sa yana zuwa ya dau waya ya kira ta.

Bata so barin yan uwan nata ba haka ta tafi tana turo baki ta isa dakin sa ta same shi akan kujera yai dai dai dashi. zama tayi fuska ba fara'a. Murmushi yayi yace
"Oh dan na kira ki shine kike bata rai!"

Bata kula shi ba yace
"Shikenan tashi kije!"
Mikewa tayi ta fara tafiya. ganin da gaske take yasa yace
"Kin hadan kayan ne?"

Juyowa tayi fuska a hade tayi hanyar bedroom din sa. Murmushi yayi yace
"Baza kije din ba."
Ya mike ya koma cikin yan uwan sa. Aka cigaba da hirar dashi ita kuma tana can tana hada masa kayan sa a cikin manya manyan akwati nan sa. Har akai magariba bata gama ba anan tai sallah sai isha'i ta gama ta fito dan Yaa Fauwaz ba dai kaya ba wasu ma basa su yake ba dan sai yai dinki bai fi ya saka sau daya ba ya ajiye dan yafi son saka kananu kaya. Dan durowar dakin sa bayan ta bango har da ta furnitures din sa banda kwatuna. Nan ma bata taba dayar durowar ba. Tana sallah isha'i ya shiga dakin bandaki ya shiga yai wanka. Tana shirin fita ya fito daure da towel wannan yasa tana ganin sa tadada sauri har da tuntube kamar zaka fadi. Da kallo ya bita yana girgiza kai.
"Ki jira ni!"
Ya fada da karfi. Tsaki tayi ta zauna. Minti goma sha biyar ya diba ya fito cikin wata milk shadda wacce akai mata aiki da brown zare tai masa kyau sai kamshi yake.

Ni da Yaa FauwazWhere stories live. Discover now