57-58

486 34 0
                                    

*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_

5⃣7⃣ - 5⃣8⃣

Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*

Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and  Exhortate our readers)_*

Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_

*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy na da Mommy nah)*

Da kyar yayi bacci kafin safiya yaji sauki da dama dama. Nan yai wanka ya shirya ya fito falo yana kunna data. Sako ya shigo masa ta Email din sa akan  wani wasa sa zasu tafi a ranar da dare, Da Bai son ya tafi amman yanzu ya gwammace ko wane kasa zasu zaije. Mikewa yayi ya leka dakin ta bata nan, nan ya dauki waya ya kira ta. Tana dauka tace
"Lafiya?"

"Ina kika tafi da safen nan?"
"Ban sani ba. Ko kana zaton akan ka zan ajiye aiki nane?"

"Ban son raini fa Billy wai meyasa kike haka ne? Kina da ilimin addini kuwa?"
"Ban dashi kuma bazan yi shi ba. Na gaji da rayuwa da kai Fauwaz na gaji sam auren nan ba kwanciyar hankali a ciki sa ka sani na yadda ko wanne hukunci ka ga dama ka dauka, dan ba zan iya cigaba da rayuwa dakai ba. Dan haka ni ka barni na huta kawai. Dan ka sani ba zan zauna kana juya ni  yadda kake so ba. Kasan na fada maka tin lokacin baya ko?"

Zuciyar sa yaji tana tafasa bai san lokacin da ya zare wayar a kunnen sa ya tarwatsa ta anan falon saman tiles ba. Dakin sa ya shiga ya hau hada kayan sa ya fito ya shiga motar sa, ya fice a gidan da gudu tsiya.

'Kawarta dake zaune a kusa da ita tace
"Hmmm Billy kenan laifin kine ai ba yadda banyi dake ba akan kada kiyi aure amman ya rudeki da dadin bakin sa kika yadda kika aure shi, kalle ki fa har ya fara tsofar dake, mu da bamu da auren kina ganin mu nan bamu da tension bare wata matsala. Amman ke kuwa kullum cikin matsala. Ke ni ko mahaifina yace zaina takuran tini zan ya kice shi bare wani namiji wanda ba tare aka haife mu ba. Shawara daya zan baki shine gaskiya, ki nemawa kan ki mafita tin yanzu, wato ki kwaci yancin ki har yanzu da ragowar kuruciyar ki kisan yadda za ai ki kwaci yancin ki malama. Sai kace ba wayayya mai ilimi ba kin zauna anan miki abinda akewa marasa ilimi. Ki yage wannan auren na Fauwaz, ni ban ga me kika gani kika makale masa."

Jikin Billy yai sanyi dan tasan Fauwaz miji ne na nunawa sa'a. Dan ko wace mace zata so samun Fauwaz.
"Ba za ki gane ba ina son Fauwaz fa, dan Fauwaz yana qualities da baiwa da hankali ni da nake tare dashi na san da haka. Kuma ko wacce mace nasan zataso ta samu miji kamar sa."

"To ai sai ki zauna, yayi ta azabtar dake, ke kika ga zaki iya. Yadda kike din nan wallahi zaki samu wanda yafi Fauwaz daukaka da kyau da kudi, ni dai nasan ke ba kudin sa kikewa ba kyau ma ai ba zai nuna miki ba. Sai dai ko dan celebrity ne shiyasa wanda ba a iya kasar mu Nigeria ba aka san shi. Sai dai dan haka amman kika sani ko ki nan gana ki auri shugaban kasar wata kasa ma. Bama ta mu ba dan ke ba kalar yan kasar nan bace."
Shiru Billy tayi tana tunanin shin ta dauki shawarar Kawar tane ko kuwa. Dan tasan Fauwaz karshe ne wajen nuna mata soyayya da kula da tarairaya da iya zama bar shi dai da takura in yana bukata sai kuma akan han aikin ta da shigar ta. Amman in babu wadan nan abubuwan Fauwaz ya gama haduwa daga kallo daya zai sace maka zuciya bare kuma ya furta maka ai ka gama. Ajiyar zuciya ta sauke, Wata zuciyar ta na fadin ta dauki shawarar 'kawartata wata kuma na gargadin ta. A haka suka shiga ta dau lecture tana fitowa tayi gun aiki.

Ni da Yaa FauwazWhere stories live. Discover now