*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_8⃣7⃣ - 8⃣8⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and Exhortate our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy na da Mommy nah)*
Mommy cikin daga murya da firgici tace
"Yasmeen fa kace!"Dagowa yayi ya kalle ta. Fuskar Mommy a hade tace
"Me shekarun baya ka fada min akan Yasmeen? yanzu kuma yaushe kuka fara soyayya? To ka fita a ido na in rufe, In Yasmeen ce ma ta maka nisa, dan kasan an bada ita har bikin bai fi sauran kwana ashirin da daya ba."Kai yake girgizawa kirjin sa na bugawa da kyar ya dafe kan sa dake juya masa yana ambatin
"Innalillahi wainna illahir rajiun."Jikin sa har wani irin shaking yake yi sam Mommy bata kalle shi ba bare ta san a halin da yake ta mike tana fadin
"Ka tashi ka ban waje shasha kawai!"Tayi cikin daki. Yana zaune tazo ta fice. Ya jima agun ya rasa me yake masa dadi ya rasa wane tunanin zai yi da kyar ya mike ya fita a dakin. Bangaren Alhaji Babba ya nufa.
Alhaji Babba tinda ya d'ago ya kalli Fauwaz yaga ya rame duk ya zama wani iri, daman tinda yazo wajen sa a office ya ga ya rame amman na yanzu har yafi na baya. Dan haka cikin damuwa ya ce
"Baba na baka da lafiya ne"Kansa yai kasa dashi ya kara gaisar dashi dan duk gaisuwar da yake masa baya ji. Amsawa yayi jiki ba gwari.
"Me yake damun ka Fauwaz ace baka da lafiya kayi irin wannan ramar bamu sani ba. Yaushe ka dawo? tinda baka fada mana tafiyar ka."Kansa a kasa yace
"Ayi hakuri Alhaji."Alhaji Babba yai shiru, yana nazarin yaron. can ya nisa yace
"Me yake damun ka?""Ciwo dai nayi amman naji sauki dan Allah wata alfarma nazo nema a gun ka."
Kai Alhaji Babba ya gyada yace
"Tame fa?""Alhaji daman alfarma nake so abani auren Yasmeen!"
"Wacce Yasmeen da an kawo kudin auren ta lokaci kawai ake ji Fauwaz? Gaskiya ba zan iyai maka wannan alfarmar ba dan Yasmeen ita ta zabi miji kaima a lokacin ka bamuyi maka dole ba zabin ka muka amsa haka nan dan uwan ka Nazir shima zabin sa muka amsa. Dan haka ba wanda zamu yiwa dole tinda tin farko bamuyi ba dan haka nan gaba ma baza muyi."Hawaye yaji yana zubo masa. Alhaji Babba yana gani yace
"Fauwaz ka makara na jima ina jiran wannan lokacin amman baka zo ba kaga yanzu kazo a kurarren lokaci, lokacin da Yasmeen ta riga da tai maka nisa, kar ka manta tin farko naso hada ka da yar uwar ka amman ka'ki, saboda ka kawo wacce kake so kuma muka amsa muka maka abinda kake so, kaga itama ta kawo wanda take so kaga ba a 'ki zabin ta ba itama dole a bata dama dan ba zamu danne mata hakkin ta ba. Dan haka sai dai nace kayi hakuri Allah yayi ba matar ka bace,"Kasa magana yayi sam yana durkushen mommy ta shigo ta kalle shi ta watsar tace
"Me yazo yi anan ba dai maganar da ka kawon ka kawo masa ba. Wallahi Fauwaz ina fada maka ka fita a ido na in rufe. Wato sai yanzu kasan kana son Yasmeen din ko? To wallahi Yasmeen tafi karfin ka dan ko ace bata samu miji ba bazan yadda ta aure ka ba a baya me kace kai ba soyayya tsakanin ku yanzu kuma soyayya ta zo? Alhaki ke bin ka wallahi kuma kadan ma kagani wallahi. Ka tashi ka bamu waje kuma wallahi naji maganar nan agun wani sai ranka yai mummunan baci kaji na rantse ko?"
YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasiaLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.