13-14

575 38 1
                                    

*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_

1⃣3⃣ - 1⃣4⃣

Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*

Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlightenment and  Exhortation our readers)_*

Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_

*Sakon gaisuwa gareki Aisha. Wannan page din naki ne. Allah ya shige gaba ya kare ku. Ameen*


Washe gari da yamma ya isa gidan su Billy ta waya ya sanar mata dan sunyi zasu fita. A shirye ta fito sanye da dogon wando da body hug din riga wacce duk surar ta ke a bayyane sai wata transparent din after dress wacce da ita da babu duk daya. Ta kama gashin kan ta tayi parking din shi sai dan mayafi da ta yafa a kanta duk rabin kanta a waje wayar ta ce kadai a hannun ta. Ta saka takalmi mai tudu ta ci uwar make up a fuska. Ta fito tana tafiya kugun ta kamar zai karye. duk masu aikin gidan su maza kallon ta suka tsaya yi, fauwaz dake bakin gate cikin mota ya hango ta, ido ya kura mata yana mai yaba surar ta. Ji yake kamar yai tsuntsuwa ya taro ta. Ya komar da kansa jikin kujerar yana kallota. kirjin sa na harbawa da karfi saboda wani abu da ke son fin karfin sa. Yayi zurfi a tunanin ta yaji tana masa knocking unlock yayi ta bude ta shiga. Kura masa ido tayi tare da lankwasar da kai tace
"My Fauwaz ya kake?"
Yayi dan murmushi yace
"Kalou nd u?"
Tayi murmushi ta kullon kofar. Motar y cilla kan titi gami da kokarin saka wata waka ta Simi ido ta lumshe dan tana tana son wakar sosai. Can munjibir park suka isa sai da suka zagaya wajen sannan suka samu waje suka zauna. Kallon ta yayi cikin so da kauna sannan ya fara bata labarin sa tin daga yadda yake son ball a gida ba a so har yanzu da yake cikin sana'ar sosai. Billy naji tana dariya in ya fadi wani abun.

Can ya kira sunan ta da wani irin sauti abinda yasa ta bashi duk kan hankalin ta. Kallon ta yayi ido ya kanne mata yace
"Wai billy wane irin feeling kike ji game dani?"
Dubansa tayi cikin rashin fahimta tace
"Kamar yaya?"
Kafe ta yayi da ido yace
"Kada dai kice min baki gano ina son ki ba. Bayan na gano hakan acikin idanun ki."
Kara shiga mamaki tayi dan har ga Allah bata gane mai yake nufi ba dan haka tace
"Me kake nufi? Meke faruwa wai?"
Shima mamakin ya shiga yace
"Billy wai zaki ce baki gano ina son ki ba tin tini."
"So!!"
ta ambata cikin wani yanayi. Sannan ta kuma fadin
"Wane irin so kuma Fauwaz?"
Gaban sa ne ya yanke ya fadi ace
"Ya salan!" Ya dafe kai sannan ya dago yace
"Kina tsokana ta ne billy, to in ma baki gane ba ko baki sani ba na fada mki yanzu ina son ki kuma da aure."

Wani mamakin ta kara shiga, tace
"Fauwaz kenan. Da ina kallon ka wayayye ashe bashi vane. Kai baka san friendship ba baka san soyayya ba. Lallai to ni a aboki na dauke ka in kaga zaka iya to, amman wai muyi aure bai taso ba. Daman maza da haka kuke fakewa ku cuci mata, to ni dai gaskiya mucigaba da friendship kawai."
Da kallo yake bin ta dan ba karamin mamaki maganar ta ta bashi ba. Dan haka yace
"Karya kike Billy kina sona sai dai baki san so bane, amman kina so na. kiyi hakuri muyi aure ni ba irin mazan da kike tunani bane zan kula dake."
Ya karasa maganar cikin lallashi.
"A'ah Fauwaz ka bar zancen nan. Kai kanka kafi sakewa yanzu, in kuwa kai aure duk wannan kulawar da mukewa juna duk denawa zamuyi kullum cikin fada."
Kai ya girgiza yace
"Billy baki fahimci aure ba amman duk abinda kika fada ba haka bane, wasu ke bata wasu.  Ni ma da ban da ra'ayin aure sai da na hadu dake, please ki daure muyi kinji."
Itama kan take girgizawa dan sam bata yadda ba dan haka tace
"A'ah fauwaz kaga ko 30 years banyi ba kake min zancen aure degree daya fa nayi sannan nifa a tsari na banda ra'ayin soyayya bare wani aure.  Kai ma ka cire zancen soyayya bare wani aure ma!"
ta karasa maganar cikin lallashi duk dan ya bar maganar. Kai ya girgiza yace
"A'ah Baki fahimta bane in kinga ana samun sabani a gudan aure to tunda ba su fahimci juna ba. Kizo muje gidan aboki na marzuk ki ga zaman su abin sha'awa da burgewa."
Yar dariya tayi tace
"Kaga ko abinda nake fada maka kenan in kaga ana zaman lafiya most of the time matar ke wahalawa mijin. Kullum zatai masa girki ta gyara masa gida, ta kai masa ruwan wanka, sannan tai ta haifar masa yara. in yaran sun girma ya fita iko dasu, to indai nace zata yadda tai ta aikin gida wanke wanke shara da sauran su wannan ke sa nan da nan ta tsofa bama haihuwa wacce ku hausawa kuke son ta kamar me ni kam sam ban son tsofa tin yanzu. Wannan ke sa suke zaune lafiya kullum shi yana waje yana sha'anin sa kuma yana dawowa sabo wani lokacin ma miji bai damu da matar cimar ta ba bare har tayi dan kyau. Ka sani babu namijin da zanwa wannan bautar domin duk abinda yayi zan iya yi akan me zan zauna yana juya ni. A hana ka fita ana barin ka da bacin rai, in zaka iya cigaba da alaka dani as we are now is ok, dan I just love u as my superstar in my best sport that is football."
Sam shi ba wannan abubuwan ke damun sa a ran sa ba cewar ba zata aure shi ba shi ke damun sa dan su kalamanta duk basu dameshi ba dan idon sa ya rufe kawai son auran nata yake yi dan haka cikin karaji yace
"Shut up Billy!  Muddin kina son mu'amala ta dake sai dai ki aure ni sam bazan iya cigaba da mu'amala dake ba don ina son ki....."
"So what?....."
Ta katse masa maganar da yake yi,
"So what? Idan muka rabu tare aka haife mu."
Ta mike a hasale ta nufi hanyar da suka shigo.

Ya bita da kallo kamar kirjin sa zai fito saboda yadda yake buga masa ga azaba da radadi, bai taba xaton haka zai faru ba. Bai taba zaton zata ki yadda da kudurin sa ba.  Ya gama sakan kancewa da cewar tana son sa, za kuma ta aure shi.  Nan ya fada ciki tunani can nesa ya hango ta tana tafiya a hankali kamar ba son tafiyar take ba, mikewa yayi da sauri yana kwada mata kira amman taki juyowa kamar ba da ita yake ba, dan haka ya mike da sauri yayi gun motar sa yabi bayan ta duk yadda yaso ta hau taki sai da yai ta hada ta da Allah sannan ta shiga yaja motar a 360 kamar zai bar duniya. Ita kam ido ta lumshe kawai tana jin wani abu da ba zata iya kwatanta shi ba.
A kofar gida yai parking ta fita ta juyo ta dubesa sai ya bata tausayi yadda yayi yana kallon ta. Bata so su rabu da fauwaz ba amman yaya ta iya dole ne su rbu domin ba zata tsaya dare daya ya rusa mata tsarin rayuwar ta ba domin tana da plan komai nata a tsare suke a rayuwar ta,
"Sai wata rana!"
Ta fada cikin sanyin murya. Ta daga masa hannu tana murmushin dole. Shima murmushin yayi yace
"Nagode da kaunar da kika nuna mi!"
Kamar zatayi magana sai kuma tai gaba, da tafiyar ta mai kyau da daukar hankali, kallon ta yake kamar yaje ya janyo ta har ta kwankwasa kofa sojan da ke musu gadi ya leko yana ganin ita ce ya bude mata ta shige yana mata sannu da zuwa.

Fauwaz ya maida kansa ya kifa bisa sitiyarin motar ya lumshe ido, shi kadai yasan abinda yake ji a ransa na azaba da zugi daman haka so yake musamman idan baka yi dace ba. (Nace what Yasmeen is going on kenan) sam a zaton sa haka baza ta faru ba.
"No bazan iya hakuri da Billy ba. shin tayaya Billy zata so ni? nasan Billy da tsarsaurar ra'ayi da ji da kai, zuciyar sa ta kwabe sa. Zuciyar sa ta kwabe sa, dama zai iya yin kuka da lallai da yayi ko yaji sanyi a zuciyar sa.
Kiran magariba ne ya katse masa tunani sa ya fito waje yaje massallaci yayo sallah ya dawo ya ja motar sa. Gidan Marzuk yaje ta kirashi yana harabar gidn marzuk yace
"Kaga ka shigo ciki."
"A'ah kazo ina jiranka.
Daga yadda yaji muryar sa ya san ba lafiya dan haka ya fito da sauri ya tadda shi a saman mota shima ya hau ya zauna. ya dubeshi yace
"Yaa akayi ne abokina. Allah dai tasa lafiya?"
Shieu yayi can yace
"Akan Billy ne?"
Marzuk yace
"Wai kai Yasmeen din fa?"
"Bana fada maka tsakani na da ita ba. Nace maka ba soyayya muke ba."
Fauwaz ya fada cikin bacin rai.
"Naji to yanzu me ya faru da Billyn?"
Bai tsaya jiran sa ba ya kwashe komai ya fada masa.
Tsaki Marzuk yayi yace
"Kai ba shikenan ba, sai ka hakura tinda tace ba zata aure kaba. Yan mata nawa ke son ka ya'yan manya ga kuma Yasmeen koda billy ta yadda ta aure ka ba jin dadin auren zakayi ba domin idon ta a bude yake tasan dadin duniya Yasmeen kuwa sai yadda kayi da ita ga nutsuwa."
Tsaki Fauwaz yayi ya ce
"In ban auri Billy ba ji nake kamar na gama rayuwa wallahi."
Dariya Marzuk yayi yace
"Lallai yau an tabo yan maza, kai da ke garawa yau kai ake garawa."
Fauwaz ya kule, ya diro daga kan motar da sauri Marzuk ya diro yana dariya ya kamo hannu sa yana fadin
"Haba friend kazo musan abin yi ma."
"To ai kaine ana magana serious kana dariya sai kace baka san so ba."
Marzuk yace
"Shawara biyu zan baka na daya ka tsanan ta addu'a sai kuma ka share ta na wani lokaci kar ka neme ta, sai muga wane hali zata shiga anan ne zamu gane lallai tana son naka ko bata son naka.'
"In bata neme ni bafa?"
Dafashi Marzuk yayi yace
"Shiekan sai ka hakura domin an ce in so cuta ne hakuri magani ne. Kila Allah ya kaddara ba matar ka bace daman."
Dole ba dan yaso ba da wannan shawarar ya hakura. Haka ya tafi gida cike da damuwa a hanya dai dai dan agundi yayi accident saboda kwata kwata hankalin sa ba a jikin sa yake ba, nan da nan aka wuce dashi AKTH Inda aka nemi layin Alhaji Babba aka sanar dashi nan da nan suka tafi asibitin shi da Alhaji Karami da Abbah. Ya samu karaya sai dan ciwo da buguwa, sai da yayi kwana biyu ya farka daga doguwar sumar da yayi, sai dai an hada masa da alluran bacci.

Farkawa yayi yabi dakin da kallo ganin iyayen sa mata da maza yasa yai yunkurin tashi nan yaga hannun sa a sakale sai kafar sa da tai masa tsami dan ya bugu. Komawa yayi ya kwanta yana kallon yan dakin nan Abba yayo gun sa yana fadin
"Sannu baba na. Ka farka."
Nan yan dakin suka juyo kowa na masa sannu, yan gida ne gaba dayan su, su Mommy da Mie mie da Ummi Antyn Yasmeen sai kannen sa maza da matar Marzuk yar gidan yayar Mommy binta. A hankali ya fara tuno abunda ya faru, ransa ya hau suya ya runtsa idanu yana mai ganin duk tunanin Billy ne ya janyo masa.


*Shin me kuke tunanin game da wannan soyayyar shin billy zata yadda da Yaa Fauwaz ko kuwa?*

Don't forget to comment nd vote pls.


Antty ce!!!

Ni da Yaa FauwazWhere stories live. Discover now