*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_6⃣9⃣ - 7⃣0⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and Exhortate our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy na da Mommy nah)*
Lokacin da Aisha ta ganshi duk ya rame yayi baki. Anan dakin saukar baki aka sauke shi aka kawo masa abinci da kayan sha. Sam baya iya cin abun kirki dan damuwa da tai masa yawa shiyasa duk ya rame dan yanzu haka ma bikin sa da Sajida sauran sati daya. Mamahn sa jiran sa take yanzu haka so yake daga nan ya tafi can Egypt din.
Bayan tabashi lokacin abinci ta shigo sai dai taga ba abunfa yasha sai fura kawai. Zama tayi tace
"Ya baka ci komai ba."Kai ya jinginar a jikin kujera sai hawaye ta idon sa. Hankalin Aisha ne ya tashi tace
"Ahmad lafiya me ya faru? Ko Yasmeen ce tace tafasa auren ka.!Hawayen idon sa ya goge yace
"Aisha ina cikin tashin hankali.""Naga haka Ahmad, kalli duk inda ka lalace ka rame."
"Naso ace mutuwa nayi Aisha ba wannan ramar da baki ba. Akan halin da nake ciki da wanda zan saka mafi soyuwa a waje na.""Ahmad dan Allah ka fadan me yake faruwa ne. Wallahi duk hankalina ya tashi!"
"Aisha ku fahimce ni ku gane manufa ta banzo wajen Yasmeen da yaudara ba da aure nake son ta.""Me ya faru? Dan Allah ka fada min me ya faru?"
Ta fada hankali a tsahe. Ajiyar zuciya ya sauke yace,
"Naje gida na kai batun aure na da Yasmeen sai dai Mahaifiya ta tace sam bata san da zancen ba, saboda haka a lokacin ta samin aure da yar kanwar ta yanzu haka wani satin ne bikin mu. Bansan ya zanyi ba Aisha, kullum kara son Yasmeen nake yi sam na kasa cire ta a raina. Damuwata shine wane hali Yasmeen zataji in taji wannan abun bana son damuwar yasmeen koyaya take, wallahi daba dan uwata bace ba abinda zai sa nai mata biyayya amman ina tsoron naje nayi abu ba da sa albarkar ta ba kar rayuwar mu ni da Yasmeen ta lalace sanadi na dan nasan rashin albarka ta zata ta bibiya ta sannan sai kiga muna samun sabani wanda kila rashin biyayya tane. Aisha Ya zanyi tayaya zan tunkari Yasmeen da maganar nan. Ranar da na ganku a makaranta baki ji yadda nake jin son ta na kara tsumani ba kamar nazo na rumgume ta. Aisha ki fadan yaya zanyi? Yaya zanyi."
Sai kuka.Shiru Aisha tayi ta rasa me ke mata dadi dan lakar jikin ta duk ta fita jikin ta kuwa sai rawa yake haka nan zuciyar ta sai bugawa take. Tayaya zata fadawa Yasmeen wannan mummuna labarin bayan tasan yadda yanzu ta amshi Ahmad hannu bibbiyu shin tayaya zata tunkare ta da maganar ta. Innalillahi wainna illahir rajiun, abinda take nanatawa kennan tausayin Yasmeen ya kamata taso Yayan ta amman shi bai san tanayi ba ko tace sun yaudari kansu yanzu kuma taso Ahmad ga kaddarar da ta fada musu shikenan ita bata san wani dadin soyayya ba.
"Aisha kinyi shiru ki ban shawara yaya zanyi?"
Shiru ta karayi tana tuna wacece Yasmeen tabbas Yasmeen mace mai hakuri da tawakali tasan zata amshi kaddarar ta da hannu bibbiyu."Aisha!"
Ya kira sunan ta. Dagowa tayi ta kalli shi da idon ta da ke zubar da hawaye. Tashin hankali ya kara shi wato in kawar Yasmeen zatai kuka ita Yasmeen din me zatayi kenan.
YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasiaLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.