*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_8⃣1⃣ - 8⃣2⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and Exhortate our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy na da Mommy nah)*
Yasmeen ce ta shigo hannun ta dauke da kular abinci ta dire masa agaban sa tai serving nasa tace
"Yayana kaci abincin!"
Bai yi niyyar ci ba amman sai yaji yaa son ya faranta mata rai dan haka ya ja abincin ya fara ci. Ya manta yaushe rabon da yaci abinci sai yau. tana zaune tana kallon sa duk tausayin sa ya cika mata zuciya ko yaya suke da Antyn ta ko ta canja halin ta oho?Kadan yaci yace ya koshi ta kalle shi cikin damuwa dan tasan Yaya ta da ci kamar gara amman yau shine zai dan wannan yace ya koshi. Tace
"Ko wani abu kake bukata?""Da zaki min kunun gyada da naji dadi."
Da sauri ta mike ta fita ta daura bata jima ba ta gama ta saka sugar da madata ta kawo masa ya dan sha shi sosai. Sannan ya kwanta anan falon kallon sa tayi yace
"Wai har yanzu jikin ne?"Kai ya girgiza yace
"Yasmeen wani abu ne ke damu na?""Me kenan?"
Mikewa zaune yayi yana kallon ta, zai magana kenan wayar sa tai kara yana dubawa yaga Alhaji Babba ne dan haka ya dauka cikin girmamawa. Yace
"Kana ina ne? Kazo ina neman ka.""Ok gani nan!"
Ya kalle ta yace
"Bari naje Alhaji Babba na nema na sai na dawo!"Ya mike ya fita ta bishi da kallon tausayi dan ita kam tana yausayin Yayan ta har ga Allah. Allah ya bashi mace mara kula da gyara.
Acan office din Alhaji Babba ya sameshi. Bayan ya zauna suka gaisa yana tambayar sa iyalan sa. Kansa a kasa yana jin kamar ya fada masa abunda yake so amman ya kasa yana cikin tunanin Alhaji Babba yace
"Babana daman na kira na tambaye ka ne game da yaron nan Abbas iyayen sun matsa suna son a basu dan a tsayar da ranar aure. Ya kayi binciken."Kirjin sa ne yai wata irin bugawa. Sam ba zai iyayiwa iyayen sa karya akan abinda ba haka ba. Kuma neman aure ne sai Allah ya tambaye shi dan haka, yace
"Alhaji kamar yadda na fada maka tin farko Abbas bai da aibu aboki nane sosai acan kuma sam baka taba ji sa da halin banza ko dabi'un bamza, in har Yasmeen ta amince a basu dama.""Masha Allah! Nima ta nan nasa a yo min bincike sosai kuma an min ashe kanin mahaifin sa abokin Abban Yasmeen ne ma. Dan haka komai yaxo da sauki dan haka yanzu zan sanar su zo a tsaida lokacin shikenan kiran daman!"
Sam ba gane mai Alhaji Babban yake fadi ba dan ya tafi can tunanin tayaya zai sanar da iyayen sa yana son Yasmeen."Zaka iya tafiya shikenan!"
Sai anan yaji ya mike yace sai anjima. Da kallo Alhaji Babba ya bishi duk ya rame a ransa yace ko bai da lafiya ne amman kuma yayi sanyi da yawa.
"Koma menene Allah ya kyauta!"Daga can gidan sa ya nufa Billy bata nan anan Falo ya kwanta yana mai da numfashi da kyar da kyar. Yana kwance har akai kiran sallah magariba ya tafi yai sallah daga can gida ya koma. Yana zaune ogan su ya kira sa. Bayan yadauka yace lallai lallai yazo dan suna da wasan da za ayi zasu fara training. Wannan ba shiri yasa ya hau shiri duk da yaji ba wani abun arziki za yi ba amman dole yaje dan an nrmeshi.
YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasyLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.