53-54

566 36 0
                                    

*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_

5⃣3⃣ - 5⃣4⃣

Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*

Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and  Exhortate our readers)_*

Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_

*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy na da Mommy nah)*



Shiru yayi sai kuma yaji tausayin Yasmeen din ya kamashi dan haka sai ya koma ya zauna. Ita kuma ta kalli Yasmeen dake ta ajiyar zuciya tace
"Wai menene? Me ya hadaku?"

Kin magana tayi. Kallon sa tayi tace
"Kai sai ka fadan me tayi kake ta wannan fadan."

"Haba akan me zatana jajibe jajibe wani yaro na ganta dashi dazu a gidan nan. Sam ai tasan na hana ta kula samari amman ta tsaya tana kulawa."
Kallon mamaki take masa tace

"Ooo to in bata kula samari ba wa zata aura? Shin ta kusa gama karatu me zata xauna yi maka, ko kuwa kai zaka aure tane da kake hana ta kula samari. Yarinya ba ruwan ta zaka saka mata ciwon zuciya da wannan fadan naka."
Jijjiga Yasmeen ta fara tana fadi
"Kiyi hakuri ki bar wannan aminin naki ki kunce abotar ki dawo dani, sam wata rana haka yake bai da dadin sha'ani."

Nan takama hannun ta sukai dakin ta tana ta lallashi. Shi kuma suka bar shi a falo yana ta tunanin maganar Billy da tace ya dace ace ta tsaida miji tinda takusa gama karatu ko shine zai aure ta. Tabbas gaskiya ne sam ya manta dole Yasmeen tai aure to shi baya so, ya fi son kullum ta kasance a tare dashi. Dan da tayi aure shikenan gidan wani zata tafi ta koma under control dinsa shi kuma sai yadda akai da ita. Bai da wani iko na command akan ta. Shikenan zumuncin su zai rauni.

Lallai da ace Abba zai bar masa Yasmeen zai rike ta har abada ba tare da tayi kukan komai ba. zuciyar sa tace,
"To kayi yaya da sha'awar da Allah ke halliyar bayin sa da ita fa? Shikenan ita bazata ga ya'yan ta ba?"

Tuna da wadan nan maganganun yasa ya canja shawara daga ya nemi a bar masa ita har abada zai rike ta. Sai yaji hakalin sa ya tashi tunawa da dole Yasmeen tai aure, sai ya tina lokacin da mommy takai karar sa gun Alhaji babba da yace zai auri Billy da yace akwai manema da yawa masu son Yasmeen shi ya dakatar dasu saboda karatu kenan yanzu da ta gama zai basu dama.

Billy ma fushin ta dauka dashi da ta fito a dakin Yasmeen ta shige tai kwanciyyar ta. Yana nan zaune har sha daya yana tunanin yanzu ya Yasmeen take shin tana kukan ne ko tayi shiru.  Lallai bai dace ace bai je yaga halin da take ciki ya rarrashe ta ya bata hakuri ba.

Sam ita bata son bacin ransa ko damuwar sa yanzu zata rasa nutsuwar ta sai taga ya sauko amman shi kullum yasmeen tai hawaye akan sane. Ita kuwa kullum cikin lallashi sa da kwantar masa da hankali ko wani ne ya bata masa rai ta dunga tambaya tana bashi hakuri.

Mikewa yayi ya nufi dakin da take tana kwance amman idon ta biyu sanye da wata pink kalar rigar bacci cotton mai tsayi. Kanta ba dan kwali gashin kanta duk ya baje akan filo sai ajiyar zuciya take saukewa ta rufe dukka jikin ta da bargo. ya shigo dakin. Kallon ta ya tsaya dan ita bata san ma ya shigo ba. Kayan sun mata kyau duk da na bacci ne. Kallon ta ya tsaya kirjin sa na bugawa yana fadin
"Wannan Yasmeen ce?"

Ni da Yaa FauwazWhere stories live. Discover now