67-68

508 31 0
                                    

*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_

6⃣7⃣ - 6⃣8⃣

Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*

Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and  Exhortate our readers)_*

Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_

*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy na da Mommy nah)*

Mikewa tayi cikin fada tace
"To ban yadda ba, dan tsabar cin fuska tin yaushe nake fada masa yaje ya nemi mata a wajen kanne na amman yaki zai dauko wata bare can ko wa yasan iyayen ta ma oho, to wallahi indai ina da rai Ahmad ba zai auri wata ba in ba sajida ba. wato dan ya raina ni shine ya fada maka dan yasan ba zai iya tinkara ta ba ko? To wallahi ka fada masa sati biyu ma za a daura masa aure da sajida in yaso ya hadiyi zuciya ya mutu yarinya tana son sa amman shi sai rashin mutinci yake mata."

Nan ta mike ta bar wajen. Kai Abbahn sa ya dafe dan fadan Mamahn Ahmad na bashi tsoro. Dan haka ya kira Ahmad din.

Jikin Ahmad a sanyeye, ya shigo dakin ya zauna. Abbah yace,
"Ahmad ba zabin kane bana so ba. Allah ya sani nafi aminta da zabin ka akan na Mamahn ka amman ita ta nuna lallai lallai sai ka auri sajida shawarar da zan baka kayiwa mahaifiyar ka biyayya in Allah yayi ita waccen din rabon ka ce sai kaga ka aure ta. Kaje kai ta addu'a dan tace sati biyu za a daura auren ku."

Yadda Ahmad yaji saukar maganar kamar yaji saukar aradu kan sa ya sara masa zuciyar sa ta dinga bugawa bai taba son wani abu kamar yadda yake son Yasmeen ba.

Tashi yayi jiki ba karfi dan tunanin ta yadda zai tunkari Yasmeen da wannan maganar yake, inda ya takura mata har ta fara sakewa dashi kuma yanzu yazo mata da zancen zai yi aure ai kamar ya yaudare tane shi da ya fada mata tare zasu koma da masu neman auren ta. Yaya zayi da son da yakewa Yasmeen wanda daga Allah ne kuma a jinin jikin sa yake. Ya jima yana juyi kuka a daki shi kadai. Sai da yaji wani ciwon kai ya saukar masa sannan ya mike yasha magani ya koma ya kwanta yana tunanin rayuwa.

Tayaya zai iya zama da macen da baya so. Yasha fadawa Sajida cewa baya son ta bata cikin tsarin matan da yake so amman bata daddara ba sai da ta samu Mamahn sa ko gashi yanxu Mamahn shi tace sai ya aure ta. Tabbas ba zai iya yiwa Mamah jayaya ba yadda Mamahn sa ke son sa da kula dashi. zai mata biyayya yasan Allah ba zai barshi haka ba amman har ga Allah ba son Sajida ko daya a cikin ran sa.

Satin sa daya ya koma Nigeria da shirin fadawa Yasmeen komai. Sai dai da ya koma yaji labarin suna Exam dole ya kyale akan sai sun gama dan ba karamin abu bane yasan dole ta shiga damuwa. Inya tuna yadda ta dinga gudun soyayyar sa amman har a cusa mata ta saurare sa ta kuma amince ya zama dan uwan rayuwar ta.

Yasmeen ce zaune tana karatu ta dago ta kalli Aisha tace
"Aisha Wallahi Abbas ya matsa min shiyasa nake son Ahmad yai sauri ya aiko ko na huta in yaji an bada ni."

Murmushi Aisha tayi tace
"Gaskiya ne, wallahi Ahmad yazo da sa'a shima ina fada masa. Wai yau Yasmeen ce ke maganar wani ya tura gida. Shin menene aibun Abbas din ne?"

"Wallahi bai da aibu dan zan iya auren sa amman matsalar na riga na fara amsawa Ahmad kinga in har na ce ya turo naci amanar Ahmad kuma nasan inda Ahmad ke sona din na zai iya komai akai."

Ni da Yaa FauwazWhere stories live. Discover now