85-86

479 35 1
                                    

*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_

8⃣5⃣ - 8⃣6⃣

Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*

Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and  Exhortate our readers)_*

Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_

*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy na da Mommy nah)*


Da suka dawo Nigeria can gidan sa Marzuk ya kai shi, anan kuma Yaa Fauwaz ya kara rokar Marzuk akan kar ya fadawa kowa abinda ake ciki. Amman Marzuk yace zai duba ya gani. Ganin in baiyi da gaske ba Marzuk ba karamin aiki zai ja masa ba yasa yace
"Ka bari zan sanar da Mommy da kai na."

"Kayi alkawari?"
Marzuk ya tambaye shi. Yace,
"Nayi!"

"Ina matar gidan ne?"
Ya fada yana kalle kallen gidan. Kallo sa Fauwaz yayi ya jingina da kujerar dakin yana fadin
"Tana aiki ina jin!"

"Baka fada mata zaka dawo bane."
"Uhmmm!"

"Me zan samar maka ne?"
"Kar ka damu bana jin yunwa!"

"Kasan dai doctor yayi magana akan kana cin abinci da shan magani akan lokaci ba, please friend ka kula, In kaga da matsala ka neman kaji."
Kai ya gyada ya kama hannun sa yace
"Nagode Friend Allan kara Mana zumunci ya saka da alheri.'

"Kar ka damu!"
Ya fada yan mikewa yace
"Sai munyi waya bye!"

Komawa yayi ya kwanta, yana me danne zuciyar sa, shi yaya zai yi da rayuwar sa lallai yana son kulawar matar sa amman sam Billy bata san da wata kulawa ba da ace Yasmeen ya aura daya san bai da matsala akan wai abubuwan nashi.

Sam yanzu Billy bata da wani amfani a wajen sa tinda ita bata bashi hakkin sa wanda ya tuna lokacin da ya neme ta da abinda tayi masa wannan yasa yai zuciya ya kuma sa a ransa ba zai kara neman Billy akan ta bashi hakkinsa ba sai dai in ita tane ma shi ba zai tauye ta ba. Dan shi duk abinda ke kan sa yana sauke mata Allah ya gani bai cutar ta bare zaluntar ta da shiga hakkin ta.

Ya jima a gun a zaune da kyar ya mike yana dafe bango ya shiga daki kan gado ya fada ya kwanta yana kwance har yaji ana kiran magariba ya mike ya shiga yai wanka yai alwala ya fito ya saka kayan sa ya nufi massalaci. Bayan ya fito daga sallah ya bawa driver kudi ya siyo masa abinci da snack da lemo. Yana compound ya dawo ya amsa yayi cikin dakin sa acan ya danci abinda zai ci ya saka sauran a firij ya sha magani ya kwanta.

Wajen karfe sha biyu yaji shigowar ta mikewa yayi ya nufi window yana kallon ta.  Sanye take cikin kayan da ta saba sakawa, bakin siket sai karamar riga da dan karamin mayafi kan ta ba dan kwalli motar ta rufe tayo ciki. Komawa yayi ya zauna yana mai girgiza kai wai shin yaushe Billy zata san Allah ta daina wadan nan shigar. Ko baka da aure shigar nan bata dace dashi ba bare yanzu da aure kan ta.
"Ya Allah ka yafen ka shirya Billy!"

Ya fada yana mikewa yayo alwala nan ya hau sallah yana neman sassauci da yafiyar sa.

Kwanan sa biyar amman bata san da yana gidan ba sai a kwana na shidan shima bai san tana nan ba ya fito zai dauko ruwa a kitchen. Tana falo ya same ta, ya daura kafa daya kan daya yana ta danne danne a system din ake gaban ta. Kallo daya yayi mata ya dauke kai ya shige itama ta bishi da kallon mamaki shin yaushe ya dawo. Tana cikin tunanin ya fito rike da ruwa yayi dakin sa. Kasa aikin tayi ta rufe system din tana mai tunanin yau Fauwaz ne zai ganta ya watsar kamar bai san da ita ba. Anya kuwa wannan Fauwaz ne. Sai abinda ya gani game dashi ya rame to bai da lafiya ne kome?

Ni da Yaa FauwazWhere stories live. Discover now