59-60

500 27 1
                                    

*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_

5⃣9⃣ - 6⃣0⃣

Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*

Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and  Exhortate our readers)_*

Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_

*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy na da Mommy nah)*


Da dadare bayan sun dawo daga wani store suna cikin bude kayan da suka siyo ya kira ta. Dan tsaki ta saki sannan ta dauka tace
"Assalamu Alaikum!"

"Wa'alaiku salam princess daga ina kuka dawo yanzu?"
"Kamar ya daga ina na dawo? Ni ba inda naje."

"Sam baki kala da masu karya ba dan haka kada ki fara. Yanzu naga dawowar ki daga bakin gate sanye da jan hijab, ina kika je?"
Jikin ta ne yai sanyi to bibiyar ta yake kome. A'ah ta ina ma yasan makarantar da take kuma a hostel take. Take tsoro ya kamata. Kamar ya san taji tsoro sai yai dariya yace
"Ni ban tambaye ki daga ina kike dan na tsorata ki ba. Kada ki manta in har mutum na son abu zai yi komai dan sanin inda abu yake da kuma bashi kulawa. Ki sani daga yanzu kina karkashin kulawar Allah da kumatawa. Fatana ki kasance cikin aminci kan kuma na dauke daga wajen Mommynki."

Sororo tayi tana mamaki. Nan taji yace
"Maryama kenan, ni nasan komai akan ki kuma ba zan taba sanya ba sai na same ki. Lallai Allah yana sona da har ya hadani dake, tin kan nasan ke wace naji na gama aminta da ke, sai kuma yanzu da na kara sanin ke wace ki sani zanyi duk yadda zanyi naga kin kasance uwar ya'ya na domin ba abinda zan wa ya'ya na a rayuwa face na samar musu uwa tagari kuma na samu kece. Ina alfahari da kasancewa ta da ke. Ina godiya da Allah da ya hadani dake yanzu sauran na san yadda zan yi na samu soyayyar ki. Dan Allah princess ki tausaya min, ki amshi soyayya ta."

Aisha na zaune ta zuba mata ido a ranta tace
"Yau wa kuma Yasmen ta samo!"

"Amman nace ka barni zanyi tunani ko?"
"Wallahi duk na kagu naga na samu soyayyar kine? Ya sunan kawar taki da na ganku ynzu?"

"Aisha!"
Ta bashi amsa a takaice.
"Ok ki gaishe ta. Me kike bukata yanzu?"

"Ba konai!"
"Haba dai dan makarana ai ba a rasa shi da bukata."

"Ni kam bana bukatar komai"
"Ok shikenan sai anjima. Ki kular kin da kanki."
Ya kashe wayar. Dakin taji ana knocking mikewa tayi taje, wata yarinya ce ta miko mata wata katuwar leda guda biyu tace
"Gashi inji wani acan bakin gate yace na kawo miki!"

"Ni kuma?"
"Eh ke yace min Maryam wacce ake kira da yasmeen yar department din medicine with ur friend Aisha!!

Mika hannu tayi ta amsa. Sannan tayi godiya ta shiga cikin dakin. Karar text ne ya shigo yace
"Sako nane!!
Kai ta jinjina sannan ya ajiye kayan.

Aisha ta mike tana fadin
"Me muka samu!"

Ta fara budewa, katon gwamgwanin madara ne da na milo sai goldern morn da cornflakes sai wasu bikist kala kala da lemo. Dayar ledar kuma gasasun kaji ne manya guda uku sai shawarma da meat pie da cake da lemo a ciki.

Ni da Yaa FauwazWhere stories live. Discover now