51-52

492 31 0
                                    

*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_

5⃣1⃣ - 5⃣2⃣

Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*

Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and  Exhortate our readers)_*

Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_

*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy na da Mommy nah)*


Zaune take a gidan ita kadai a falo dan Anty Billy ta tafi aiki Yaa Fauwaz kuma ya fita. Tana zaune taji karar wayar ta, number Ahmad ce sai da ta danyi tsaki sannan ta daga.
"Baby nazo dan Allah!"

Ya fada dan da kyar jiya bacci ya dauke shi daga ya rufe ido zai gano ta tana masa murmushin nan nata wanda three beauty point dinta ke lotsawa. da yadda take zaro ido, wanda idanun ke kara kyau da girma. Tin safe da ya tashi bai da aiki sai na tunanin ta, dan haka yanzu ganin yamma tayi bata neme shi ba yasa ya kira ta shine ya fara da rokar ta.

'Wallahi in ban ganki ba yau zan shiga wani hali ki taimaka min nazo."
Murmushi ta dan saki ko ba komai ya nuna soyayyar ta da damuwa da ita dan haka tace
"Ba matsala."

Karfe biyar sai ga kiran sa nan yazo hijab ne a jikin dan haka ta fito tsaye ta ganshi a parking space jikin wata hadadiyar motar sa. Yana sanye da milk kalar shadda ta masa masifar kyau gashin nan nasa sai sheki yake. Yana ganin ta ya kafe ta a ido dan shi kadai yasan me yake ji game da Yasmeen. Wajen sa ta karasa a kunya ce tace
"Bisnillah!"

Sukayi can gefen parking lot inda aka ajiye wasu kujeru da table. Zama yayi itama ta zauna tace
"Ina yini?"

Kanta a kasa, yanayin kunyar ta sai ya burge shi dan haka ya dinga binta da kallo yana murmushi can yace,
"Wallahi princess son ki yai min magu kamu. Da farko sunana Ahmad Iliyasu, ni ne Auta a gun iyaye na, Yaye na biyar mata biyu maza biyu duk sunyi aure da ya'ya. mahaifina shine ambassador na Nigeria a kasar Egypt. Yanzu haka iyaye na suna can, nazo hutu ne nazo gidan abokina jiya na ganku. Nayi degree dina har zuwa matsers dina yanzu haka ina aiki acan kasar Egypt. a bangaren addini na sauke alkur'ani har da hadda da sauran littafan addini. Tinda na ganki jiya naji duk duniya babu  wacce nake so sai ke, yan mata da yawa na so na amman sam ni ba kyau nake nema ko ilimi ba. Tindaga kallon ki na daya da nayi naji kece kalar matar da nake so tin daga kan shigar ki har yanayin maganar ki. Dan Allah Yasmeen ki taimaka ki amshi soyayya ta ko yaya ne ki gutsura min zuciyar ki nai miki alkawarin zan kula miki da ita har karshen rayuwa ta bazan taba barin ki kiyi kuka ba. Ki taimakan ko na samu sa'ida da nutsuwa wallahi daga jiya zuwa yau ni kadai nasan wahala da zulumin da nake akan ki."

Kai ta kara dukawar daga jiya zuwa yau ya gane Yasmeen yarinya ce mai kunya shi kuma yana son mutum mai kunya abinda ya kara masa son ta, a da sam bai da niyyar aure bare soyayya dan abokan sa har zolayar sa suke. Wasu suce dan yana da kyau ne. Shima a inda ya dauki kan sa ba macen da zai matarwa dan gani yake tsadar sa tayi yawa sai gashi lokaci guda Yasmeen ta canja masa tunani da tsarin sa yana ganin in har ya rasa ta ya rasa rayuwar sa. Bayan a da ya wulakanta yan mata kala kala ya'yan manya daga sarakuna gwamnoni da sauran su. Amman yanzu Allah ya daura masa son wacce bai san wacece ba kuma bai damu da sani ba ko ya take yana son ta zai aure ta.

Ni da Yaa FauwazWhere stories live. Discover now