119-120

1K 41 0
                                    

*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_

1⃣1⃣9⃣ - 1⃣2⃣0⃣

Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*

Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com
Wattapad *Msindabawa*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and  Exhortate our readers)_*

Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_

*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a adidu'a Mommy na da Mommy nah)*



Zaune yake kanta a saman cinyar sa yana wasa da gashin kanta dayan hannun na saman kirjin ta.
"Yasmeen!"

Ya kira sunan ta idon ta ta bude wanda suke kamar me jin bacci.
"Tashi muyi magana."

Mikewa tayi tana kallon sa.
"Baby na ina da wasan da zamuyi ina son na tafi nan da kwana biyu saboda zamuyi shirye shirye, domin babban wasa ne dan world cup ne. Yasmeen ina so kiyi hakuri kinji, Dan ina son na ajiye wannan wasan nima na dawo gida dan ba zan na iya nisa dake ba kullum ina waccan kasar gobe ina can kuma ni bazan iya tafiya dake ba dan ina kishin ki bama wannan ba nan gaba muna son samun zuri'a kinga nima wasa na ba dole ne ko yaushe ina wata kasar daya ba yau ina can gobe ina can kinga karatunyaran mu zai samu matsala kuma ina son yara na su samu karatun addini kamar yadda kika samu zaman mu anan zaifi dan haka daga wannan wasan zan bar shi."

Murmushi tayi dan itama tana tunanin yadda zata na yin kewar sa. tace
"To Yaya Allah ya taimaka ya bada sa'a hakan ma yayi!"

Fuskar ta ya shafa yace
"Na bude wani kamfani wannan satin order mu zata zo Abba shi ya shigen gaba sannan na samu aiki dan na Kai takarduna kuma sunyi accepting dan na ce su dakata ne."

"Alhamdulillah Yaya na. Allah yasa a fara a sa'a!"
"Ameen My princess, sai abu na gaba, Yasmeen so nake in kina gama service ki fara aiki a asibitin da na gina miki an miki komai, time kawai muke jira a bude!"

Rumgume shi tayi ta rasa abinda zata ce sai hawaye. Dago ta yayi yana sharre mata hawayen tace
"Yaya da me zan saka maka ne? Tin ina yarinya kake dawainiyya dani, har na girma gashi yanzu na zama matar ka amman duk da haka kana dawainiyya shin Yaya da me zan saka maka?"

Murmushi yayi yace
"Yasmeen tin da aka haife ki Allah ya dauran son ki, ban kara son ki ba sai lokacin da kowa ya daina sona a gida yadda kike kula dani da damuwa da damuwa ta, Yaameen son ki a jinana yake a lokacin da nace ba soyayya muke ba sam na kasa samun nutsuwa, kishin ki ya hanani sakewa wannan yasa na hana ki kula samari sai daga baya na gane son ki nake. Yasmeen son ki ya wahalar dani lokacin da Abbas yace yana son ki na shiga damuwa da tashin hankali. Ina son ki Yasmeen Abba shi ya shige gaba na same ki. Abba na sona shiyasa nima nake son sa sosai. Ya min abinda ko Alhaji na bai min ba."

Nan ya bata labarin duk abinda ya faru dashi. Yasmeen kuka take tana rumgume dashi.
"Yasmeeen ban san me ya hanani bayyana soyayya ta gareki ba amman kece farin cikina abin alfahari na hasken idaniyya ta rayuwa ta."

Kamkame shi tayi tace
"Yaya nah ban taba son wani aduniya ba bayan kai duk wanda ka ganni tare da shi ina kula shie kawai saboda na rasa soyayyar ka."

Nan ta bashi labarin duk halin da ta shiga time din da ya fara cewa Billy zai aura da yadda take fama da soyayyar sa. Hawaye ta goge tunawa da rayuwar ta tada ashe dadi yana gaba.

Ni da Yaa FauwazWhere stories live. Discover now