101-102

915 48 2
                                        

*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_

1⃣0⃣1⃣ - 1⃣0⃣2⃣

Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*

Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com
Wattapad *Msindabawa*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and Exhortate our readers)_*

Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_

*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a adidu'a Mommy na da Mommy nah)*





--------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Tin da ya fara maganar yai aure ta dauke wuta bata farga ba sai ganin fitar sa tayi. Nan ta shiga gumi da tashin hankali. Yau Fauwaz din ta ne yayi aure. Lallai ai kam bazata taba sabuwa ba sam ba a isa a ci mata mutumci ba ita za ai wa kishiya tab din. Nan ta hau surutai kala kala wanda bata san a halin da take ciki bama.

Wayar ta ta dauka dan kiran kawar ta Asiya. Tana dauka tace
"Ya akayi me kika manta kuma?"

Kuka ta fashe mata da shi da sauri Asiya tace
"A'ah Billy lafiya kuwa?"

"Inafa lafiya Fauwaz yau yaci mutunci na wai aure yayi."
"Me? ai duk laifin kine."

"Kamar ya laifinane Aisya dan Allah ya zanyi?"
Tsaki tayi tace
"Wallahi Billy ni ba zan iya zama da kishiya ba in dani ce ke in bai saken ba wallahi daga shi har matar sai na kashe su. Da girman ki da ajin ki da komai ace za a miki kishiya haba dan Allah. Ke Billy ki tashi tsaye dan ba abinda yafi ai maka kishiya kaskanci da ke a yanzu ma kisan mazan dake min maganar ki amma kin tsaya a Fauwaz uban me Fauwaz din yake baki in ba razhin mutunci ba. Wallahi Billy ki kwaci yan cin ki haba sai kace ba wayayya ba."

Nan tai ta mata hudubar banza wanda Billy ta dauke su dan itama a yanzu ta shiryawa rabuwa da Fauwaz din. A raina nace ai daman yanzu ba aure a tsakanin ku.



*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-

Tinda su Aisha sukq tafi bacci ya dauke ta anan kan gadon ta kuddundune jikin ta, ta fara baccin ta.


Abba na kai shi gidan yace
"Sai kayi hakuri Allah ya bada zaman lafiya. Allah yayi muku albarka."

"Amin Abba nagode Allah saka da alheri."
"Ba komai Fauwaz! Debi kayan ka shiga dare yayi!"

Diba yayi ya kara masa godiya sannan ya nufi barandar gidan. Ya shiga main falon kamshi da sanyin dadi suka masa sallama. Ido ya lumshe yana mai hamdala ga Allah. Agogon dakin ya kalla yaga karfe sha daya da kwata. Dakin da yai tsammanin nata ne ya shiga. Falon ba komai sai kamshi da karar Ac dake tashi. Kofar Bedroom din ya bude a bakin kofa ya tsaya yana hango ta kwance a karshen gadon ta kule a waje daya, da ido ya bita ya jima a tsaye kan ya ajiye abun hannun sa ya rufe mata kofa ya nufi dakin sa.

Yana shiga yai alwala yai sallah ya hau sallah ranar kwana yayi akan sallaya yana godiya da Allah sannan yana addu'a akan Allah ya yafe masa batawa iyayen sa da yayi. Sai kuma yaji wata kunyar Yasmeen.
Da sassafe ya bar gidan dan baya so su hadu da Yasmeen.

Ni da Yaa FauwazWhere stories live. Discover now