*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_1⃣5⃣ - 1⃣6⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlightenment and Exhortation our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_*Ina mika sakon gaisuwa ga Autan Mommy _Al AMIN_ Allah ya raya mana kai yayi albarka ya bada ilimi mai amfani. Ameen*
Not Edited
Sallamar Dad da Billy ne ya katsewa yan dakin maganar da suke. Tana sanye cikin shigarta ta ko yaushe sanye take da dogon wando da riga, dama dama ma ta yau tinda ta kusan zuwa gwiwa sai dai sun dame ta. Tayi rolling kan ta da dan karamin Mayafi.
Abba ne ya mikawa Dad kujera ya zauna Billy kuwa kusa da Fauwaz dake kwance ta karasa. Gaisawa sukai da Baba da Su Alhaji Babba yai musu ya mai jiki. sannan ya juyar da kansa ya suka gaisa da Fauwaz yana tambayar sa ya jiki? Fauwaz yace
"Da sauki."Mikewa su Alhaji Babba sukai dan zasu mai da Baba da Mama gida
Billy dake gefen sa sai kallon sa take amman sam yaki ya kalle ta. Kai ta langwabar tace
"Ya jikin Fauwaz?"
"Alhamdulillah!"
Ya fada ya mai da kallon sa ga Dad da suke magana. Idan ta saka musu baki sai ya kautar da maganar, har abin ya fara bata dariya, ana haka ne Kanin Fauwaz Nazir ya kawo masa brush yana daga zaune yayi sannan ya hado masa tea da dankali. Billy ce ta amsa ta fara bashi.Abin sai burge Dad yake sai fara'a yake. Bayan ya gana ci ne yan kungiyar su suka shigo duba shi wannan ne dalilin yasa su Billy tafiya bayan Dad ya ajiyewa Fauwaz kudi masu uban yawa. Amman daga Billy har Fauwaz ba wanda yaso tafiyar junan su. Duk da dai ba hira suke ba.
Bayan kwana uku da farfadowar sane yake tambayar Yasmeen. Mommy tace
"Ah lallai bata sani ba domin ba wanda ya fada mata. Bari na kira ta."
Nan ta dauki waya ta fara neman layin ta.Yasmeen kuwa tin ranar da abin nan ya faru, taji a jikin ta dan wata faduwar gaba taji. Har tana dafe kirji. Aisha tace
"Lafiya?""Wallahi gaba na ne yake ta faduwa."
Yasmeen ta bata amsa."Ayyah sorry kina addu'a kinji."
Da toh kadai ta amsa mata.Tin daga lokacin ta rage walwala dan har ciwon ta kwanta adaddafe. Tana kwance Wayarta ta hau ruri dauka tayi taga Mommy ce da sauri ta kara a kunne tana fadin
"Mommy na ina yini?"Mommy ta amsa da
"Lafiya ya makarantar?""Alhamdulillah! Momny ya kowa da kowa?"
"Lafiya Alhamdulillah sai dai yayan ki da ya samu accident yau har kwana uku."Cikin rudu da tashin hankali ta hau fadin
"Innalillahi wainna illahir rajiun. Yanzu yana ina?""Muna asibitin Aminu Kano."
Cikin kuka tace
"Ok Mommy gani nan."Aisha dake gefen ta tace
"Lafiya?"
Hawayen idonta ta hau gogewa tace
"Yaa Fauwaz ne yai hatsari."Tsaki Aisha ta saki tace
"Shine kika tada hankalin ki haka."Duk da dan ita take wannan abun amman bataji dadi ba. Dan tana son Yayan ta ko ba na aure ba. Dan haka bata tanka mata ba tace
"Uhmm bari na shirya na tafi tinda gobe Friday bamu da aji sai Monday zan dawo""Au ba neman rakiya?"
Aisha ta tambaya."A'ah ai kar na shiga hakkin ki ko bakya son zuwa."
"Zani ko dan Anty Binta mana in huta da mitar naki naje gidan ta."Nan da nan suka shirya suka nufi asibiti lokacin karfe biyar da rabi suka karasa asibitin.
Dakin cike yake da kannen sa su Yaa Ishaq da Yaa Nazir da Yaa Abba da su Siyama dukkan su. Suna shiga suka fara gaishe da yan dakin. Siyama kanwar Yasmeen tace
"Oh ke Anty Yasmeen sai yau zaki zo duba aminin naki wajen sati daya lallai mun ganku a rana."Yasmeen da ba gwanar magana ba tai shiru tayi gun Yaa Fauwaz da tin shigowar su idon sa na akan ta. Aisha ce tace
"To ai duk laifin kine da baki fada mata ha."Siyama tace
"Lah Anty Aisha shigar mata zakiyi, Allah ki bar Anty Yasmeen din nan."
Dariya Aisha tayi kawai.Gaban gadon ta karasa ta zuba masa ido tana kallon hannun da ya karye da ciwon da ya danji. Daya hannun mai lafiya ya dago ya janyo ta ta zauna. Fuskar sa ta shafa tana ya mutsa fuska kamar ciwon a jikin ta yake tace
"Sannu Big bro!"Idon ta ya ciko da kwalla. Hannun sa mai lafiya yasa ya fara goge mata ido yana fadin
"Daina kuka mana ai dasauki."Kai ta girgiza tace
"Amman sai yau za a fada min Yaa Fauwaz. ace kana wannan halin ban sani ba."Anty Binta da ta shigo tai wajenta ta hau lallashi. su Yaa Ishaq kuwa suka hau tsokana wai mai arahar hawaye zata fara kenan. Ita dai tana jin su tai shiri.
Yaa Fauwaz ne yace
"Wallahi duk wanda ya kara tsokanar ta sai ya bar dakin nan."
Da yake suna shakarsa sai duk sukai shiru.Aisha kuwa tin da suka shigo take kallon dramar su, ranta tace 'ana so ana kaiwa kasuwa jibi nasu salon soyayyar kuma.'
Shigowa Alhaji Babba ita ta katse musu hirar da ake yace
"magariba ta taho ga driver can zai tafi gida kowa ya tashi yatafi."Yaa Fauwaz yace
"Alhaji Babba Yameen zata zauna ta yankan lemo abarta"Hararasa Alhaji Babba yai yace
"menene anfanon su Ishaq yankan lemo ne sai ta zauna. Maza ku wuce driver na waje."
Hannun ta yarike yana kallon ta tace
"Sannu Yaya na? Da ciwo ko? Kana shan magani?"Kai kadai ya gyada mata ta zare hannun ta tace
"Sai da safe Yaya na."Ta juya tabi bayan yan uwan ta. Ba dan taso ba shima haka bai so tafiyar taba. A mota ma sai tsokanar ta suke yan gidan su sai Aisha da Anty Binta ne ke kare ta domin ita babu baki.
A gidan Anty Binta suka kwana dan tin asuba Yasmeen da ta tashi bata koma bacci ba ta shiga kitchen duk abinda tasan yana so shi dafa masa kan karfe takwas tagama ta hada komai tabawa drive ya kai masa asibiti. Ai kam yaji dadi dan a asibitin ma hana su Ishaq da Nazir yayi. Sai tsiya suke mai basu taba ganin ma jinya yana cin abinci haka ba. Shi dai sai yace
"Naji ai jiki na nunawa."A haka har ya koshi ya basu saura suka hau ci
Yasmeen kuwa da ta gama, sannan ta hau gyaran gidan ko ina ta turare shi. Tana gamawa ta shiga tai wanka ta fito ta shirya cikin wata atamfa riga da raper zani sai hijab dinta daura. Ko karyawa ba tai ba tana zumudin taje taga yayan ta.
Don't forget to comment and vote
Antty ce

YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasyLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.