71-72

536 33 0
                                    

*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_

7⃣1⃣ - 7⃣2⃣

Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*

Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and  Exhortate our readers)_*

Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_

*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mun ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy na da Mommy nah)*



"Yasmeen!"
Ya kira sunan ta yana fade kirji tare da yin tari. Sai da tarin ya tsagaita sannan tace masa
"Sannu!"

Bai amsa ba yace
"shin ke wacce irin yarinya ce? Hakika nin gaskiya zanyi rashin babba rashi na samun mace mai ilimi da nutsuwa da tarbiyya. Yasmeen duk wanda ya same ki na masa murna bai da bakin ciki ya kuma gama dacewa a duniya sauran sa kiyama. Kuma kasancewar sa dake na tabbata zai gyara masa lahirar sa. Hakika zanyiwa yarana takaici na rashin kasancewar ki mahaifiyar su. Hakika ke yar aljanna ce. Nasan da wata ce shawara zata ban na bijewa iyaye na ko nazo mu gudu muyi aure amman ke kalaman ki ya kashen jiki yasa na daina jin haushin zabin da Mamah tayi min sai takaiicin rashin ki da zanyi. Allah miki albarka. Allah ya baki miji mai kaunar ki sosai. Wallahi Yasmeen a duniya daga iyayen ki nafi kowa son ki amman ban san yanzu ta yadda zan nuna miki sona ba. Amman ki sani ina miki son da banawa kai na. Rayuwa ta duk dake na gama tsarawa na baki farin cikin duniya amman Allah yayi ba haka bane. Ina fatan ki zama tawa amman bansan tayaya ba. Addu'ar da zan miki shine Allah ya jikan Mamin ki dan nasan da Mamin ki na da rai da tafi kowa farin ciki da alfahari da samun ki. Allah ya sakawa Mommy da gidan Aljanna dan tana daya daga cikin wadan da suka taimaka kika zama abinda kika zama. Allah ya baki miji na gari mai kaunar ki ya kuma baki zuri'a mai albarka Amin. Ina son ki Yasmeen bazan taba daina son ki ba......."

Tari ne ya kwace masa abinda yasa ya dakata da maganar kenan tace
'Sannu Ahmad wai baka da lafiya ne?"

"Uhmm Yaseen nayi ciwo a garin su kawar ki Aisha su sukayi ma jinya ta Yasmeen. Naje dan na fadamata abinda ya faru acan na kwanta ciwo."
"Ayyah sannu amman shine ba a fadamin ba."

Ta fada kamar zatai kuka.
"Kada ki damu naji sauki. Gobe ma zan wuce can Egypt din!"

"Allah ya kiyaye hanya ya jikin?"
"Naji sauki wallahi.

"Allah kara sauki!"
"Amin!"

"Nagode Ahmad sai anjima ko!"
"Nike da godiya Yar Aljanna. Nagode Allah miki albarka! Zanyi rashin hasken idaniyya ta mai sakani farin ciki mai kwantar min da hankali, ruhin rayuwa ta."

"Hmmm!"
Kawai ta fada ta kashe wayar dan wani kuka ne ya taso mata tun daga kasan zuciyar ta. Kanta ta cusa cikin filo ta saki kukan mai zafi. Kuka take kamar ba gobe zuciyar ta na mata zafi kan ta na sara mata amman sam ta kasa dainawa da ta jiyo muryar Siyama zata shigo sai tayi sauri ta shige ban daki tana ganin jiri. Acan bandakin ma bakin ta ta toshe tana kukan ta fi minti ashirin sannan ta mike ta yi wanka ta fito lokacin har ta Siyama ta fita dan daman gidan Aunties din su zasuje. Tana fitowa ta saka kaya ko mai bata shafa ba saboda wani zazzabi ke nema rufe ta da ciwon kai ta haye gado taja bargo ta rufe jikinta.

Ni da Yaa FauwazWhere stories live. Discover now