39-40

526 30 0
                                    

*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_

3⃣9⃣ - 4⃣0⃣

Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*

Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and Exhortate our readers)_*

Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_

*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy da Mommy nah)*




Tin da ya tafi kullun suna makale da waya dan yanzu da baya nan tafi kula dashi da tarairayar sa har da nuna masa soyayya. Dan haka sai yaji yana son ya dawo gida yaga Matar tasa. Duk da suna yawan vedio call su sha soyayyar su.

Ta koma bakin aikin ta. Sosai ta mai da hankali akan aikin ta dan tana son sa. Sai dai sam in ka kalli Billy ba zaka ce matar aure bace kullum cikin saka kaya damamu ko riga da wando, mayafi kuwa sai ta ga dama in ma ta saka to dan karami ne wanda dashi da babu duk daya dan haka zaka gansu transparent dasu.

Ranar Alhamis ya shirya dawowa kuma itama ya fada mata sai murna da doki gaba dayan su suke. Dan ya fada mata jirgin da zai hau da lokacin da zai sauka.

Karfe tara na dare ya sauka, driver ya sama yaje daukar sa. Tara da kwata a cikin gidan sa tai masa ya fito yana mi'ka hadi da sakin murmushi. Cikin gidan ya nufa yana zumudin yaga Billyn sa, saidai me? Bata falo ya shiga dakin ta nan ma bata nan. Dakin sa ma haka dan haka ya wuce gun megadi yana tambayar sa
"Billy ta fita ne?"

"Eh ranka ya dade!"
"Tin yaushe?"

"Wajen karfe shida ta fita!"
Cikin gida ya koma ransa a bace tasan zai dawo ina ta tafi. Wayar sa ya zaro da zumar kiran ta sai yaga sakon ta.
"Hae Baby nasan by now u are at home. Am sorry yau aikin dare ne dani ga Devid nan ko Samuel zasu kula da kai in kana bukatar wani abu zaka iya neman su. Sai na dawo I luv u."

Tsaki ya saki ya fada kan kujera yana dafe kansa. Shin wai me Billy ta mai dashi ne, ace mijin ki yai tafiya yai wata daya baya kasar ai ko excuse ta dauka a gun aiki for one day dai kawai tai welcoming nasa amman ina. Lallai Billy bata san aure ba ya yadda sai yanzu yake ganin abinda ta fada masa a baya.

"Hello Oga!"
Muryar Samuel ta doke shi. Da sauri ya dago yana kallon sa da jajayen idanun sa. Kan yai kasa dashi yace
"Welcome oga ur food is ready, kana bukatar wani abu ne?"

"No!"
Ya fada yana lunshe idon sannan yace
"You can go tnc!"

Tsaki yayi yace
"Wai daman wadan nan kedaren take cewa in uina bukatar abu in tambaye su. Shin abinci ne kadai bukatar ta. Yadda nai tafiyar nan ya dawo ina son tarba daga matar ta ta hada mai ruwan wanka nai wanka sannan ta ciyar dani abinci da hannu ta daga nan ta min massage bayan nan inda nai missing din nan nata na samu tarba ta kawar min da ishrwar da nake ji da zumar ta. Amman shi ba ko daya."

Yana zaune a falon nan yana ta karanta wasikar jaki ya jiyo karar motar ta. Ido ya daga yana kallon agogon dakin karfe sha biyu da rabi. Shin sai yanzu take dawowa in tana nyt shin wannan wane irin aiki ne, ace mace matar aure ta kai har 12am a waje basa tsoran wani abu ya same ta. Yana cikin tunanin ta budo kofa tana ganin sa tayo kansa da gudu tana fadin
"I miss u my Husband!"
Nan ta hau kissing nashi ta ko ina abinda ya mantar dashi damuwar sa da baci ran da yake ciki kenan. Nan ta jefa shi a wata duniya sun fi awa biyu sannan ta zame jikin ta ta kwanta akan kujerar tana mai da nufashi.

Murmushi ne kwance akan fuskar sa. A hankali ta mike tace
"Let me take my bath!"

"Muje muyi!"
Ya fada yana kwasar kayan su da suka zubar anan.

Tare sukai wankan ya fito ya gama shiryawa ya haye gado yana daga kwance yana ganin yadda take kwalliyar ta, shi gani yake da gayya ma take ja masa aji, ta fesa turare yafi kala biyar can ta yo gadon tana fadin
"Baby kaci abinci kuwa? Ni kam yunwa nake ji bari na kira Peeta ko Devid su daura min indomie dan I cant eat heavy food by dis tym."

Take yaji ransa ya baci dan a yanzu ba abinda ya tsana kamar wannan ma'aikatan nata. Agogo ya kalla yaga har karfe uku a wannan lokacin zata bar wasu karati su shigo musu bangaren su. Gaskiya bai dace ba.

Cikin sanyin murya yace
"Ooo haba Baby ke indomie din ma sai an dafa miki. meyasa ke bazaki dafa da kanki ba. Yanzu sun kwanta sai ki taso su haba ance fa dare ma hutar bawa ko?"

Da yadda yai mata maganar ba zaka kawo so ne baya su suyi mata ba dan haka ta dan kwanto a jikin sa tace
"Baby ni kam I didn't now how cook indomie, kai ni even d gas cook I can't on it."

Mamaki ya cika shi yama rasa mai zaice jin yayi shiru yasa tace
"Bari na kira su nasan kila idon su biyu kawai."

"No bari na dabo miki. Tashi muje kitchen din!"
Ya fada yana fita. Da kallo ta bishi tana mamakin Fauwaz bai gajiya da yin aiki, mikewa tayi tabi bayan sa har ya kunna gas din ya daura mata ruwan indomie din. A bakin kofa ta tsaya tana kallo kitchen din da aka cika da kayan amafani. Sai kace iya amfani tayi dasu. Kallon ta ta maida kan Fauwaz da yake aikin dafa indomie sai konewa yake dan shima ba wani abu ya iya ba sosai. gun sa tayi tana fadin
"Oh my god kaga ko?"

Ta kamo hannun sa da yayi ja dan yadda ya kone tace
"Sorry!"

Ta fara hura masa hannun basu farga ba sai jin kauri sukai dan haka tayi gun tukunyar zata sauke tana kama hannun tukunyar ta saki kara dan yadda taji zafi ita bata zata tukunyar da zafi ba. Dariya yayi dan yadda tayi tsallen ya bashi dariya nan yayi gun ta ya jata wajen sink ya kunna famfo ya tara hannun. Hawaye take tana fadin
"Baby mu tafi asibiti hannu na zai cire."

Dago hannun yayi yaga yayi jajir nan uai mata tofi yana hura hannu. Gas din ya kashe ya nufi firij ya dauko musu nono ya zuba madara sukai falo suna zauna yana bata tana masa rakin hannun ta wai zafi sai sannu yake mata.

Sai da suka gama suka koma daki duk yadda yaso ya same ta ta hanashi wai ta gaji dole suka kwanta lokacin uku da rabi ma ta wuce. Sai shida sukai salllah asuba. Nan suka kara komawa bacci.

Karfe tara ya farka daga bacci bai ga Billy a gefen sa ba sai ya zata ko tana falo ko dakin ta. Wanka yayi ya shirya ya nufi dakin ta bata nan dan haka ya fito ya sauka kasa bata falo. Tsayawa yayi yana mamakin to ina ta tafi. Yana tsaye kukun su ya shigo, ya durkusa yana gaishe da Fauwaz. Bai amsa ba sai tambayar sa da yake ina Billy.

Kai a kasa cikin girmamawa yace
"Ta fita tin 7am dan yau zata amshi morning duty."

Kan kujera ya fada yana mai da numfashi kamar wanda yai gudu saboda bacin rai. tin da yai aure in dai yana cikin gidan sa to sai ran sa ya baci to me kenan da ba ruwan sa sai yadda yaga dama da rayuwar sa. Yanzu maganar Billy ta fado masa da take cewa aure takura ne da bacin rai. Shi dai shi auren ke batawa rai. Bacin ran da yake ji har ji yayi kirjin sa na zafi da nauyi.

Peeta dake tsaye akan sa yana kallon ikon Allah yace
"Are all right Sir!"

Kai kawai ya gyada masa.
"Ok sir ur food in on the dining!"

Da hannu yai masa alamar da ya fita dan ko magana bai son yayi dan yadda kijin sa ke bugawa saboda bacin rai. Dining din ya kalla an jere masa kayan abinci amman duk yadda yake da ci sai yaga ko sha'awa abin bai bashi ba.


*Ina mai kara baku hakuri dan naga comment dinku kuna cewa na dada yawan rubutun dan Allah kuyi hakuri da wannan. Aka ce da babu gwara ba dadi da ba zan mayi typing din ba dan ba lokaci da kyar na samu nayi wannan. Ina fatan zaku fahimce ni. Abubuwa ne sukai min yawa. Pls kuyi ta sakani a addu'a. In na samu dama gobe zan muku typing da yawa insha Allah! Nagode da yadda kuke nuna kin soyayya akan littafin nan. Wallahi ban taba zata littafin nan zai amsu ba. In ba zan manta ba ina jin shine rubutu na na farko amman Allah bai ban damar fara rubuta shi ba sai yanzu. Sai gashi ya shigo da kafar dama dan masoyan sa na da yawa wasu na san su wasu ban san su ba. Alhamdulillah ina godiya Allah ubangiji ya bar kauna. Madallah da kulawa.*

Ni da Yaa FauwazWhere stories live. Discover now