*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_5⃣5⃣ - 5⃣6⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and Exhortate our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy na da Mommy nah)*
Tinda suka fita ba wanda yace da dan uwan sa kala har suka shiga harabar gida. A parking space yai parking zata bude kofar taji ta a rufe juyowa tayi ta kalle shi. Maimakon ya bude sai ma ya kwata a jikin kujerar motar. Fuskar sa cike da damuwa da ta rasa ta mecece.
Hannun sa takamo tace
"Yayan mu wai me yake damun ka, damuwar ka ba daya bace, ka sani in har kana cikin damuwa nima ina cikin ta domin kuwa ba zan iya wani abun kirki ba ko a ckul in na koma. Ka daure ka gaya min meke damun ka. Na lura tin jiya da nace zan taho ka canja."Kama hannun ta yayi yana matsawa a hankali sannan yace
"Tabbas ina cikin damuwa Yasmeen. Damuwa ta tana da yawa na san wasu ban san wasu ba. Zaman ki a gida na yasa na fara gane nayi kuskuren auren Billy domin kuwa ya dace na auri macen da zata na kula da hidama dani amman sam Billy bata san wannan ba sai dai ni nayi mata hidima ita tana zauna. Ace mace ba zata iya gyara miki gadon da kuka kwana ba bare ta wa mijin ta girki yaci yaji dadi ya saka mata albarka. Bata san komai ba. Tayi shigar da ta ga dama ta fita da ita in nai mata magana ma ba dainawa zatai ba dan ita bata yadda da tayi badai dai ba. Sam ba zance tayi abu tayi ba. A farko da Marzuk yaban shawara akan na gyara ta amman sam Billy ba irin wadan da ake gyarawa bane kiga fa yanzu kinje gidan amman ganin dabi'un ki sam bai sa tana kokarin canja nata ba sai dai kullum ai mata gyara akan laifi daya......"Take tausayin Yayan ta ya kamata dan tabbas yana cikin damuwa sosai, ace kayi aure baka da kwanciyar hankali da samun kula da tarairaya. To me zata ce masa yanzu shi ya dauko ruwan dafa kan sa yanzu dai hakuri zata kara bashi. Amman kuma lallai Anty Billy na wasa da damar ta. Ina ma ita ta samu Yaa Fauwaz da ya samu dukkan kulawar da yake bukata har ma fiye da haka. Da ta maida shi autan maza. Dan tasan samun namiji kamar Yaa Fauwaz abu ne mai wuya amman Anty Billy ke wasa da damar da Allah ya bata. Menene aibun Yaa Fauwaz babu mai kyau ne yana da kudi da ilimi da sanin ya kamata to me kuma zaka nema.
Cikin lallashi tace
"Yaa Fauwaz, ka sani komai na duniyar nan kaddara ce, kuma dole kana hakuri Allah bazai taba hada maka dukkan abinda kake bukata ba kai ma kasan haka. Ka godewa Allah da ya baka iyaye masu son ka da har suka baka tarbiyya da ilimi ya baka zuri'a mai albarka, gani kanwar ka mai son ka da damuwa da damuwar ka, baka da matsalar komai, kaga dan Allah ya jarrabace ka da mace Kamar Anty Billy bai kamata ka butulce masa ba ka cigaba da masa biyayya insha Allah komai zai zo da sauki. Kasan Allah baya hada wa bawansa komai dole zai tauye bawan sa yaga taya zai amshi kaddarar sa. In har kaci jarabawar ka kuma kana da lada agurin sa. Kayi hakuri ka jure kaci wannan jarabawar taka, insha Allahu, Allah zai sauya maka komai a sannu. Nasan dole a zaman ku ba zai taba yiyuwa ace bata taba kyautata maka ta wani fannin. Dan haka yanzu abinda zance maka shine duk lokacin da tai maka abu ka dubi alherin ta a gareka. akwai wata kissa ta sayadina Umar (AS) wani mutun matar sa ta bata masa rai har ya fusata ransa ya baci dan haka sai ya tafi ga Sayyadina Umar sai ya aika ai masa sallama dashi yana waje yana jiran sa sai yaji muryar matar Sayyadina umar na fada da gaya masa magana. Dan haka sai ya juya zai tafi dai dai lokacin da Sayyadina Umar ya fito kenan. Sai yace ya ka aika nazo zaka tafi kuma. Sai wannan mutuni yace ya "Amirul mu'iminina daman na kawo karar matata ne sai na jiyo mai dakin ka na daga murya akan ka kuma baka cemata komai ba." Sai sayadina Umar yace "eh ai idan ta bata min ta wani gurin tana kyautata min ta wani gurin domin tana dauken bukata ta, ta hananin zuwa ga zina sannan tana haifar min ya'ya ta shayar dasu.
To kaga kai ma dole akwai abinda take maka ko yaya ne da zai faran ta maka dan haka kana kasancewa mai ganin alherin ta sannan kana mata addu'a."

YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasyLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.