*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_9⃣5⃣ - 9⃣6⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and Exhortate our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy na da Mommy nah)*
------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------
Kan Yamma numfashin ta ya zama normal, dan haka har an cire mata oxygen sai allurar bacci da akai mata take ta aikin Bacci. Mommy zaune a gefen ta sai addu'a take mata tana share hawayen idon ta sam ta kasa daina kukan ta.Sai magariba sannan ta farka da kuka ta tashi nan Mommy tayi kanta tana ta lallashin ta ganin Mommy ma na kuka sai tayi shiru dan bata son ganin Mommy na kuka bama akan ta ne.
Likita ya shigo ya duba ta sannan ya ce ta sha tea da abinci a bata magani, dan haka Mommy ta taimaka mata tai wanka sannan tai alwala tayi sallah daga zaune sannan Mommy ta hada mata tea ta bata abinci ta bata magani ta sha ta koma ta kwanta.
Bata jima da kwanciyya ba yan gidan su suka dinga shigowa suna duba ta. Baba da Mama suma duk sunzo da su Yaa Nazir da Yaa Ishaq. Abban ta ne bata gani ba da Marzuk da Yaa Fauwaz wanda daman shi bata san yazo ko bai zo ba.
Yadda ta ga yan uwan ta tasamu ta dan sake sosai. Dan har karfe goma suna nan sannan suka tafi.
Washe gari kuwa da safe aka sallame ta dan haka sukayi gida amman sai tace ita wajen Anty Binta zata tafi.
Tana shiga taga Aisha nan ta fada jikin ta tana sakin kuka. Nan ta hau lallashin ta, tana kwantar mata da hankali, Anty Binta ce ta shigo, nan ta zauna ana tana mai da magana anan Take fadin ashe mahaifin Abbas yazo ya bada hakuri, har suma Abbas yayi dan mahaifin sunki amincewa,
"Kiyi hakuri. Allah yasa haka ne mafi alheri.!"Haka yan uwa ta suka taru duk ana bata baki da kwantar mata da hankali.
++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++++
Sai dare da Abba ya dawo Ummi take fada masa abinda ya faru tana fadin
"Kai Abban Yasmeen ban san meyasa sam baka damu da Yasmeen ba yarinyar nan tana bukatar kulawar iyayen ta fa amman an kama an bada ita a wani aje!""Rufe min baki. Wallahi kulawar da Yasmeen take samu ko agun ki baza ta samu kulawar da take samu ba. Su Yayan ne wasu ki kula da abinda zaki fada. Ni na cire Yasmeen a lissafin ya'yan da na haifa dan na barwa Yaya da Yaya dan haka ba ruwan ki da har kar su. Kuma in naje me zan mata addu'a ce kuma ina daga nan ma nayi ta isa"
Ya mike yabar mata wajen.*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-
Washe gari tana kwance duk garin ba dadi ji take kamar komai akan ta aka saukar mata. Ta kasa yadda wai auren ta aka fasa, tana wannan tunanin Anty Binta ta shigo kallon ta tayi yace
"Yasmeen tashi kiyi wanka ko kya ji dadi."Baki ta turo ta kalli hannun ta da yaji lalle kamar a lokacin aka gama zanawa tace
"Anty please ki nemon abinda zan goge lallen nan in daina ganin sa. Hankali na yana dada tashi."Anty Binta tace
"Haba Yasmeen ya za'ai ya fita kina amarya!"Da sauri ta dago tana kallon Anty tace
"Anty Abbas din yace da wasa hake ko?"Tausayin yasmeen ya kama Anty dan tin da jiya da aka sallamo ta take wasu abubuwa kamar bata cikin hayaicinta. Tayaya mutumin da ya ce ya fasa har an daura aure ya dawon yace a aura ai kam ko iyayen sa ce a'ah. Dan haka tace
"A'ah su Alhaji Babba sunce acigaba da biki kamar yadda aka tsara."Kuka Yasmeen ta saki, Anty Binta ta huu lallashi haka Aisha ta shigo ta same su itama ta zauna aikin laashin.
*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+*+
Lokacin da Halima taji abinda iyayen Abbas suka zo akan suna neman auren Halima murna kamar me haka ta dinga ji. Dan haka take ta kira Billy tace ta turo mata number kawar ta sannan ta shaida mata abunda yake faruwa. Itama ta taya ta murna sosai.
Dan haka a lokacin ta kira ta ta fada mata ta tambayi boka nawa yake bukata zata aiko masa. Nan taje gun sa ya fadi abinda za a bayar ta daura nata itama. Haka Halima ta tura bataji zafin fitar kudin ba.
Wanda a lokacin aka daura musu aure, kuma anyi shagali ba kadan ba dan ma abin bai zo a yadda aka so na.
Abbas kuwa sam ya kasa gane inda kan sa yake. Dan boka ne ya aiko masa da aljannukan yana shiga garin Adamawa ya ji ba wanda yake so sai Halima. Nan yaje ya sawa iyayen sa rigima yace shi sam Halima yake son ya aura da Mahaifin sa ya hau fada yace ba za ai auren ba shine ya zube musu. Ganin haka yasa Kanin Mahaifin sa yace ai masa yadda yake so din. Sam shi bai ji yana farin ciki da wannan abin ba dan duk hankalin sa na can wajen Yasmeen. Ya rasa gane me yake faruwa. A haka aka gama biki suka tare da amarya lafiya.
*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-
"Wai Yasmeen ba zaki tashi ki shirya ba ga mutane na can suna jiran amarya!"
Anty Binta ta fada.Baki Yasmeen ta turo tace
"Nifa gaskiya Anty ba zani ba, haka kawai ban san waje mijin na fa.""Au ba zaki tashi ba kuwa Yasmeen dole ne sai kinsan mijin? Wallahi in baki shirya ba sai na fadawa Mommy!"
Cikin kuka ta mike ta fara zira kayan da Antyn ta fiddo mata.Fita tayi ta kira mai make up din suka shigo a tare. Tana ganin su ta kara bata rai ta ce
"Anty ni kam bana son wannan kwalliyar!""Kar kiso man Mommy ce ta aiko in kuma ta koma tafada mata ne bismillah!"
Fuska a hade haka akai mata make up din simple. Duk da fuskar taba walwala haka aka gama. Kwalliyar tayi kyau dan da ta fito falo duk wanda ya ganta sai yace tayi kyau.Gurin bridal shower din ya hadu sosai, yan matan amarya duk sunyi kyau, cikin pink din material. Amarya Yasmeen kuma tayi kyau cikin blue din material mai white stones ta saka fashion din farin dan kunne da sarka.
Su Aisha da Siyama da su Anty Asabe sai rawa suke sun raya wajen sosai. Haka akai hutuna kawayen ta duk yan ckul sun zo kuma sun mata banjinta ansha rawa da hutuna aka tashi.
Washe gari akai kamu anan compound din gidan Anty Binta akayi anyi decoration din wajen. Mommy da su Mama su suka kama ta. Amarya tayi kyau cikin wani jan Less mai adon baki. Sosai tayi kyau an mata make up. Duk yan uwan ta sunzo daga dangin Mamin ta har dagin Mahaifin su a na su Mommy. A wajen sam ba dangin ango sai danginta na uwa da na uba da abokan arziki.
Morning and have a happy weekend

YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasyLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.