77-78

435 31 0
                                    

*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_

7⃣7⃣ - 7⃣8⃣

Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*

Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and  Exhortate our readers)_*

Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_

*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy na da Mommy nah)*



Bayan tafiyar maneman auren Yasmeen, Abba ya kira Fauwaz bayan Fauwaz ya dau waya uace
"Iyayen Abokin ka ne suka zo neman auren kanwar ka shine na kira naji ya halayar sa suke."

Kirjin Fauwaz ne ya buga dan fargaba bai taba zaton abun zai zo da wuri haka ba. To shime zai ce dan Tabbas Abbas bai da aibu ko kadan, da Siyama yace yana so da ya shige masa iya karfin sa amman Yasmeen ba zai iya ba saboda itama zabin sa ce. Farin cikin rayuwarsa.

Ba zai iya bata abokin sa akan son da yakewa Yasmeen ba amman dole yasan abun da zai yi tinkan wankin hula ya kai shi dare. Alhaji ne yace
"Ya dai ko akwai matsala ne!"

Firgigit yayi yace
"A'ah Alhaji ba wata matsala,"

"Ka tabbata?"
"Eh Alhaji."

"To masha Allah! Ina son ka karai min bincike kan lokacin dan na dakatar dasu har Yasmeen ta dawo naji daga gare ta."
"Insha Allahu Alhaji."

Nan sukai sallama. Ya fada kan gado yana danne zuciyar sa wani tari ya tasar masa sai da ya shafe kusan minti ashirin sannan ya lafa masa. Idon sa yai jajir ya mike ya dauki ruwa ya sha ya koma ya kwanta kansa na sara masa.

Bacci yake so yayi amman ya kasa saboda tunani abun da Alhaji Babba ya fada masa duk ya shiga tashin hankali. Yana kwancen nan bai ankara ba sai ganin asuba tayi yayi nan ya muke yai wanka yai alwala yai sallah. Ya jima akan sallaya yana kai kukan sa ga Allah sannan ya mike ya fada saman gado saboda kan sa dake masa ciwo.

Tin daga lokacin ya kara fita haiyacin sa ya rasa tunanin tayaya zai yi ya samu Yasmeen shin Mommy zai sama kowa? Lallai a da ya tafka babban kuskure na kin amsar Yasmeen yanxu kuma ya dawo yana jin ita kadai ce fari cikn sa burin zuciyar sa.

Taji dadin garin sosai, dan yadda yan uwan ta ke jan ta a jiki da kuma nuna son su da kulawa da ita. Kullun suna waya da Mommyn ta Aisha ce dai sam ta kasa kiran ta dan sai taga in ta kira ta bata fada mata abun da ya faru ba kamar taci amanar ta ne.

Sosai Muhammad ya matsa mata da kira da sakonnin sa. Abbas ma suna dan yin waya amman ba sosai ba. Sai Yaa Fauwaz da kwana biyu sam bai kira ta ba itama da ta kira dukka layukan sa a kashe suke.

Likita yai masa fada sosai dan jinin sa ya hau ga zuciyar sa da take gab da kamuwa da ciwo dan sign din ta ne yake tambayar sa. ya bashi shawara akan lallai ya nemi abunda zuciyar sa ke so, in kuma wani abu ne baya so ya cire shi a zuciyar sa ya rage kuma tunani.

Sai da ya koma gida ya sha magani ya dan ci abinci ya kwanta tunani ya dawo masa sabo indai dan yawan tunanin Yasmeen ne da kishin ta ya yadda ya jima yana son Yasmeen, kenan duk abun da yake mata har da dan yana son ta ne. Ya illahi yanzu wa zai tara da zancen yana son Yasmeen bayan a da yace baya son ta, ya gama fadam bason sa take ba. Amman kuma Marzuk yace masa tana son sa, ikon Allah lallai in har tana son sa a da yasan a yanxu bata son sa dan gashi ta amshi soyayyar Abbas in tana son sa ba zata taba amsar son wani ba. To kai baka son ta tayaya zata tsaya tana son ka. Ko a da yasmeen ta so ka yanzu zai yi wuta ta soka. Duk wannan maganganun yana yi da zuciyar sane. Ganin wani zazzabi na neman rufe shi da ciwon kai yasa ya lumshe ido dan sosai likita yai masa gargadi akan ya rage tunani da saka abinda zai bata masa a ransa.

Tunanin sa daya tayaya zai tunkari Yasmeen ko wani da maganar nan.


Su Yasmeen sun dawo lafiya inda kowa a can bai so tahowar ta ba dan an saba da ita sosai dan Yasmeen akwai shiga rai sai dai baku zauna tare ba. A nan gida kano ma sai murnar dawowar su ake yi.




Ranar da suka dawo a ranar Yaa fauwaz ya dira shima gidan sa na can Cbn quarters yaje yai wanka ya canja kaya ya taho gida. Lokacin da ya shiga gida kowa ya ganshi sai yai magana dan ya rame sosai.

Lokacin da ya shiga dakin Mommy ya samu Yasmeen zaune akan kujera tan dane danne a waya. Wani kallo ya kure ta dashi sai a lokacin Fauwaz ya gane Yasmeen kyakyawa ce ta karshe. Doguwar riga ce a jikin ta sama ya kamata kirjin ta ya bayyana sosai wanda suke a cike. Fatar ta ta dada kyau da haske, sai sheke takeyi, sai a yau ya kara sanin lallai Yasmeen abar so ce dan tafi Billy komai haske kawai Billy zata nuna mata da wayewar zamani. A ransa yace lallai da ya bar Yasmeen kula samari yasan da yanzu tayi aure, in kuwa tayi aure shikenan ya rasa ta yana tina haka ya ringa godiya ga Allah. Amman kuma yana tunanin ta ina zai fara ne.

Zama yayi yana mai da numfashi wannan yasa ta dubi inda ya fada ya zauna. Kallon sa tayi ta saki murmushin ta mai kyau da ke kara mata kyau ta mike ta koma kan kujerar da yake tana fadin
"Ashe ka dawo"

Idon sa a lumshe dan bai son ya kalle ta dan wani abu yaji yana yawo a jikin sa wanda yasa tsigar jikin sa gaba daya ta tashi. Muryar ta ta kara haifar masa da kasala, sai a yanzu ya fara jin wani feeling na daban game da Yasmeen.

"Na dawo Princess kun dawo lafiya?"
Kai ta gyada tana bin sa da kallo yadda duk ya rame. Dan haka cikin damuwa tace
"Big bro baka da lafiya ne?"

"Me kuka gani?"
"Duk ka rame fa. Please me yake damun ka?"
Tayi tambayar cikin damuwa kamar zatai kuka.

Idon sa ya bude da sukai jajir ya dago hannun sa ya safi gefen fuskar ta yace
"Kar ki damu kai na ne ke ciwo kawai!"

"Ciwon kai? Amman kasan ciwon kai signing na wani abu na damun kane ko? Kaje asibiti? Ka fadan me kake ji na baka magani please Yaya na!"
Ta karashe maganar kamar zatai kuka.

"Uhmm kar ki damu naje asibiti na sha ma magani tafiyar da nayi ce ta karan ciwon amman am ok kinji."
Kai ta gyada. Wayar ta ce ta hau kara tana dubawa taga Abbas ne.

Dauka tayi da sallama. Tace
"Ina yini?"
"Lafiya kin dawo baki fadan ba ko?"

"Am sorry yanzu nake tunanin ka wallahi. Mun dawo lafiya ka kwantar da hankalin ka."
Kirjin Yaa Fauwaz ne ya dinga bugawa kamar zai fito waje saboda yadda yaji Yasmeen na fadin tana tunanin wani da maganar da take masa.

Tari ya hau yi da sauri ta katse wayar ta nufi firij ta dauko masa ruwa dan kamar kwarewa yayi ta dawo tana shafa masa baya a hankali. Sannu a hankali ya fara lafawa har ya dauke ta bashi ruwa ya sha sannan ta hau jera masa sannu. Ya jima a zaune idon sa lumshe har yaji abun ya lafa masa dan haka ya mike ya fita.

Ni da Yaa FauwazWhere stories live. Discover now