*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_9⃣9⃣ - 1⃣0⃣0⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and Exhortate our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy na da Mommy nah)*
Har Mota Mommy ta saka ta da kyar suka rabu da Yasmeen ita kuka Mommy kuka a haka Mie Mie da Anty Yagana da kanwar Abba, Amina da tazo daga waje suka tafi kai ta gidan ta.
Gida ne madaidaici dan Abba shi ya bawa Yaa Fauwaz sannan ya zuba komai na cikin gidan yace kan ya hada su da matar sa in zai hada kenan.
Kana shiga compound ne sai barander in ka shiga katon falo ne mai kofofi guda hudu biyu na passing each other biyu kuma suna makwabtaka da juna masu passing junan su daya bangaren Yasmeen ne dayan na Yaa Fauwaz wanda yake da kofa da zata fitar da kai compound din gidan. Kofofi biyun dake makwabtaka da juna kuma main kitchen ne da toilet.
Bangaren Yasmeen yana dauke da dan corridor wanda a corridor akwai toilet da kitchen sai kofar da zaka kai ka falon ta a cikin falon akwai bedroom da toilet. Haka ma bangaren Yaa Fauwaz yake amman shi ba kitchen a falo da bedroom ne da toilet.
An kawata Main falon da kujeru Milk kala da labuyale suma milk sai kayan kallo bakake. Daga can gefe aka saka dining da durowar da firij. falon yai kyau ba tarkace sosai amman yai kyau.
A falon ta ne aka saka showglass na turaren wuta da maroon kalar kujeru da labulaye haka ma bedroom dinta. Gaba daya kitchen dinta Mommy ta cika mata su da kayan amfani na zamani da tsada masu kyau.
Suna zuwa Mie Mie ta saka tayi bismillah sannan tace ta shiga da kafar dama duk yadda ta saka tayi haka tayi suka karasa har bedroom din ta dake tashin kamshi suka zaunar da ita. kamshi da sanyin dakin ya mata sosai. Dan haka tana zama ta sauke ajiyar zuciya. Nan yan matan amarya suka fara shigowa ana kallon dakunan ta ana fita. Ita kam tana zaune agefen gado kanwar Abba na mata nasiha cikin lallashi da kwantar da hankali. Ahaka suka gama suka fice.
Aisha da wata yar school din su ne suka shigo hadi da Siyama da sai rawar kai take an zama yan mata. Nan Aisha ta hau mata shakiyanci tana fadin
"Nada gobe ina zuwa ba wannan kukan dan kin samu nutsuwa wajen mijin ki wanda kike so!"Bata so tamka musu ba amman ta dage mayafin kan ta tace
"Please Aisha kin san wanda aka aura min?"Kai ta girgiza tace
"A'ah!"Siyama ta kalla tace
"Kefa Sister?"Wani murmushi tayi zatai magana aka kira ta a waya tana dubawa taga saurayin ta ne abokin Yaa Fauwaz da suka zo bikin Abbas kuma bai yiyu ba sai suka zauna aka maida Kan Fauwaz shi yaga siyama suka kulla soyayya dan haka dauka taui ta fita tana fadin
"To Anty Yasmeen sai kinganni nan da sati biyu kila."Ta fice. Mayafin ta maida ta rufe fuskar ta ta kwanta tana mai cigaba da kuka. Gidan suka dan kinkimtsa mata sukai mata sallama. Aisha ce ta shigo a karshe tana fadin
"Amarya ni kam ina jin sallamar kenan dan gobe da safe zan tafi."

YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasiLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.