49-50

587 35 0
                                        

*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_

4⃣9⃣ - 5⃣0⃣

Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*

Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and  Exhortate our readers)_*

Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_

*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy na da Mommy nah)*



Zaman gidan ne ya ishe ta dan Yaa Fauwaz ya fita, Anty Billy ma ta tafi gun aiki dan yau na rana take sai magariba zata dawo. Wajen su Bintalo da Talle taje tace suzo su rakata ta zagaya unguwar su.

Sun fita sunje bayan layi sun dawo dai dai kofar gidan sukaji ana sallama. Juyowa dukkan su sukayi. Yasmeen ta amsa da
"Wa'alaikum salam!"
Ba tare da ta kalle shi ba.
"Dan Allah minti daya man!"

Juyowa tayi ta kalle shi, dogone amman ba can ba dai dai. bai da wani kiba fari ne tas kyakyawa da shi daga gani hutu ya ratsa jikin sa dan yadda fatar sa take luf luf da ita. Bakin sa pink kala. Kwarjini yai mata dan haka bata kasa magana sai cewa tayi
"Wa kenan?"

Nuna ta yayi da yatsa, yana sakin wani murmushi wanda ya karai masa kyau. Tana ganin masu kyau amman bata taba ganin irin nasa ba sai kace aljani.
"Ke!'

Ya bata amsa. Ciki su Talle sukai ta kalle shi tace
"Ina jin ka! Lafiya dai ko?"

Ta fada fuska ba fara'a
"Haba yan mata ki saki fuskar mana, da farko sunana Ahmad yanzu naga kunzo wucewa shine kikai min sata!"

Ido ta zaro tace
"Sata kuma? Me na satar maka kalli ni ba abinda na satar maka kaga hannu na."

Ta daga hannayen ta. Murmushi yayi yana kallon ta kanar wanda ya samu tv, dan yadda komai nata yake burge shi. Yadda ta zaro idon ta sai suka kara kyau. Dan haka yace
"Kwantar da hankalin ki ai na bar miki abinda kika satar min fata na dai kawai nima ki ban irin shi na wajen ki."

Duk ta rasa gane abinda yake nufi gashi sai murmushi yake, yadda fuskar ta ke cikin tsoro shi ya fi masa kyau a gare t. Ya zaga kasashen duniya amman bai taba ganin macen da ta burge shi ba. Wacce son ta ya shiga lokaci daya a cikin zuciyar sa.
"Ke yanzu baki gane abinda nake nufi ba. Anya kuwa ke bahaushiya ce, gaskiya kin fi kama da larabawa. Bari na fada miki abinda nake nufi to, tinda na ganki ki satar min zuciya ta wanda na biyo ki nima ki bani taki, kinga sai mu mucanje ko?"

Wata ajiyar zuciya ta sauke, tare da dafe kirji ta dan harare shi tace
"Amman wallahi ka dau hakki na dan ka bani tsoro."

Hannu ya hade gu daya ya dukar da kai yana fadin
"Am sorry princess ban yi hakan dan na tsoratar dake ba."

Murmushi ta tsinci kan ta da yin, dan ba karamin burge ta yake ba.
"To ni tinda ka gama zolayar taka ni zan shiga dan na gaji wallahi."

"Ayyah sorry gaskiya kam kije ki huta kar jikina yai ta ciwo kinji, amman kan ki tafi ki ban number ki dan Allah!"
ya hade hannayen sa alamar roko. Kallon sa tayi taga yadda langwabar da kai alamar yana neman taimakon ta. Bata san lokacin da ta fara karanto masa number ta ba tana gamawa ta shige gida tana fadin
"Bye!!"

Ni da Yaa FauwazWhere stories live. Discover now