65-66

531 29 0
                                    

*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_

6⃣5⃣ - 6⃣6⃣

Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*

Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and  Exhortate our readers)_*

Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_

*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy na da Mommy nah)*

Ranar sam bata ga Yaa Fauwaz ba har suka dawo daga make up suka shirya suka tafi gun dinner. Abbas na ganin ta ya koma wajen ta. Sun sake sosai dan Yaa Fauwaz bai zo ba sai hirar su suke yana kallon yadda bakin ke wakana cikin tsari. Da aka ce ango da amarya su fita ango ya dinga mata liki sai abin ya birge Abbas yace
"Yasmeen Allah nuna mana namu kamar haka."

"Amin!"
ta fada dan ba dadi ace ana son ka kai kana nuna kin sa a fili. Ai kam yaji dadin amsar da ta bashi. Nan ya dinga mata hira a ciki ya fada mata tarihin sa da komai na rayuwar sa bai boye mata komai ba. Sai taji ya burge ta.

Yaa Fauwaz kuwa yau da safe ya nufi gidan sa, a falo ya samu Billy dan aikin dare ne da ita kuma bata da lectures safe. Daga ita sai wani gajeren wando da karamar riga. Tana zaune devid na gyara mata kafa. Turus yayi yana kallon su ko dagowa batai ba duk da taji sallamar sa. Devid kuma ya cigaba da abinda yake yi.
"Tashi ka fitar min a daki."

Yaa Fauwaz ya daka masa tswa. Jiki na bari ya mike zai fita. Billy tace
"Kamar ya? ya fita bayan kaga aiki yake min."

Tsayawa David yayi Yaa Fauwaz yayi kan sa a zafafe ai da sauri ya fice. Dawowa yayi yai mata wani irin kallo da sai da ta ji kirjinta ya buga sannan yace
"Wallahi Billy ke jahila ce. In ba jahila ba kalle ki fa kalli shigar ki wai wani kato yazo y kama kafar ki yana gyara miki. To baki isa ba wallahi wannan dabi'ar taki dole ki canja in ba haka ba zaman mu sam ba zai yiyu ba. In banda rashin sani da jahilci katon namiji yana taba ki kawai da zumar gyaran jiki an kalli shirgar ki ko kishin kan ki bakya yi."

Ya buga wani tsaki ya shige ciki yana mai cigaba da aika mata wannan kallon da yafi komai tsaya mata a ran shi ya hanata magana dan Fauwaz bai taba mata irin haka ba a gaban yan aiki ya koro mai mata abu a da sai dai yace zaiyi mata su harshi amman yanzu ya kore shi sannan yazo yana fada mata ita jahila ce bayan yanzu ma masters take yi amman yake ce maga jahila. Har yake cewa zaman su ba zai yiyu ba. Tabbas akwai abin da Fauwaz ya taka.

Bai taba mata irin wannan abun ba. Bare yai mata kallon banza amman yau kallon tsana ma yake mata lallai abun abin tsoro ne.

Kawar ta ta kira tana fada mata abinda ya faru. Wata dariya tayi tace
"Ai dole yai miki haka ba ya dawo ya sameki a cikin gdansa ba kinki ki koma gidan ku. Kadan ma kika gani daga cikin wulakancin d'a namiji in dai zaki zauna yana taka ki."

"Yanxu ya zanyi?"
Ki bari anjima in mun hadu ma san abi yi."

"Ok shikenan bye."
Ta kashe wayar. Kan kujera ta fada tana mai lumshe ido. idon ta ya fara hango mata yadda ya kara kyau da jin hutu. Ko ba komai tana son Fauwaz dan kyan sa da kuma baiwar da Allah ta bashi dan in dan kudi ne tana dasu mahaifin ta ma haka.


Ni da Yaa FauwazWhere stories live. Discover now