*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_7⃣ - 8⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com*
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlightenment and Exhortation our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_Dagowa yayi bayan ya gama wayar yana mai cewa
"Wow! My princess kinyi kyau fa kai wannan sister tawa ba dai kyau ba."
Sanye take da arabian gown orange kala sai mayafin ta ba wani kwalliya tai ba daga powder shikenan sai man lebe sai turare da ta fesa sai wani half cover takalmi mai tudu da ta saka da jaka duk brown. Bata yi magana ba domin a dane wannan kodawar tasa ke faranta mata taji dadi yanzu kuwa ta gane duk yaudara ce.
"Taho mu tafi."
Ya fada yana mikewa ganin bata da niyyar magana. Yai gaba tabi bayan sa tin dazu taso tai tafiyar ta Yaa Ishaq ya kai ta sai kuma tai tunanin in har ya tambaye ta dallili me zatace masa wannan yasa ta hakura kawai ta jira yazo suje taren. Bangaren Alhaji Babba suka je suka gaishe shi ya miko kudin registration din ta amman sam Fauwaz yace shi zai mata komai dole Alhaji Babba ya hakura ya dinga sa musu albarka.A wata sabuwar motar sa ya dauko ta shiga gidan gaba. A haka suka karasa BUK tinda suka shiga ckul din suke gaisawa da mutane wandanda ke matukar sonsa. sam bai da girman kai zai tsaya suyi musabaha har wasu suyi hoto ma. Ita kam har ta gaji tai gaba abin ta da ya hango ta da gudu ya karasa yana bawa fans dinsa hakuri. A can gun screening ma hakan ce ta faru amman da yake dashi nan da nan akai mata suka fito dan zuwa banki yai mata registration. Duk tai sanyi dan har ga Allah ta gaji bata saba wannan hada hadar ba. Har da su haki. Kallon ta ya tsaya yi yana dariya yace
"Yarinya yanzu kin girma dole kina daurewa ko zirga zirgar zuwa hall din lecture ma ta ishe ki, daga dan wannan tafiyar zakice kin gaji."
Fuska ta marairaice tace
"Wallahi big bro na gaji."
Dariya yayi gaban ta ya duka yace
"hau in goya ki."
Dariya ta saki tana yin gaba tace
"Haba dai yanzu fa na girma."
Biyo ta yayi yana dariya. Suna zuwa jikin motar sa kamar daga sama suka ji ance
"My Fauwaz!"
Cikin siririyar muryar ta mai dadin sauraro. Da sauri suka jiyo shi da Yasmeen. Billy suka gani. Fauwaz ya saki murmushi, Yasmeen kuma sai taji wani abu ya cunkushe masa, a zuciyarta kai ta dauke. Ta karaso tana fadin.
"yanzun nan ina parking na hango ku."
Ta kalli Yasmeen tace
"Sister ya kike?"
Juyowa Yasmeen tayi tana murmushi da bai kai ciki ba tace
"Lah ina yini?"
"Lafiya."
Ta fada tana kallon Fauwaz tace
"Me ya kawo ka ckul din mu."
Yasmeen ya kalla yace
"Pincess muka zo screening."
Kallon Yadmeen ta kara tace
"Oh har zata shiga university wane course?"
"Medicine ne!"
Ya bata amsa.
"Masha Allah gashi mu mun gama ke kuma yanzu kika shigo ai da ina nan da mun dinga gaisawa ko?"
Kai Yasmeen ta gyada kawai. Fauwaz ta kalla tace
"My Fauwaz kanwar ka ba ruwan ta so silent and she is beautiful dan ta fika kyau duk wannan kyan naka."
Yasmeen Murmushi tayi kawai ta dukar da kai. Shi kam Fauwaz dadi yaji Billy na son kanwar sa. A haka hira ta barke tsakanin sa. Tin Yasmeen na tsaye har ta gaji ta bude motar ta zauna amman nan ma basu bar hirar ba ita ga kishi na nukurkusar ta. Sun fi awa da taga ba mai karewa bane kawai sai ta bude kofa ta fice tana fita ta tsaida Napep tayi gida. Tin tana hanya taji kiran sa a wayar ta amman sam taki picking. Tana shiga ta tadda mommy a kitchen duk masu aikin su Mommy bata yadda su mata girki ba sai dai wanke wanke da shara da wasu aikin. Nan tace
"Mommy sannu da aiki."
Mommy tace
"Har kun dawo?"
"Eh mommy!"
Ta hau sama ta canja kaya ta sauko dan taya mommy aiki. Dan Mommy ta hora Yasmeen akan aiki da girki ba dan bata son ta ba sai dan gidan aure zataje bata yadda ace yar ta bata iya girki ba. Wannan nawa Baba da Mama dadi dan yadda Mommy ta rike Yasmeen tamkar ita ta haife ta. Dan Kanwar maman ta Nusaiba Ita ta soma sanar da ita cewa Mommy ba maman ta bane. Ansha daru a family din wai dan me ta fada tace dan yarinya tanawa uwar ta uwar ta addu'a da Baba yaji haka sai yace kuma tayi gaskiya to anan ne fa aka fada mata Mamanta ta rasu Nusaiba Umma itace maman ta Abba kuma Baban ta amman duk da haka soyayyar dake tsakanin su da Mommy bata gushe ba sai ma kara sata a hanya da take akan tanayiwa mahaifiyar ta addu'a. Ta kan zuwa wajen Umma da Abba ta gaishe su jifa jifa

YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasyLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.