*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_1⃣1⃣3⃣ - 1⃣1⃣4⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and Exhortate our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a adidu'a Mommy na da Mommy nah)*
02:30pm ta farka, baya dakin dan haka ta mike a hankali ta shiga toilet ta hada ruwan zafi ta shiga ta sauya ruwa yai sau uku sannan ta bude wata durowa a toilet ta dauko wani abu da mai gyaran ta ta bata ga goga a gaban ta sannan ta mike tayi wanka ta dauro alwala. Sosai taji wajen ya saki amman jikin ta duk babu gwari ji take kamar iska zata iya daukar ta.
Sallah tayi sannan ta shirya cikin wata doguwar riga sannan ta fice ta tafi kitchen. Kayan miya ta deba ta gyara sannan tai blending ta markada ta daura akan wuta. Kaza ta dauki ta yayyanka sannan ta wanka ta zuba a tukunya ta yanka albasa ta saka tafarnuwa da kayan kamshi sannan ta saka magi ta daura akan wuta. Bayan ta tafasa kazar ta sauke ta soya ta juye man akan kayan miyar ta soya su ta gama ta tsaida ruwa da ruwan da ta tafasa kazar ta saka magi da kayan kamshi da curry nan da nan gidan ya dumame da kamshi.
Ruwan cus cus ta daura sannan ta yanka carrot ta zuba a tukunya ta zuba sugar saboda kar kalar sa ta canja ta zuba green beans bayan ya razana ta hada shi cikin cus cus din yai kyau sannan tayi hadin carbage wanda yaji egg da hanta ta saka carrot da cocumber da bama a ciki sannan ta saka a frij. Zobo ta tafasa wanda yaji kayan kamshi. ta tace shi sannan ta zuba sugar ta markada cocumber ta tace ta zuba ciki ta saka a firij.
Tana gamawa ta shige ta kara wanka ta fito ta turare jikin ta sannan ta wurare gidan. Shirya tayi tai kwalliya ta saka wata rigar ta mai hannun shimi iyakar ta cinya ta saka wani wandon jeans ta kama gashin kanta ta hade shi ta zubo da shi gadon bayan ta ta hade cikin turarukan ta in ka ganta sai ka zata yar babyn roba ce. Tayi kyau karshe. Sallah la'asar tayi tabdauki wayar ta dake kara Mommy ce nan tai mata ya jiki cikin jin kunya ta amsa da naji sauki ai. Suka dan taba hira sukai sallama. Mommy nacewa in da matsala ta fada mata.
Yaa Fauwaz kuwa yana can hankalin sa na kanta dan kawai yana son ya gama abinda yake ne kawai. Ya matsu a gama komai ya dawo ya ganta ya bata tukwucin abin da tayi masa da yadda ya same ta.
Karfe 05:30pm ya shigo gidan kan kujera ya fada yana fadin
"Washhh!!
Ido ya lumshe yana shakar kamshin turaren dakin me dadi da kamshi.Yasmeen dake daki tajiyo shigowar sa ta mike ta fito sallama tayi abinda yasa ya bude idon sa kenan suman zaune yayi ya zuba mata ido inda take tafiyar ta mai daukar hankali ta lumshe ido kamar me jin bacci. Har ta isa bai san ta karasa ba sai da yaji ta a jiki sa ya sauke wata ajiyar zuciya sannan ya rumgume ta tace
"Sannu da zuwa!"Ido ya bude ya yana fadin
"Babynah ina son ki sosai. Baby na kin tsaya min a rai Baby na duk inda nake kina tunani na na kasa sakewa nayi komai saboda tunanin ki. Kina lafiya ya jikin?"Ya fada yana taba jikin ta ba zafi ko kadan. Hannun ta ta sakalo ta wuyan sa ya kara janyo ta jikin sa yace
"Jikin ya warware?"Kai ta gyada masa, cikin jin kunya tai kasa dakai. Murmushi yayi yace
"Jiya kin kira min Mommy yau zaki kira min Alhaji Babba ko wa?"

YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasiLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.