*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_9⃣7⃣ - 9⃣8⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and Exhortate our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a addu'a Mommy na da Mommy nah)*
Washe gari aka yi yini a can Meena Event Center yan uwan ta sun nuna mata kara. Haka Mommyn ma tayi rawar gani. Mie Mie da Ummi ma haka abun yai kyau sai dai ba ango a duk bikin da akai daga amarya sai yan uwan ta haka aka tashi. Amarya tai kyau kamar a daule ta a gudu da ita.
Da dare akai dinner a theabsent, Kawayen amarya sunyi kwalliya cikin blue kalar matrial amarya kuma ta shirya cikin wani bakin material da akai wa zane da yellow ba karamin kyau tayi ba kamar ka sace ta ka gudu. Haka akai taron dinner dafa abokan su Yaa Ishaq sa na Yaa Faiwaz da yan uwan ta maza da Mata amman ba ango. Sai karfe daya aka tashi kowa yayi gida anci ansha anyi hotuna abin yai kyau.
Ana gobe daurin aure asabar Iyayen Maza suka hadu dan jin wanda zasu aurawa Yasmeen. Alhaji Babba yace a aura mata kanin Yaa Nazir, Salisu. Alhaji Karami kuma yace Yaa Ishaq. Amman Alhaji Babba yace ai Yaa Ishaq ya kawo zancen auren kawar Yasmeen. Baba da Abba na zaune suna ta tattaunawa.
Abba ne yai gyaran murya yace,
"Nasan nine karami, amman dan Allah ina son ku aurawa Yasmeen, Fauwaz."Alhaji Babba yace,
"A'ah ba za ai haka ba."Abba yace,
"Dalili na da yasa nace a aurawa Yasmeen Fauwaz shine saboda halin da Fauwaz yake ciki.
Kwanakin baya sam na daina ganin kira da sakon sa wannan yasa hankali na ya tashi dan nasan da dalili wannan yasa na nemo Marzuk shine ya fada min halin da Fauwaz yake ciki."Nan ya mika musu file din Fauwaz na asibiti yace
"Gashi nan komai da komai yana ciki na halin da yake ciki."Amsa Alhaji Babba yayi ya karanta sannan ya mikawa Baba shima ya karanta sai ya mikawa Alhaji Karami. Dukkan su shiru sukai.
Kai Baba ya jinjina yace
"Allahu Akbar kenan dai Yasmeen Rabon Fauwaz ce kenan. Tin a baya min so hada wannan zumuncin amman suka ce sam ba Soyayya tsakanin su to Yau gashi nan Allah ya kama shi ya nuna komai. Allah ya bawa fauwaz lafiya itama Yasmeen din Allah ya bata lafiya ya bata ikon masa biyayya. Dan haka ni na yanke goben za'a daura auren Fauwaz da Yasmeen!"Nan duk ya'yan suka amince da maganar mahaifin nasu suka saka albarka gaba dayan su.
Ranar Asabar aka daura aure Mayam Abdulkadir Ahmad da Ahmad Suleiman Ahmad.
Yasmeen ita tana can gidan Anty Binta bata san da wanda aka daura ba duk da ka ganta zaka san bata cikin nutsuwar ta. Tin safe ta tashi da wani zazzafan zazzabi da yasa ko tashi ta kasa yi da kyar ta iya yin wanka tana fitowa aka aiko mota tazo aka dauke ta dan za a kai ta gidan Baba.
Mommy kuwa jin an daura auren kuma taji ance da Fauwaz aka daura, sai da tai hamdala don daman tana masa sha'awar Yasmeen dan Yasmeen yarinya ce a nutse ga hankali da biyayya kowanne uba da uwa zai wa 'dan sa sha'awar samun Yasmeen a matsayin sirikar sa.

YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasíaLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.