121-122

943 56 1
                                        

*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_

1⃣2⃣1⃣ - 1⃣2⃣2⃣

Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*

Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com
Wattapad *Msindabawa*

🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and  Exhortate our readers)_*

Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_

*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a adidu'a Mommy na da Mommy nah)*





Yana isa wanka ya shiga zai yi sai ya tuna da Yasmeen wanda da a gida ne da tini ta hada masa ruwan wankan. Kai ya girgiza dan yasan zai sha wuya dan tin a jirgi ya fara missing nata.

Yana gamawa yai daura alwala ya fito yayi sallah ya shirya cikin gajeran wando da wata karamar farar singlite. Ledar da ta bashi ya bude ya ga abinda ya zubo masa a ciki.

Dambum naman da tayi masa yaci ya sha lemo kawai yaji cikin sa ya cika hamdala yayi sannan yace
"Allah miki albarka!"

Wayar sa ya janyo dan ya kira ta sai yaga sakon ta.
"Honey I love u soo much, I miss u darling, I really miss u Baby take care. Muaahh!"

Ido ya lumshe ya fara neman layin amman wayar taki shiga ajiyewa yana fadin
"Miss u more Baby nah!!

Nan ya kwanta dan ya huta. Amman kewar ta duk ta ishe shi har wani zazzabin missing nata take yi.

Can ya kara daukar wayar ya kira tana ringing ta dauka kamar me jira.
"Hello Yaya na ya gajiya bakai bacci ba?"

Ajiyar zuciya ya sauke yace
"Baby tayaya zan iya bacci ban jiki a jikina ba."

Murmushi tayi yace
"Hakuri zakayi Ai!"

"Uhmm uhmm wallahi I miss u alot!!"
"Miss u more Yaya nah!!

Sun jima suna waya dan har kusan asuba sannan sukai sallama ya koma ya kwanta ita kuwa alwala tayi tazo ta hau kan sallaya tayi sllah. Ba ita ta koma bacci ba saida tagama aikin gidan ta hada break sannan ta shige dakin ta takwanta.

Siyama da ta tashi Antyn ta tagama komai dan haka ci tayi ta kwanta tana kallo kawai

Sai karfe daya ta tashi tai wanka sannan ta fito ta shirya tayo falo dan ta karya.

Ranar sun sha waya da Yayan ta kamar me? Siyama ta sha mamaki daman haka suke tace ai halin da ya shiga a da ya isa ya tabbatar wa da kowa yana son ta. A ranar aka kawo musu mai aiki wani daki dake waje yana da toilet da kitchen da barander can aka sauke ta suke zaman su acan dan har kayan kallo aka zuba mata.

Da dare har ta kwanta sai ga kiran Yayan ta nan. Dauka tayi tace
"Hello yaya na!"

Ajiyar zuciya ya sauke da yaji muryar ta. Cikin shagwaba tace
"Yaya na ya daren?

"Dare sai tsawo ba kya kusa dani!"
"Uhmm nima baccin yaki zuwa sai juyi nake yi!"

Tsigar jikin sa yaji tatashi saboda yadda yaji muryar ta. Sai yaji ba abinda yake son ya gani ko yaji sai ita a tare da ita.

"Sorry dear daure kiyi bacci kinji, bana so ki sa damuwa a ranki. Da ina kusa dake danu yanzu na jijjiga ki na shafa bayan ki ina hura miki iska a kunnanki ina lallamin ki har kiyi bacci! Baby na rufe idonki zan zo miki yanzun nan a mafarki ki kinji? Zan zo na faranta miki ina son cooperation naki!"

Ni da Yaa FauwazWhere stories live. Discover now