*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_1⃣0⃣5⃣ - 1⃣1⃣6⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and Exhortate our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a adidu'a Mommy na da Mommy nah)*
Tana zaune a falo wajen karfe biyu sai ga sallamar Asiya nan matar Yaa Nazir nan Yasmeen ta tashi da murna ta taro ta tana fadi
"Ammn fa da nayi fushi."Dariya tayi tace
"Afuwa"Ta zauna sai ga sallamar Yaa Nazir nan ya shigo. Murmushi tayi tace
"Barka da zuwa Yayanah!"Zama yayi yana fadin
"Sannun ki "Nan ta mike ta hau kawo musu ruwa lemo abinci da snacks dukka. Sannanbta zauna dan bakin ta yaki rufuwa tace
"Ina yini Yaa Nazir?""Lafiya lou amarya. Ya gida ya Yayan namu?"
Murmushi tayi tace
"Lafiya!"Ta kalli Asiya tace
"Ya gidan?""Lafiya Alhamdulillah!"
Nan ta zuba musu lemon tace
"Please ku sauko kuci."Asiya ce ta sauka. Yaa Nazir ya kalle ta yace
"Zaki iya ci?"Kai ta gyada masa dan tana laulayi ne ba komai take iya ci ba. Ai kam nan ya sauka ya dinga bata da kansa. Kuma taci da yawa. Yasmeen na kallon su sun matukar burge ta. Sai da suka gama sannan yai musu sallama kan zai dawo ya dauke ta.
Nan Yasmeen ta kwashe kayan ta wanko sannan suka dawo hira. Asiya tace
"Amarya kinyi kyau sai dai duk kin rame kar kice min har yanzu baki saba ba!""Da mene ban saba ba?"
"Abin mana."Hararar ta Yasmeen tayi tace
"Kin shiga uku sai kawai nayi ta rama dan bansaba ba?""Eh mana. Baki san kan abun ya amshi mutun haka wani yake ba."
Shiru Yasmeen tayi tace
"Alah ya kyauta. Kema naga ai kamar ciki gare ki!"Shafa cikin ta tayi tace
"Wallahi har wata biyar fa!"Murmushi Yasmeen tayi tace
"Ah mun kusa shan suna kenan. Allah ya inganta!""Amin!"
Ido yasmeen ta zaro yace
"Sirikar kice fa ni!""A inda ba sirikar ba. Ke ni ko Mommy bana sirika da ita bare ke."
"Allah ya shirya ki to!""Ameen!"
"Kinji an saka ranar bikin Yaa Ishaq ko nan wata uku fa!"Ido Yasmeen tayo waje dasu tace
"Dan Allah amman shine Aisha bata fadan ba. Lallai Aisha!"Ta dauki wayar ta ta fara neman layin ta kira daya biyu ta dauka tana fadin
"Besty na ya amarci.""Ba wani besty ashe an saka ranar auren ku ko ki fada min haba sis!"
"Am so sorry sister walalhi na zata an fada miki.""An fada min kuma ba zan miki maganar ba. Jiya ma fa munyi waya ko?"
"Ni dai naji nai laifi ai min hakuri!"

YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
خيال (فانتازيا)Labari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.