*NI DA YAA FAUWAZ*💕💕💕💕
_(Love story)_1⃣1⃣1⃣ - 1⃣1⃣2⃣
Na
*MARYAM S INDABAWA (ANTTY)*
*MANS*Facebook group:- *Indabawa novel group/ Hakuri da juriya hausa Novel Group*
Email:- -Maryamsuleiman220@gmail.com
Wattapad *Msindabawa*🌐🌐🌐🌐🌐🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITER'S* ✍🏻✍🏻✍🏻
*(HAJOW)*
*Gidan Amanci da albarka*
*_(We Educate, Entertain Enlighte and Exhortate our readers)_*Dedicated to
*Nafisa Suleiman (Mommy nah)*
_Allah kara girma da daukaka ya raya zuri'a AMEEN_*Mommy na ina godiya da soyayyar ki da kulawar ki gareni. Allah ya bar kauna. Allah ya kiyaye min ke, ya Raya Auta Al amin. Ya Albarkaci zuri'a. Ameen. Mommy nah Allah saka miku da alheri ya bar mana ke ya raya miki Autah Yasmeen Ameen. (Kusa min iyaye na a adidu'a Mommy na da Mommy nah)*
Jikin ta ya fara rawa, tsayawa yayi da abinda yake sannan ya dorata akan kirjin sa, ya sabule rigar jikin ta, kan sa ya tusa tsakiyar kirjin ta. Duk abinda yake jikin ta sai rawa yake kamar mazari. Dan tsoro ya gama cika ta. Nan ya hau aika mata da sakonni masu wuyar fassarawa duk yadda take kukan shi bai jin ta ji yake kamar tana kara ingiza shine.
Ta sha kuka kamar me dan muryar ta ma har dishashewa tayi.Bazan ta iya fassalta a wane hali Yaa Fauwaz ya tsinci kansa ba don be san a wacce duniya yake ba, dan ji yai kamar bai taba sanin wata 'ya mace ba sai akan Yasmeen sam ya manta da Yasmeen sabon hannu ce, A rana fadi yake wannan yarinyar yar albarka ce, me cikakkiyar ni'ima lallai su hajiyar sa sun so masa gata tun farko yaki amman yanzu ba zai sake kin bin umarnin su ko shawarar su, ranar ya sawa Yasmeen albarka ba adadai haka iyayen sa ma yana godewa Allah kullun da Abba da iyayen sa har da kakanin sa da Abbas ma da ya fasa auren ta. Shin wai da tini wani ne ya lwashi wannan zumar Yasmeen din bashi ba lallai da ya tafka babbar asara.
Ashe haka rayuwar aure take, ashe haka Allah yake wadata wasu matan da ni'ima, lallai Yasmeen ta ciri tuta tafi sauran matan da ya gane abin ba a girma ko waye wa bace daga Allah ne, lallai ba wanda ya isa ya raba shi da Yasmeen ba, in ba mutuwa ba.
Yasha shagwabar Yasmeen wacce ta kara masa tsantsar son ta da begen ta. Da kyar bacci ya dauke ta, a hankali ya zame jikin sa ya tashi zaune ya jima yana zaune yana kallon ta, wani sonta na dada narka masa zuciya yana mai mata addu'a da sa mata albarka. Sannan ya mike ya shiga ban daki yai wanka ya dauro alwala yazo ya tada sallah. Yayi nifila tafi raka'a goma ta godiya ga Allah sannan ya zauna yana kirari ga Allah tare da gode masa yai addu'ar Allah ya bar masa Yasmeen har a aljanna ya kuma bashi ikon adalci a tsakanin matan shi ya saka wa Yasmeen son sa da kaunar sa duk da yasan akwai ta yan uwan taka. Sai da ya gama ya koma gadon yaja ta jikin sa. Ta sauke ajiyar zuciya. Jikin ta har ya fara zafi. A haka bacci ya dauke shi.
Da asuba ya tashi ya kara watsa ruwan yai alwala, yaje yai sallah ya dawo. ya zauna ya zuba mata ido tana ta sharar baccin wahala yau sam ta kasa tashi dan ya gajiyar da ita ita da take tashi tin kan a kira sallah. Kallon ta yake son ta da kaunar ta yana kada ruruwa a ransa. Fuskar ta ya shafa ta dan bude ido.
Murmushi ya sakar mata yace
"Baby na tashi kiyi wanka kiyi sallah gari ya waye!""Yayahhh!"
Ta kira sunan shi a shagwabe kamar zatai kuka.Janyo ta yayi yace
"Yi hakuri Babyn Yayanta!"Ya dauke ta suka nufi toilet, yayi mata wanka da wankan tsarki da alwala. Ya dawo da ita daki, ya shimfida mata abin sallah, Sallah tayi tana idarwa ta nannade ta kwanta akan abun sallah. Ya dago ta ya rumgume ta a jikin sa,
"nagode miki Yasmeen Allah yayi miki albarka, Allah ya bamu zuri'a ta gari."
YOU ARE READING
Ni da Yaa Fauwaz
FantasyLabari ne akan wani saurayi da kanwarsa wacce take cousin dinsa ce.