Page 5

181 8 0
                                    

*PHTEENJIDDAH*

*MALLAKAR*
*_Ƴar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
 
   *Please Subscribe My Channel*

https://www.youtube.com/channel/UCWyfuDW1EWCBqzOrwaCnq3Q
  Domin kawu muku Audion littattafan Hausa

                             5

Tun daga lokacin su phaty basu 'kara fita ko ina ba, kullum suna cikin gida basuson fita.

Phaty tana kwance tayi rubda ciki tana tunanin abunda ya daruu da ita adaran randa sukaje party, cikin zuciyanta ta fara tambaya wanene wannan, me naimai haka?, wlh ALLAH ya isa bazan yafe masa ba.. mtseew tsa'ki tayi ta kamo wani tunanin daban, domin kuwa ranta ya fara 'baci.
Tana cikin wannan tunaninne wayanta ya fara ruri, janyo wayar ta dauka batare dataga mai kiran ba, ihuu taji cikin kunnanta, cire wayan tayi daga kunnanta ta duba numbern sai taga numbern Amin's, Phaty tace,

"Beb yadai wannan ihu haka?"

"Ke kwana biyu ina kiran numbernki not reachable yadai"?

"Phaty tace wlh komi normal ne, ya da wannan kira haka?"

"Kinsan kuwa na kusanyi birthday?"

"Oh my God wlh na manta shaf, yaushene haka?"

"Ranar saturday ne wlh kuma i think ba anan zamu had'a partyn ba"

"A haba beb to a ina za ahad'a mana wannan partyn na big girl?"

"Wlh a abuja ne ba wani gari mai nisa bane"

Phaty shiru tayi tana tunanin anya zata iya attending din wannan partyn kuwa coz, garin yayi mata nisa sosai, inma tace zata tayaya ma Mom dinta zata yadda taje ta kwana a wani wurun, wannan ma bamai yuwuwa bane.

"Amins tace yadai Beb najiki shurune"?

Ajiyar zuciya Phaty tayi tace "Beb bana tunanin zanze partynnan coz akwai damuwa"

"Damuwa kuma?, wani irin damuwane zai hanaki zuwa birthday dina?, kinsan fa kece best friend dina, abun kunyane ace baki a wurun birthday dinnan, plz kiyi wani abu akai mana, please besty".

"Phaty tace okey, okey zan duba lamarin nagani maybe nazo maybe kuma bazan zoba, kinsan yadda Mom take sa mana ido alamuranmu, ke kanki kinsani Mom batason mu'amalata dake wai bata yadda dake ba, kawai ki barmin lamarin zansan yadda za ayi"

"Yawwa 'yar gari zan bada passport dinki coz kinsan da flight zaku taho keda wannan broda na kinsan har yanzu bai ha'kura dake ba"?

Murmushi Phaty tayi tace ALLAH sarki sweetheart kice har yanzu yana nan?, kice mai nayi fushi tunda baya nemana."

"Beb karkice ban fada maki yayu rashin lafiya ba?"

"Wlh baki fadamin ba, amma kin fadamin yanzu dayake takice takawoki, ba damuwa beb sai munyi waya tukun duk yadda na tsara na fada maki"

"Owk ba damuwa sai najiki take care"

"Aha thank you"
Phaty ta kashe wayan ta gyara kwanciyarta ta cigaba da tunani

_INA LABARIN UMAR_????

Sir na d'auka kace yau zamu tafi tunda angama abunda ya kawomu, umar yana zaune ya d'aura 'kafa daya kan daya, hannunsa ru'ke da coffee, shiru yayi na d'an wani lokaci cikin 'kasaita da nuna isa yace,

"Kagaji da aikin kenan?"
"Cikin sauri ya girgiza kai Oga ba haka nake nufi ba kawai naga kaine ka 'kosa mu gama wannan mission din shiyasa nai maka magana kar ranka ya 'baci"

"Umar yace, to ba yanzu zamu tafi ba kai infact banma san ranar tafiyarmu ba"

"Oga cewa kayi fa bakasan ranar tafiyarmu ba, alhalin sai azalzala mana kakeyi muyi mu gama wannan mission din"

"Umar lumshe idanuwansa yayi yace, Jafar!, kayi abunda nace maka kawai pleasee i need space"

"Owk sir insha ALLAHU, amma ya maganar zuwanmu abujan kasan urgent call akaimin ana bu'katar ganinka"

"Baana tunanin zanje abujannan jafar maybe kaine zakaje ka wakilceni please karka dameni da surutu, kaje kawai saina nemeka."
Yayi mashi nuni da hannunsa donya tafi.
Jafar tafiya yayi amma yana tunanin abunda ya samu ogansa domin kuwa shine shaidansa na rashin son zama a garin kaduna, amma abun mamaki cewa yakee baisan ranar tafiyarsa ba, ALLAH yasa koma menene yazoma oganmu da sauki domin kuwa oganmu mutumin kirkine, ALLAH kasa komenene ya samu ba tare daya wahala ba, haka jafar ya tafi yanata maganar zuci...

_Phaty na hango durkushe agaban Mom dinsu nace bari inji wani shirgegen 'karya zata kuma_

Mom dan ALLAH ki barni inje anty fa'iza bazataji dad'i ba tunda harta kiraki tanemi alfarma kinsan idan kika hanani bazataji dadi ba kuma kinga Dad yaji labari shima bazaiji dadi ba zaiga kamar baki dau kanwarsa kamar kanwarki bane, dukda dau Dad yana da kawaici pleasee Mom," suna cikin maganarne Jidda ta shigo dakin daga ita sai shimi da gajeran wando, Mom na ganinta ta hade rai tana kallonta, tace, "Twins yaushe aka fara wannan shigar agidannan bansanu ba?" Jidda zama tayu kusa da ita tace, "Mom wlh zafi nakeji shiyasa na saka amma kema kinsan wannan ba irin shiganmu bane, abunda yasa nasama naga babu wanda yake shigo mana gida ba tare da izini ba shiyasama na saka, kuma Sis ta gudu tabarni kunzo kunata hira"

Phaty kallonta tayi tace, "dalla malama kimana shiru muna maganar hankali kinzo sai zuba kike kamar parrot"

Baki Jidda ta turo, tace, "wai dan ALLAH Mom nida sis waya girma wanine?, nidai nasan ko minti goma bata bani ba wlh" ta 'karashe maganar kamar zatayi kuka.
Mom tace, "to akoke saiki zauna kina mata kuka, dayake abun kuka baya maku wahala, ke kuma ki tashi ki shirya gobe ki tafi cand'in kuma sati daya kawai nace kiyi mata karki 'kara karki rage wlh", ke kuma, ta nuna jddah "kije ki cire wannan kayan nan kafin ranki ya 6aci acikin gidannan, ku wuce kubani wuri".

Jidda nasanjin farkon zance amma ba dama, fitowa sukayi sunata fama gwara kawuna, Phaty tace, "Wlh Sis bansan maiyasa Mom bata sakar mana fuska muyi hira da ita yadda yaka mata, sannan mu run'ka fad'a mata damuwarmu, bansan dalili ba".
Ta6e baki Jidda tayi, tace, "kanki akeji sai yanzu kikasan da haka?, ke bara fa na fad'a maki wlh Mom tafi damuwa akan business dinta sama damu, idan munyi mata complain bakyaji tana cewa danwa take business din in ba danmu ba, ni wlh tun ina damuwa harma na daina damuwa akan wannan lamarin, Sis wai ina zakine?.

Murmushi phaty tayi, tace, "abuja wlh aunty fa'iza ce ke nema na, kinsan cikinta ya girma so maybe aiki zan tayata".

Jidda tace "zaki tayata, ko zamu tayata?, kema kinsan batsa kikai wlh nufinki ki tafi ki barni a gidannan?, never wlh, dawama zan run'ka hira please Sis karkije, nasan Mom bazata barni na biki ba, please karki tafi gidan bazaimin dadi ba wlh, kinsan Mom bata yadda muyi hira da ita mai tsayi"

Phaty murmushi tayi, don a yadda Mom ta barta dakyar dinnan,  bata tunanin zata fasa zuwa, cikin zuciyanta tace wlh kida amin's ta fasayin birthday dinnan mai hanani zuwa abuja sai ALLAH. Dafa kafad'an Jiddah tayi tace, "Sis karki damu insha ALLAHU  bazanma kai sati d'aya ba, karki damu kinji, akwai waya ma run'ka waya koda yaushe, kuma always zamu run'ka chat kinji, fadamin innaje mai zan siyo maki?"

Ajiyar zuciya Jiddah tayi, tace, "Ba damuwa ALLAH ya kaiki lafiya ya dawo dake lafiya, amma dan ALLAH sis banda zuwa party, kinga abunda yaso yasamemu kwanaki"

Phaty Jijijjaga Jiddah tayi tace, "Sis uwar tsoro karki damu, inma banda abunki wana sani a abuja da zanje wani party?, abunda ya kaini kawai zanyi in dawo gida, kinji Sis"

Murmushi Jidda tayi tace, "hmmm Sis sai kace bansanki ba saidai bakiji casu ba, saidai nace ALLAH yasa abunda kikace ya zama gaskiya"

Murmushi phaty tayi, ta janyo wayanta ta turama aunty Fa'iza sa'ko kamar haka _"Aunty fa'iza bansan dame zan gode maki ba, Mom ta barni nagode sosai, gobe insha ALLAHU inanan tafe thanks alot auntyna_

Nan ma ta turama amin's text itama kamar haka _Beb komai normal fa, gobe insha ALLAHU ina abuja, sai mun hadu a waya ni zanyi gaba, na ha'kura daa flight din nahau mota kar asirina ya tonu_

Jiddah sai zuba takema phaty, amma ta lura hankalinta nakan waya, d'agowa tayi tace, "Sis lafiya naga kinata fama danna waya?"
Ad'an firgice ta d'ago ta ije wayan, tana murmushin ya'ke, tace, "bakomai Sis abuna duba"
jinta kawai Jidda tayi badan ta yarda ba azuciyarta tace _"intayi wari taji"_
Haka suka raba dare suna hira, kamar bazasu 'kara had'uwa ba.

PHATEENJIDDAHWhere stories live. Discover now