Zumbur Phaty ta tashi tsaye, har tana k'warewa, tari kawai takeyi, tari sosai, dak'yar ta iya tsugunnawa ta d'auko ruwa ta kwankwad'a, still tarin bai tsaya ba, zuwa gurin k'ofa tayi da niyyar fita ta jita gam, sosai ran Phaty ya 6aci komawa bayan kujera tayi ta fara kuka, saboda a ganinta Umar bai kamata ya ganta da k'ananan kaya haka ba, ranta ya 6aci matuk'a, harta rasa abunda zataima Jiddah insun had'u, _"Jidda ta rainani"_ ta fad'a acikin zuciyarta, sosai ta takure a bayan kujera, abun takaici bata fito da wayanta ba, aida yau babu mai hanata kiran Momy wlh.
Umar kuwa tunda suka had'a ido da Phaty ya kawar da kansa, ya shimfid'a dadduma ya tada sallah, cikin tsanake yake sallahrsa, har saida ya idar, yayi addu'o'insa.
Phaty kuwa tana bayan kujera sai rera kukanta take, tunanin irin rashin mutuncin da zataima Jiddah kawai take.
Umar kuwa nannad'e daddumar yayi, ya maida ita mazauninta, mik'ewa yayi ya taka har inda Phaty take, tananan tana ta rafka kuka, sosai take kukanta kamar ance an kashe mata iyayenta, gyaran murya Umar yayi, cikin sanyin murya yace, "Haba Phaty kukan ya isa haka mana, bakya gudun kanki yayi ciwo ko zazza6i ya kamaki?, please ki daina kukannan ya isa haka, kinsan banason kukanki ko kad'an, dan ALLAH kiyi hak'uri ki shiru, magana kawai zamuyi dake shikenan saiki tafi abunki, but please karkiga laifin Jiddah kuma karki mata hukuncin da baidace da ita ba, batasan komai ba, nine dai na nema alfarmar ganinki, kuma taimin alk'awarin haka, kiyi hak'uri kinji."Tunda Umar ya fara maganarsa Phaty ko d'aga kai batai ba balle ta kallesa, itadai sai shashshek'ar kuka take tamkar wata k'aramar yarinya, magana Umar yake mata amma kamar bada ita yake ba, shirune ya biyo baya na d'an wasu lokaci, Umar ya lura Phaty ko zata shekara a wurinnan tofa bazata tanka mai ba, kallanta yakeyi kawai, ita kuma ta saka kanta a cikin cinyoyinta, amma tai shiru, Sosai taima Umar kyau ba d'an kad'an ba, cikin wata siririyar murya ya kira sunanta yace, "Fatima".
Phaty kuwa kamar an fizge idanunta batasan lokacin data d'aga kanta ba, suna had'a ido tai saurin maida kanta, dan gani take bazata iya jurar ganinsa ba, yayi mata kwarjini a ido ga kuma wani kyau da yayi mata.
A hankali ya d'an matsa kusa da ita, cikin muryarta wacca tasha kuka harta gaji tace "Dan ALLAH karka matso kusa dani, please."
Murmushi yayi wanda ya k'ara fito da ainihin kyawunsa, yace mata "Naji, amma mai yasa ina tai maki magana amma kinyi shiru kin k'yaleni?"
Phaty tace "A haka kakeso nai maka maganar, kaban wayarka na kira Jidda nai mata magana ta kawomin hijab."
Umar dariya yayi, yace "Ank'i wayan ni zakima wayo ko?, wato na baki wayan, ki kira Momy, ai tun d'azu na ankara da hakan, karki damu, kinsan nine mijinki na gobe, so banga abunda zaki 6oyemin kuma ba, kawai ki tsaya muyi magana dake ta fahimta saiki tafi abunki"
Phaty d'ago kanta tai ta maka mishi harara sannan ta maida, tace "ka fad'a abunda zaka fad'amin, bance kaimin dogon zance ba, kai sauri ka fad'a abunda zaka fad'amin, don kuwa inada abunyi"
Kallanta Umar kawai yake, saboda yadda takemai tsiwa kamar wani sa'anta, ajiyar zuciya ya saki, ya kamo hannunwanta yace "Dan ALLAH phaty ki dainamin haka, banajin dad'i kokad'an wlh, kodan na fad'a maki abunda ke cikin zuciya tane shiyasa kikemin abunda ranki keso?, hannunta yasa akan k'irjinsa da sauri da zare, dan kuwa ba k'aramin tsorata tayi ba, sosai zuciyarsa ke bugu da sauri da sauri, a hankali yayi mata magana, yace "Nasan kinji yadda zuciyata ke bugu, to ki sani sankine a cikinsa, aduk lokacin da kika nuna bak'ya k'aunata, takanyi fiye da haka, dan ALLAH Phaty kiyi hak'uri da abunda ya faru a tsakanina dake, ki manta komai, kizo muyi sabuwar rayuwa, ina miki san da banama kaina, kiyi hak'uri da abunda nake maki, sanki ke sakani haka, na kasance namiji mai controlling d'in kansa, amma bansa maiyasa idan ina tare dakeba bana iyawa yadda ya kamata, kiyi hak'uri da abubuwan danake maki,ba zan maki alk'awari na dainaba amma insha ALLAHU zanyi k'ok'arin daina wasu, please Fatima."
Sosai muryar Umar ta fara sark'ewa, don kuwa shi kad'ai yasan abunda yakeji a cikin zuciyarsa, shirun da Phaty tajine yasata d'agowa, da sauri ta maida kanta, dan kuwa ita yake kallo, sosai ta razana da kallon da yake mata, _"Idanunsa sun sauya kala"_ ta fad'a a cikin zuciyarta, Sosai yaba Phaty tasauyi, a cikin zuciyarta fad'i take _"ALLAH kenan babu ruwansa, kalli wannan guy d'in, ninasan yafini komai naisa ba kusa ba, amma ALLAH ya jarabceshi da soyayyata, ya fini kud'i, ya fini kyau, ya fini ilimi, amma kalli yadda ya zauna agabana yana neman soyayyata, anya kuwa idan nace zanja mishi aji ajin bazai tsinkeba kuwa?, yaka mata na kar6i soyayyarsa tun kafin lokaci ya k'uremin, ALLAH ya kawomin mai k'aunata tsakaninshi da ALLAH zanyi sake da damata, baya 6oyemin gaskiyar abunda ke ransa, dukda nasan nima zuciyata ta kamu da sonshi tun ba yauba, amma yazama dole na 6oye nawa son."_
"Kinyi shiru kin k'yaleni, Phaty", cewar Umar.
'Dago fuskanta tayi ta kallesa, ba yabo ba fallasa tace "Naji, amma sai nayi shawara, duk yadda na yanke zakaji komai"
Murmushi ya sakin mata yace "Nak'i wayan, ba inda zani saikin fad'amin matsayina a zuciyarki, abundama saboda rashin matsayina har a blacklist aka sakani"
Had'e rai Phaty tayi tace "Kai yanzu na baka ansa zaka yadda da abunda nace?, ka bari naje nai shawara da zuciyata da Sister d'ina sai kuma Mom and Dad d'ina, duk yadda na yanke zan fad'a maka nan da rana itayau, alk'awari d'aya zan maka duk abunda na yanke bazan 6oye maka ba, kuma idan na koma d'aki zan cireka a blacklist d'in, ina fatan hakan yayi maka ai"
Kallanta kawai yake, a cikin zuciyarsa fad'i yake _"yarinyarnan ta tafi da zuciyata da yawa wlh, ina matuk'ar k'aunarta, ALLAH ka nunamin ranar da zan mallaketa, ameen"_
Kallansa Phaty tayi tace, "Wannan kallanfa?, kallan yayimin yawa, sai kace yau ka fara ganina"
Murmushi yayi yace "Ah mana yau na fara ganinki mana, tunda kin gama gwaramin kai, kin sani ciwon kai da yawa"
Murmushi tayi, nan fa hira ta 6arke tsakaninta da Umar sosai suke nunawa junansu kulawa, barinma Umar wani irin k'aunartace ke kwarara a cikin zuciyarsa, sam Phaty tama manta da irin dad'ewar da sukai suna hira, can ta kalli Umar tace, "Friend yaka mata kazo ka wuce, bana tunaninma kaje gida, kuma naga lokaci yaja"
Kallanta Umar yayi yace, "Ba wani korata kike, nina sani, kuma wannan suna yaza dole acanzamin dan bana sonsa"
Dariya Phaty kawai tayi, shi kuma ya mik'e yace "bari na tafi gimbiyata, amma ki shiryamin delicious dan da daddare zan dawo na k'ara ganin hasken idaniyata"
Murmushin jin dad'i Phaty tayi, tace "amma gaskiya yaka mata ace kaje gida ka huta, coz nasan kagaji"
Umar yace "Baki da damuwa, amma ki sani da daddare ina nan zuwa"
Mik'ewa Phaty itama tayi tace, "To shikenan ALLAH ya kawoka lafiya"
Hugging d'inta Umar yayi very tied _"ya salam"_ kawai Phaty tace a cikin zuciyarta, rad'a yayi mata a cikin kunnanta yace "I love you"
"Uhmm" kawai Phaty tace, tana k'ok'arin zame jikinta, sakinta yayi a hankali, ita kuma ta maka masa harara tace "Yaushe zamu daina 'yar haka dakaine?, na fad'a maka banaso amma kak'iji wlh"Dariya ta bashi yace, "amma aina fad'a maki ba laifina bane, laifin sonkine da yayimin yawa a cikin zuciyata, amma ai nace zan daina, sai a hankali ai zan daina d'in"
kallansa tayi tace "yaka mata ka tafi kaga ko sallah azahar banyi ba, gwara kai kayi, ga la'asar nan ta gabato"
Umar yace "Shikenan, ki kulamin da kanki, ki gaida momyna da kuma dad d'inmu, kima k'anwata godiya, kice anjima zamu had'u"
"Uhmm" kawai Phaty tace, Umar kuma ya fita, jinsa yake kamar wani sabon ango, "Komai ya kusan zamamin daidai insha ALLAHU", ya fad'a a zahiri, fita yayi da sauri daga gidan, ya shiga motarsa ya tada ita.
Phaty kuwa kulle d'akin tayi ta fito, sai zabga murmushi kawai take, d'akinsu ta shiga ta hango Jidda akwance kamar mai bacci, alhalin ba baccin take ba, Phaty tace mata "to gulmammiya ai sai ki tashi nasan ba bacci kike ba"_Niko nace to ina rashin mutunci da kikace zaki mata, nima fa da harnace zan tayaki, ya kuma zakice mata haka?, kina nufin taci bulus kenan?_
Wani kallo taimin tace, "Kai mum irfaan naga alama bakya farin ciki da wannan soyayyar tamu, amma nasan fans d'in Phateenjiddah zasuso hakan, ki sani ba abunda zan mata don kuwa ta gyara soyayyane. Ke Sis tashi muyi sirri ma"
Jiki ba k'wari na fito, danda harda bulalata na taho da ita zamu jibga JiddahUmar kuwa a wani makeken gida naga yayi parking, gidan ya tsaru, ya had'u iya had'uwa, yana fitowa daga motarsa naga ya turnuk'e rai, kamar ba Umar d'in da yagama shan soyayya ba, fan's zan iya ce muku tunda nake ban ta6a ganin Umar a irin wannan yanayin ba, sai kace an mishi bushara da gidan wuta.
_aiba shiri na koma baya ina tunanin anya wannan rahoton zaiyuwu na kawo maku shi kuwa?, karfa Umar ya maujeni nida d'an littafina da biro, ba shiri na tarkato na dawo gida, dan na nemi irin kayan da gwaska ya saka saboda tsaro badan tsoro ba_
YOU ARE READING
PHATEENJIDDAH
ActionYana maganane akan yara guda biyu Wanda suka kasance tagwaye, gashi Allah yayi musu rashin basajin magana ko kadan, sannan kuma ina gargadin iyaye da su runka jan 'yayansu a jiki basu wancakalar dasu ba akan wani dalili nasu na daban,👭