Jidda ta kasa zaune ta kasa tsaye, tana ta kiran numbern Phaty amma no answer, sosai hankalin Jidda ya fara tashi, saboda batasan halin da 'yar uwarta take ciki ba, sosai hankalinta yayi mummunar tashi, ta kira wayan a kalla yafi so hamsin amma no answer, Jiddah ta rasa yadda zatayi kawai ta fara karanta addu'o'i duk wanda yazo bakinta akan ALLAH ya kare mata 'yar uwarta aduk halin datake ciki.
Sai wuraren k'arfe biyar Phaty ta tashi, zumbur ta tashi tana mutsitstsike idanuwanta, gyalanta ta hango agefe guda, da sauri ta d'auka, ta tashi ta gyagygyara jikinta, jakarta ta d'auka cikin sauri-sauri, harta fito daga cikin bedroom d'in sai kuma ta koma, taga Umar yana baccinsa cikin kwanciyar hankali, harda wani murmushi akan fuskarsa, murmushin itama tayi, tayi saurin fita taga d'akin, d'akin ta murd'a ta fita, tana cikin tafiyane taji an shak'o mata wuya, Dija tace "Sannu karuwa maibin namiji har cikin d'akinsa, saboda babu aji, in banda rashin class irin naki, ya za'ai ki biyo har namiji cikin d'aki, wannan wani irin rashin kamun kaine?"
Phatee k'ok'arin k'wace kanta kawai take, juyowa tayi suka had'a ido biyu da Dija, Dija cikin mamaki da al'ajabi tace ma Phaty "PhatynJidda, ryt"
Kallan k'ask'anci Phaty taima Dija tace "Yes, kinsan da haka kuma kike tambayana, madam ki sakeni kafin na nad'a maki na jaki acikin gidanku, inga uban da zai rama maki, kuma kina f'adin karuwanci, baki da labarin yanzu karuwanci ke ci a yanzu ba, ai karuwancinma waje ake samu da har akeyinsa, kuma na rantse da ALLAH kika k'ara fad'amin kalma wacca tai dangantaka data 6atanci zan miki shegen duka wlh inga uban daya tsaya maki, nasan kin sanni dukda dai nidai banma ta6a ganinki ba sai yau, but yaka mata ki tsabtace harshenki"
Tuni Phaty ta fincike hannun Dija tayi gaba, har Dija tana k'ok'arin fad'uwa, k'wafa tayi tace "Lallai Umar yayi nisa yama rasa wacca zaiyi tarayya da ita sai Phaty wannan k'asurgumar 'yar duniya, lallai Umar dama haka yake, wlh da sake, bazai yuwu ni nabi maza ba shi yabi mata ba, ai abun sai yayi yawa gwara nid'in dai nabi"
Tafiya kawai take tanata 'yar zage-zage, Hajiya aina'u tace "Ke lafiya naga kin taho kamar wata zararra?, ya kuma na ganki haka keda mukai zakimin flashing nazo? ba magana nake miki ba"
Dija cikin in-ina tace mata "Dama nazo na fad'a maki ne, maganin na d'auka yana da kyau kamar yadda muke tunani, to dana koma naga ba wani canji, ni kuma nace bari na farayimai koda wasannine, banma k'arasa zuwa wurinsa ba ya dakamin tsawa ya koreni a d'akin, harda cewa idan ya kamani saiya nad'amin duka" Dija ta karashe maganar kamar zatai kuka, wani ashar da Hajiya ta doka ni kaina saidana razana, cikin hargagi da masifa tace "Ina wlh bazai yuwu ba, komai baya yi maka, kaiii ina k'aryane, dolene na koma nai sabon shiri banga ta zama ba, nidashi ne wlh, saiyasan niya ta6o wlh, sai na nuna mashi nice hajiya aina'u acikin gidannan"
Dija tunda taji haka tace "Hajiya dan ALLAH komai zakiyi kada ki cutar dashi"
Hajita waigowa tayi a fusace tace "Dallah matsa ki bani wuri mara zuciya, in banda rashin zuciya, mutum kusan kullum a wulak'ance yake d'aukarki amma ke kin nace saishi, wlh danice ke tuni nabar banza na ajeshi a hofi" Hawa upstair hajiya tayi tanata zabga ruwan bala'i, da tijara a cikin gidan, fad'i take "wlh baka isa ka d'auramin ciwon zuciya ba, yazemin dole kabar duniya, in kuma ka kawomin taurin kai a lamarin, ka zama abun tausayi a duniya, ita kuma yarinyar da kake nema dole saina bincikota,da farko dole nai mata warnning in kuma tak'i ji, zata janyoma kanta bala'in da bazata iya dashi ba har abada, nice fa, nice hajiya aina'u naci dubu sai ceto, koni tsoron kaina nake balle kuma wasu" dariyar k'eta kawai tayi ta shiga cikin bedroom d'inta.
K'arar bud'e get Jidda taji, zumbur ta tashi ta lek'a ta window, Phaty ta gani ta dawo, cikin sauri da sassarfa Jidda ta fito dan isa gurin Phaty, Phaty tana kulle motar taga Jidda akanta, murmushi tayi mata tace "Sis wannan kallan fa, ai kya bari mu shiga dak'i na baki latest labari ko"
YOU ARE READING
PHATEENJIDDAH
ActionYana maganane akan yara guda biyu Wanda suka kasance tagwaye, gashi Allah yayi musu rashin basajin magana ko kadan, sannan kuma ina gargadin iyaye da su runka jan 'yayansu a jiki basu wancakalar dasu ba akan wani dalili nasu na daban,👭