page 43

94 8 0
                                    

_Wannan page din nakune ku kadai masoyan littafina, bazan boye muku ba ina matukar jin dadin comment dinku, naga yadda kuke rugurguzamin ruwan comment hakan nasani jin dadi da karfin gwiwar cigaba da bankado muku posting, wato shiyasa na daddage na 'ku'ke nace wannan page din nakune ku kadai kuyi yadda kukeso dashi kuba wanda zaku ba ku hana wanda bazaku bawawa shiba, nidai na mallaka mukushi halak malak_



Alhajin Umar baiyi kasa a gwiwa ba ya sanarwa da Umar halin da ake ciki, idan hankali Umar dubune to duka ya tashi dan a tunaninsa abun baikai haka ba sai gashi yana neman kure tunaninsa, daurewa yayi bai nunawa Phaty halin da ake ciki ba, amma zuciyarsa ta karaya badan kadan ba, yana zaune kusa da Phaty lokacin da mahaifinsa yasanar dashi abunda ke faruwa, yake yayi mata wanda baikai zuci ba saboda kallan data kafeshi dashi, cikin sanyi murya tace "Kamar ba lafiya ba?, coz naga tunda ka ansa wayannan yanayinka ya canza, ALLAH yasa lafiya"

Murmushi Umar ya kasheta dashi yace "Yace babu komai, kawai Dijace batada lafiya akace dole ni takeso na kaita, shiyasa kikaga yanayina ya canza"

Phaty tuni ta murtuke fuska tace "Nifa wlh banaso inga kana mu'amala da Dijannan dukda dai yar uwarkace amma agaskiya bana sonta harga ALLAH"

Umar ruko hannunta yayi yace "Karki damu, kisa aranki ni Umar Faruk nakine ke kadai babu wata"

Hararar wasa tai masa tace "Ni banason dadin bakinnan, da zarar mace ta shiga daka ciki sai ku runka kokarin kara wani auran"

Maganar taba Umar dariya, darawa yayi kadan ya matse mata hannun ta saki wata yar kara "Wash, hannuna"

Kallanta yayi da sexy eyes dinsa yace "Ki daina tunanin ni Umar zan hadaki da wata, nidai a raya'ayina bana bukatar ko wacce mace face ke, saidai bansan ta yadda ALLAH zata kasance ba, amma ni nafisan mace daya inhar zaki jura abubuwan danake bukata kuma nakeso shikenan keda kishiya kuma saidai ki runka jiyota a makota"

Dariyar jin dadi Phaty tayi tare da rufe fuskarta murmushi kwance a fuskarta tace "Insha ALLAHU"

Duba agogon wayarsa yayi yace "Bari naje na dawo, naga Alhaji sai kirana yake bazan dade ba zan dawo"

Kallansa tayi tai narai-narai da idanu muryarta na rawa tace "Bafa ka dade da zuwa ba, amma ace har zaka tafi"

Kafeta yayi da manyan idanunsa saita sadda kanta kasa saboda bazata iya jurar kallan daya yake mata ba, goge hawayan idanunta tayi tace "Shikenan, saika dawo amma please karka dade"

Dawowa yayi ya zauna gabda ita yace "Karki damu bazan dade ba insha ALLAHU, danma Alhajinane ke kirana da ba inda zanje ina tare dake, kuma banaso kina yawan damuwa saboda banajin dadi ganin yanayin da kike ciki, karki damu yanzuu zan dawo" Goge mata hawayen fuskarta yayi da wani handkerchef mai dan karan kyau da kamshi.

Alhaji Abdul-aziz ne a bedroom din Hajiya Amina ya harde hannayansa yana kallan ikon ALLAH yadda ta dage tanata faman loda uban kayanta a akwati, jefi-jefi sai ta share kwallan idanunta, shi kuma yana jikin kofar ya tokare, yaga Aminan nasa ta burkice masa kamar ba itaba, kamar ba wacca take gudun bacin ransa ba, kamar ba wacce take musu fatan dawwama a duniya da lahira ba, kamar ba masoyiyarsa ta hakika ba, akan abunda baikai ya kawo ba zatabi ta daga masa hankali, gyaran murya yayi a karo na ba adadi yanaso yayi mata magana amma yana shakkar abunda zaije ya dawo, kara kallanta yayi yaga yadda ta kara ramewa, tafiya yayi yaje har inda take, kamo hannunta yayi ya zaunar da ita a lafiyayyan gadonta, A hankali yace "Cool down ma'am"

Kallansa tayi ta zabga masa harara tace "Ai idan kaga na kwana a gidanka toka tabbatar gawa tace ta kwana amma bani ba, yaya mukai dakai?, Shine danka tozartamu kaje ka kama ka kirasu a waya akan suzo su karbi sadakinsu, kana tunanin bansani bane, to wallahi abunda kakemin ya isheni a cikin gidannan, haka kawai yarana sun sanu mazajan rufin asiri amma kake kokarin tozartasu saboda sun maka laifi, ni na fada maka ban hanaka yi musu hukunci ba, amma hukunci daka yanke musu yayi musu tsauri da yawa yaya za'ai ka koresu kace suje duk inda sukeso, babu ruwanka da inda zasuje, saboda kasan idan sun lalace dani za ai kuka bada kaiba, nidai gwanda naje na nemo 'yayana mu zauna dasu cikin rufin asiri"

PHATEENJIDDAHWhere stories live. Discover now