*PHTEENJIDDAH*
*MALLAKAR*
*_Ƴar Gafai_*
*(Mum Irfaan)**WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
33Cikin murna da d'oki Mom tace "to" kwalawa 'yar aikinta kira tai ta fara sanar mata abubuwan daya kamata, sannan ta shiga part din su Phaty, cikin jin dad'i da annashuwa tacema Phaty "Daughter idan bakya komai ki d'anzo ki tayani aiki, kinjii yarinyata, ki bar Jiddah nasan tana bacci yanzu"
Phaty sakin baki tayi tana kallan Mom d'in nata ta kasa gasgata cewar Mom d'insuce ke fad'a mata kalamai masu dad'i ba tare da fad'a ba ko tsangwama, daka tsalle tayi farin ciki fal cikin zuciyarta, da k'arfinta ta dosa kitchen farinciki cike da zuciyarta tana fatan ALLAH yasa Mom d'insu ta d'ore a haka.
Hajiya Aina'u na hango gefen Alhajii, kallansa tayi ranta fal da bak'in ciki tace "Alhaji magana fa nake maka tun safe ammaa ka mayar dani wata 'yar iska, tsakani da ALLAH abunda kakeyi ya kamata?"
Alhaji kallanta yayi yace "To ni kuma mai nayi?"
Aina'u tace "Ai ka fini sanin abunda kayi, nace maka wannan goron da tulin sweet d'innan na menene danaga ka shigo dashi jiya da daddare?"
Murmushi irin na manya Alhaji yayi cikin tsokana da zolaya yace mata "Abokiyar zama zan samar maki, naga alamun gidan baya miki dad'i shiyasa nakeson na kawo maki wacca zata runk'a tayaki hira"
wata k'atuwar harara Aina'u ta bishi dashi tace "Aini kishiya ko alahira bana fatan na kasance da iya balle a duniya, Alhaji bana k'aunar irin wannan wasan kaji na fad'a maka kaimin wasan komai k'wak'walwata zata iya jura amma banda ta kishiya, me za'ai da kishiya ALLAH kaimin tsari da ita duniya da lahira"
Alhaji kallan mamaki ya bita dashi yace "Zanso inga ranar da zaki kar6i kishiya hannu bibbiyu, amma wannan kishin naki gaskiya yayi yawa kar wataran ya kaiki ga halaka fa, yaka mata ki runk'a sawa kanki namiji domin mata hud'u aka yishi bake kad'ai ba, idan da rabon dake kad'ai zaiyi rayuwarsa har lahira sai kiga bazai ta6a yin auran ba, fatanmu ALLAH yasa mu dace"
Turo baki gaba tayi tace "Ameen dai" tashi tayi tabar d'akin ba tare dataji kayan sa ranan wanene ba, tana cikin sauka daga downstair taga Umar zai shiga part d'in babansa, wata harara ta maka masa sannan ta saki wani murmushi tare da cewa "A'a Son za'a shiga gurin Abba kenan?, d'an Abban kenan d'an gatan Abba"
Umar kuwa ko kallanta baiba ballema yasan tanayi, ra6awa yayi ta gefenta ya wuce ba tare da yace mata uffan ba, binsa tayi ta harara tace "Dan wulak'anci kawai dashi, ai wallahi nidakaine zakasan ni kake wulak'antawa a cikin gidannan, nice fa, ba'aimin ba ya mutum ya k'are balle kuma mutum ya shiga gonata" Sauka tayi tana ta zabga ruwan tijara ba tare da kowa yasan me take ba.
Umar ne durk'ushe gaban mahaifinsa yana fad'in "Yanzu tsakani da ALLAH Abba sai dare zakukai kayannan mai makon kuje ido naganin idon, kuma dan ALLAH Abba ka rok'anmin alfarmar ko sunsa rana mai tsawo kace kunason bikin da wurine saboda an bani wani course ne zan tafi da ita please Abbana"
Alhaji kallansa yayi sakeke yana kallan Umar, sai kuma ya bashi tausayi ko ba komai Umar yayi hak'uri da har yakai iyanzu baya neman manta banza ga abokanansa nan daga mai 'yaya biyu sai mai 'yaya uku, amma gashi shi yanzu zaiyi auran, da fari ya d'auko ko Aljanu ne suka auresa sai kuma yaga lokacin auranne baiyi ba, gyaran murya yayi yace "Amma Umar baka da kunya ko kad'an ni kake ba sak'on idan naje nace kar asa ranar da yawa saboda na gama musu komai na biki shiyasa xan fad'a musu, an fad'a maka auran mace da namiji d'ayane?, to bari kajii na fad'a maka abunda baka sani ba, auran mace yafi kashe kud'i nesa ba kusa ba, kuma kaga ba ita kad'ai zai aurar ba ita da 'yar uwarta zai aurar dukda mutum ne mai kud'i yaka mata mu jira muji hukunci dashi zai yanke hakan yayi, kai kuma basai ka k'ara hak'uri ba ana saka ranar fa zakaga abun yazo ba wuya, wuyarta ba'asaka ranar ba"
YOU ARE READING
PHATEENJIDDAH
ActionYana maganane akan yara guda biyu Wanda suka kasance tagwaye, gashi Allah yayi musu rashin basajin magana ko kadan, sannan kuma ina gargadin iyaye da su runka jan 'yayansu a jiki basu wancakalar dasu ba akan wani dalili nasu na daban,👭