page 18

112 6 2
                                    

Kallan cikin gidan yake cike da tsana, wani sashe naga ya nufa a cikin gidan, da dukkan alamu 6angaranshine, tafiya yake cikin k'asaita da tak'ama, mai bawa flowers ruwa yagani, yace "sannu baba", cikin fara'a da farin ciki wannan d'an tsohon yace "oyoyo ga magaji, oyoyo ga alhaji k'arami."
    Murmushi kawai Umar yayi, ya gaisheshi cike da labani da biyayya, tsohon kuwa sai washe baki yake, Umar har yayi hanyar part d'inshi wannan d'an tsohon yace "A'ah Alhaji k'arami baza kaje ku gaisa da Alhajin naka bane?"
    Umar juyowa yayi ya kalleshi yace, "Dama Alhaji ya dawo?, yaushe ya dawo?
    Tsohon yace "Jiya da daddare jirginsu ya sauka, na d'aukama sabodashi kazo gidannan, tunda bama ganinka sai Alhaji na nan"
    babbban part d'in gidan ya nufa, yana cewa tsohon "Dama ai baba ka ruga ka samin ido yasin, yanzu har kasan lokacin da nake dawowa gidannan, bari naje mu gaisa dashi"
   "Adawo lafiya" cewar d'an tsoho.
    Tafiya yake har ya isa wani makeken falo, wata dattijuwar mata nagani, wacca ak'alla zatakai shekara sittin, kana ganinta kasan ansha duniya tun ba yauba, fuskannan tata tasha man bleaching, gashi ta hakince akan kujera tad'au remote tana canza tashoshi, taunar cingam take ji kake 6as-6as tana taunawa, Umar kuwa tunda ya hangota tuni naga ya 6ata fuska, har zai juya, komai ya tuna, sai kuma ya fasa, sallama yayi a ciki-ciki, wanda ke kusa dashine kawai zai iyajin wannan sallamar, tuni ya tamk'e fuska, ya d'auko wani bak'in glass ya saka _Oh my God, kawai nace dan kuwa glass d'innan ba k'aramin kyau yayi mashi ba_ shiga d'akin yayi yana k'ok'arin hayewa sama, anan matar ta lura dashi, tana ganinshi tace "Oyoyo my lovely son, u ar highly welcome, Son, zo mana, zoga Momynka, kasan yadda nai missing....."
Bata k'arasa  bama, taga ya haura sama ko kallan inda take baiba, k'wafa tayi tace "Wlh nida kaine acikin gidannan, wannan d'an iskan girman kan naka saina sauke makashi, kuma zanyi maganinka wlh, saidai ko ba hajiya aina'u ba"
Tana cikin magananne komai ta tuna Oho, naga tayi zumbur ta tashi, wani shashe ta shiga na cikin d'akin, gudu-gudu, sauri-sauri kawai take, tana zuwa wani d'an ma dai-daicin d'aki naji tana knocking, tana fad'in "Ke Dija, dan k'aniyanki, ki bud'e nace, bud'e mana"
   Wata murya naji, kamar ta 'yar maye tace "Hajiya wai mai zan makine, kinsan ina hutawa banason damu"
Hajiyar tace "To kar ALLAH yasa ki bud'e, kingama tafiyata, dama waccan tak'adarin yaronne ya dawo, nakeso ki k'arashe planning d'in da muka had'a, kinga ko in baki bud'e ba kinma kanki"
    Wufff Dija ta bud'e d'akin, cikin zumud'i da d'oki tace dan ALLAH hajiya da gaske ya dawo?"

_Kallan Dijar nayi,_ ba laifi tana da nata kyan dan baza akirata da mummuna ba, saidai fuskarnan tata, tasha uban man bleaching ga wani k'atoton attach akanta, sai kace ba musulma ba, ga jikinta yasha zanan tatoo, idonnan nata yasha eye shado da gashin ido, idan kaganta tamkar wata aljana.

   Harararta hajiyar tayi tace mata, "Ina wasa dake kenan dahar zan zauna ina maki wasa, to gashi can yana gurin ubanshi bansan ranar fitowarsa ba kuma, ni wlh wannan yaron ya hanani rawar hantsi acikin gidannan, keee"
   Hajiya ta waiga tanama Dija magana tace "Wlh ki tabbata kin saka abunnan adaidai, inba hakaba kin cuceni, kuma kin cuci kanki, dan dazarar kin sameshi ai kin zama billionaire, ni kuma na zama Auntyn billionaire, dan haka kibi step d'innan dakyau, dan naga alamun bakyason samunsa, da kinaso aida sauran aiyukan dana bakii kimai da haka bata faru ba, ki tabbatar yaci wannan, kinji na fad'a maki, ki tsaya agabanshi har sai kinga maganin ya faramai aiki, kinga shikenan, dan da zaran ubanshi yaji fyade yayi maki babu mai hana yin aurannan dan dole ya aureki, ko yanaso ko bayaso, shiba ustaz ba, yau zaki sauke mishi ustazancin nashi, tunda munyi munyi mun kasa dashi, ina tunanin wannance hanya mafi sauki agaremu"
    Shewa suka saki kamar suna gidan biki, da sauri kuma suka rufe bakin, suna dariya k'asa-k'asa, Dija tace "Shiyasa nake k'aunarki Auntyna, sai yanzu na tabbatar cewar kina k'aunata, ni kuma nai miki alk'awarin idan har nasamu dama kema dole ki dama, kuma haihuwar fari da zanyi zan mallaka maki kyauta tunda ALLAH ke bai baki haihuwa ba, karki damu Auntyna muna tare"
Hajiya tace "Inhar ban gina rayuwarki ba rayuwarwa zan gina?, karki damu k'anwata komai kikace nasan zakimin arayuwa, bari naje naji uwarmai suke tattaunawa"
    Dija tace "To Aunty ina key d'in d'akinsa wanda muka yanko? kinsan da zarar ya shiga d'akinnan bazai bud'emin ba, komai nacina kuwa"
Hajiya tace  "Kije d'akina akan bedside drower zaki ganshi na ajeshi, daganan kije kitchen akwai best food d'inshi sai kiyi using dashi"
     Hajiya bata zarce ko inaba sai a makeken falon alhajin, acan ta hangosu, suna hira irinta d'a da uba, ta6e baki tayi tace "Munafukai zanyi maganinku very soon ne"
   K'arasawa tayi cikin d'akin tanata washe hak'oranta, cikin farin ciki tace "Son, ashe nan kazo, d'azu inatai maka magana, kai gaba nasan bakajini ba ans d'aukin ganin Dad, to kaganshi kaji dad'i ko"
   Tanata faman zabga murmushi kamar da gaske, Umar yi yayi kamar bai jitaba, ya cigaba da danna wayarsa, dariya Alhaji yayi yace "Ta ina zai jiki, yana d'aukin yazo yayimin albishir, yanzuma wai kunyata fa yakeji shiyasa kikaga ko d'aga kai baiba"
Murmushi tayi tace "Alhaji wani irin albishirne da bai fara fad'ama mamansa ba saikai, gaskiya nayi fushi da yawa"
Dariyar jin dad'i Alhaji ya k'arayi, yadda yake ganin matarsa tana kulamai da tilon d'ansa a duniya, shiyasa yake k'ara k'aunarta, cikin jin dad'i da annashuwa yace "To kwantar da hankalinki, suruka yayi maki, yanzuma so yake atura aje a nemamai izinin yin magana da ita"
  Ai tunda Alhaji yace suruka akai mata, gabanta ya fad'i, ruwan da zatasha ya k'warar da ita, Sosai take tari, acikin zuciyarta fad'i take _"Shikenan na shiga uku na lalace, wannan d'n iskan bokan aikinsa baiyi yadda yakamata, gobe insha ALLAHU zan dirar mai"_
     Alhaji fad'i yake "sannu, sannu hajiya"
  Murmushi tayi tace "aima tarin ya tsaya"
Umar kuwa a zuciyarsa fad'i yake _"dama kin mutu, bak'ar munafuka kawai"_
Wani murmushin ta k'ak'ulo tace "Son, a ina ka samo mana itane?, kuma 'yar gidan waye?"
Alhaji yace "Ai babanta ba 6oyayye bane, 'yar gidan Alhaji Abdul-aziz mai gwal ce"
Hajiya tace "ALLAH ya sanya alkhairi, ALLAH yasa kuma abokiyar zamace"
"Ameen, Alhaji yace.
Shidai Umar shiru yayi, yace ma baban "Alhaji bari naje d'aki, inada wasu ayyukan da ban gama ba"
harya mik'e baban yace zauna kaji, Hajiya tunda taga ya koma ya zauna ta d'auko wayanta ta turawa Dija message kamar haka
          _"Ke shashasha, kiyi shiri mai kyau inba haka ba, shirinmu ya 6aci, kinada labarin neman aurema yake?, to kisan yadda zakiyi wannan abun ya faru ayau, inba hakaba wlh mun kad'e, akwai wata humra a d'akina, kije ki sakata, ki bad'e jikinki da ita, kinji na fad'a maki, itama akwai sihiri a cikinsa, ki kuma gaggawar rigasa shiga d'akin, dan gashinan zuwa"_
     Umar duk yana hankalce da ita azuciyarsa yace _"yau kuma mai aka shiryamin agidan?, dan kusan kullum akwai sabon makirci"_
Alhaji yace "Shikenan zan samu k'anin nawa da sauran 'yan uwa sai suje ko"
    Murmushin jin dad'i yayi yace "To abba, ALLAH yasaka da alkhairi"
Cillo mai filo Alhajin yayi yace "bako kunya ko"
   Da sauri ya fita yana dariya, Hajiyama dariyar take, amma cikin zuciyarta cunkushe da bak'in ciki.
   Umar bai zarce ko inaba sai part d'insa, yana k'ok'arin bud'e d'akin kenan yaji sak'o ya shigo wayarsa.........

PHATEENJIDDAHWhere stories live. Discover now