Yace kamar fa tana numfashi yaka mata ayii gaggawar kaita asibiti, ai tuni aka samu wani tsohon machine aka hadasu da wasu yan sandan gari aka kaita asibiti mafi kusa dan ceto rayuwarta da gaggawa, suna zuwa ba'a bata lokaci ba wajan karbarsu kasancewar sunje da police, nan take aka kaita emergency sannan aka bukaci a kira wani nata dan a sanar dasu, nan take wannan tsohon ya mika woyoyinta wanda ya gansu a kasa, touching din dukta dagargaje sai karamar wayartace batai komai ba, a haka har suka duba wajan kira dan suga dawa tayi waya ta karshe, suna dubawa sukaga an My Aunty nan take aka dannawa Hajiya Aina'u kira aka sanar da ita halin da ake ciki.
Nan take Hajiya Aina'u ta finciko gyalanta tana kokarin gyara zaninta amma sai kara sullubewa yakeyi tana ihu da kururuwa haka ta shiga mota bata zarce ko inaba sai asibitin da akai Dija cikin gunjin kuka ta tambaya inda aka kwantar da Dija, kasancewar kowa yasan an kwantar da ita babu bata lokaci aka kaita dakin, Hajiya Aina'u tana ganin Dija da yadda halittatta ta koma nan take ta rushe da matsinancin kuka tana fadin "Khadija haka kika koma?, yanzu haka halittatki ta koma Khadija?, Mun shiga uku mun lalace, Khadija kinga yadda kika koma kuwa?, Innalillahi wa inna ilayyir raju'un wallahi nayi imani ko me getman din gidanmu bazai yadda ya aureki bare kuma Umar da kike saka rai kike mafarkin samunshi"
Dija cikin zafin ciwo da wahaka tace "Haba Aunty ya zaki runka sagarmin da gwiwa alhalin kece wacca tafi kowa bani karfin gwiwa akan lamarina nida Umar, kinsan duk abunda na samu daga gareshi dole hannunki zai dawo, please Aunty kice zan samu Umar, zan sameshi cikin sauki kamar yadda masoya suke muradin su kasance tare"
Hajiya Aina'u kara fashewa da kuka tayi tace "Gaskiya Khadija wannan lamarin saidai ya kasance miki amafarki dan a gaskiya bazan miki karya ba wannan abun bazai yuwu ba, barima nakira Alhaji na sanar mai da halin da ake ciki"
Dija cikin radadin ciwo tace "Dan ALLAH ki kira Umar ki fada masa shima, nasan zaizo yaga halin da nake ciki"
Hajiya Aina'u tace "To shikenan, ALLAH yasa yazo dan naga dan ra'ayine"
Nan take Hajiya Aina'u ta sanarwa da Alhaji tare da yan uwa da abokan azziki akan Dija tayi accident, Alhajin Umar da yazo yace a maidata asibitin cikin gari kuma babban asibiti ba'a bata lokaci ba aka maidata babban asibitin cikin gari, nan take aka karbesu aka basu lafiyayyan daki kasancewar Alhajin Umar yana da abokai acikin asibitin kuma suna matukar ganin girmansa, anan aka bar Dija tare da Hajiya Aina'u ana basu kyakykyawan kulawa.
Phaty ce ta sauko daga upstair tana tafiya tamkar wata hawainiya, tayi kyau matuka, bakar doguwar riga ta saka tai rolling dinta fuskarnan tata tasha makeup kamar wacca zataje gasar sarauniyar kyau, Mommynsu zaune a makeken falon kasa ta hango yartata kin kowa wanda ya rasa tace "Dotanah ina zuwa haka?"
Phaty murmushi tayi yayinda dimple dinta suka lotsa gabaki dayansu kyanta ya kara fitowa tace "Mommy kenan, zan fita ba tare dana nemi izininki ba, kawai inaso na dau hotunane a garden"
Mommynta dariya tayi tace "Wowww!, harna hango kyan da hoton zayyi, idan kin dauka ki kawomin nagani"
Murmushi Phaty tayi tace "Shikenan Mom insha ALLAHU zan kawo miki, dan ALLAH idan Sis ta sakko kice tazo ta daukan nayi-nayi tazo taki zuwa sbd tana waya da yaya Dausayi"
Mommyn tace "Jeki karki damu nasan tana gama wayar zaki ganta, akwai wanda yakai Jiddah san daukar hoto a gidannan, kawai dan tana wayane, buh ina tabbatar miki tana gamawa zaki ganta saidai inba Jiddah bace"
Dariya Phaty tayi tace "Kuma fa hakane mommy, zatazo ta sameni ai"
Fita tayi ta dosa hanyar garden tafiya take tamkar hawainiya yayinda Umar ya saki baki da kunne yana kallanta dan ko kadan bai taba ganin Phaty tayi wannan kwalliyar ba iyakacinta simple makeup, agaskiya Phaty ta tafi da Umar yadda mai karatu baya tsammani, yana zaune cikin motarsa bai fito ba yana kallanta, yayinda ita kuma ta doshi hanyar garden tana ta faman daukan hotunanta hankalinta kwance, dukda rashin kiran da Umar bai mata yana damunta amma haka ta daure zuciyarta danta kwatarma kanta yanci a wajansa, hotonta takeyi hankalinta kwance, yayinda Umar Phaty ta gama batamai lissafinsa, ya rada yadda zayyi kuma yasan tabbas yayi mata laifi dan tuh randa abunda ya faru tsakaninta dashi bai kara kiranta ba dan lokacin haushinta yakeji, cikin kwana biyu ya tabbatarma da kansa bazai iya rayuwa in babu ita ba, yanzu satinsu daya cif da fada amma bai daga waya ya kirata ba, yanzu ma yaso ya samu Jidda ya fada mata sakonshi ya wuce amma yaga lallai yau sai yaga Phaty bazai iya tafiya ba tare da yaji daddadar muryarta ba, runtse idanuwansa yayi yana imaging yadda zai shawo kan Phaty dan yasan tunda ta shareshi itama kwana biyu ya nuna cewar itama fushi take dashi, ajiyar zuciya ya saki sannan ya dau waya ya kira Jiddah ya fada nata yana harabar gidansu, Dama Jiddah ta sauko dan taje wajan Phaty yin hoto kawai ta hango motar Umar.
YOU ARE READING
PHATEENJIDDAH
ActionYana maganane akan yara guda biyu Wanda suka kasance tagwaye, gashi Allah yayi musu rashin basajin magana ko kadan, sannan kuma ina gargadin iyaye da su runka jan 'yayansu a jiki basu wancakalar dasu ba akan wani dalili nasu na daban,👭