*PHTEENJIDDAH*
*MALLAKAR*
*_Ƴar Gafai_*
*(Mum Irfaan)**WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
*Please Subscribe My Channel*https://www.youtube.com/channel/UCWyfuDW1EWCBqzOrwaCnq3Q
Domin kawu muku Audion littattafan Hausa
6*WASHE GARI*
Tunda asuba phaty ta tashi ta fara shiri, Jidda na hango ta rafka tagumi a tsakiyan gado, tanata kallon Phaty yadda takefa faman farin ciki, gyaran murya tayi tace,
"Sis waida wuri zaki tafine?, naga sai faman shiri kikene".
Juyowa Phaty fuskartaa cike da nishad'i, yanayin dataga Jiddah ne saita bata tausayi, tace,"Haba Sis kiyi ha'kuri mana na fad'a miki bazanyi sati d'aya ba zanma dawo, sai kace wacce inta tafi bazata dawo ba, nasan zakiji gidan ba dad'i amma kiyi ha'kuri kinji Sis".
Ajiyar zuciya Jiddah tayi, sannan ta sauka daka kan gado, taja trolley din Phaty tana had'a mata kayanta, tace,
"shikenan Sis tunda kinmin al'kawarin cewar bazaki kai sati d'aya ba kuma karki manta al'kawari cikawa" murmushi phaty tayi tace,
"karki damu muna tare ai, bari naje na fadama Mom na shirya saiki rakani parking space ko 'kanwata,"
Upstair Phaty tahau tana tufke gashin kanta, domin kuwa ta gama shirinta mayafi kawai zata saka, sallama tayi ta tura 'kofan d'akin ta shiga, hango Mom dinta tayi akan gado tana danna lapton, azuciyarta tace,
_"Mom an fara business kenan yau gidan tsit zakajishi"_
'Dagowa tayi ta kalleta, sannan ta ansa sallamar, ta maida dubanta da abunda takeyi, tace, "lafiya daiko?,"
Phaty cikin d'ar-d'ar tace,"Mom dama na shiryane nace bari na fad'a maki"
Kallanta tayi dakyau tace,"wannan rawar kanfa?, daga ina yake?, yanzu zakice zaki tafi sai kace wacce ake kora, ki kiyayeni fa, wlh saiki fasa tafiyarnan, amma.." sai tayi 'kwafa alamun zaki sanine.
Cikin sanyi jiki Phaty tace,"dama Mom naga bakyasan tu'kin darene shiyasa nakeson na isa da wuri, kar dare yayimin a hanya"
Yanayin yadda taga Phaty tanayi da alama ta tatsorata da mahaifiyartane, sai maman taga bata kyauta mata ba, gyaran murya Mom din tayi tace,
"shikenan, akwai enought kud'i a hannunki kuwa?"
Phaty d'aga mata kai tayi tace, "inada 10k". Mom din tace "okey ki duba bedsite drowerna ki d'au 20k ina tunanin kika had'a dana wurinki zai isheki ko?"
"Ah Mom zai isheni nagode ALLAH ya 'kara bud'i da nisan kwana"
"ameen" ta cigaba da aikin gabanta, Phaty kuwa zuwa tayi ta d'iba kud'in tabar d'akin, tana rufe 'kofar tace "yess" da 'karfi, Mom tace "me kike cewa", Phaty tayi saurin cewa "Mom wlh bigewa nayi".
Tayi saurin barin wuraren, bata zarce ko inaba sai kitchen, taga mai aikinsu tace, "dan ALLAH ladi d'an had'omin shayi mai kauri ina d'aki, kiyi sauri fa".'Dakinsu ta shiga tace, "kai Sis nagode sosai fa harkin gama shiryamin komai kenan, bari nad'an 'kara shafa powder, kafin ladi ta had'omin break fast, nakama hanya karnai dare, "hmmm" kawai Jiddah tace.
Tana cikin shafa powder ladi ta kawo mata break fast, a daddafe tasha tea din, ta d'auko hand bag d'inta, tace "yawwa Sis mi'komin purse d'innan karna manta, bari na kira misbahu mai gadi yazo ya d'aukanmin trolley d'ina."
Jiddah tace,
"No Sis basai kin kirashi ba, bari nad'aukar maki zan iya, muje kawai"
Phaty tace "okey" tayi gaba Jidda tabita a baya suna zuwa wurin motar Phaty ta bud'e boot, Jidda ta saka mata trolley, sannan ta rufe boot d'in, Phaty zagayawa tayi yahau driver seat, tace "to Sis ni zan wuce ai mana addu'a"Jiddah 'ko'karin maida 'kwallan idonta tayi, tayi murmushi tace "shikenan Sis ALLAH ya kaiki lafiya ya dawo mana dake lafiya, please Sis ki kulamin da kanki kinji". Murmushi phaty tayi tace ba komai insha ALLAH komi normal zai zama sai munyi waya, ina sauka zan kiraki byeeee" haka Phaty tana motarta, Misbahu mai gadi yayi saurin bud'e mata get kar yayi laifi,
_niko nace safe journey phateenjiddah_
"Sir gashi ana kiranka" cewar Jafar, idanunsa a lumshe yace wake kirana haka?, banace ka daina kawomin waya ba, duk wanda ya kiraka kace masa bana kusa that's all,"
"Sir ka gafarceni wlh shugaban 'kasa ne ke nemanka yace dakai yake son kuyi waaya."Mi'ko hannunsa yayi alamun ya basa wayar, mi'ka masa wayan yayi, yace masa, "jeka zan nemeka"
"Hello"
_kawai naji yace, ya banko d'aki don karna jiyomuku abunda zaasuce shida shugaban 'kasa_?
Phaty tsaya a ko inaba sai a Sokoro road, anguwa ta masu kudin gaske, tsarin anguwar, tsarin turawane, domin kuwa turawane suka ginata, _Wow kawai nace domin anguwar tatafi da ni_.
Wani dan'ka'kareren gida naga ta nufa aka wangale mata get, gidan ya tsaru, komai na gidan abun burgewane, parking space taje tayi parking motarta, ta fito, ihun wasu 'kananan yara na jiyo wanda shekaransu bazasu wuce biyar zuwa bakwai ba, "Oyoyo aunty phaty" kawai suke cewa, wata had'ad'd'iyar mata nagani ta fifo da 'katan cikinta, tanata faman zabga murmushi, tace, "welcome daughter, naga kinyi saurin zuwane na d'auka sai dare""Kai aunty fa'iza sai kace bakisan Mom batason tu'kin dare ba"
"hakane na tuna autar Mommynta da daddynta"
"ta6 nice auta?, ALLAH ya kiyaye Jiddah dai zakice"Haka suka jera sunata faman zabga hira kamar wasu 'kawaye.
_Nasan masu karatu zasuce ance Alhaji Abdul-aziz d'an ketawa ne, ya akai 'kanwarsa take zaune a abuja?, abujanma anguwan masu kudi, tabbas fa'iza tayi rayuwarta a 'kauyan ketawa, kasancewar tayi secondary, shiyasa tad'an waye akan en matan 'kauyan a haka har ALLAH ya fito mata da mijinta wanda yake zaune a Dausayi, ma'kotan Ketawa, sunyi zaman Dausayi nad'an 'kalilan, malam yusha'u ya fara zuwa cirani, har ALLAH yayi mashi nasibi, ya dau matarsa sukabar 'kauyan dausayi, suka dawo abuja da zama. wannan kenan_
Phaty na sauka a d'akin makwancinta, ta d'au wayanta ta kira Mom dinsu, suka gaisa ta shaida mata tazo lafiya, suna gama wayan ta kira Jiddah itama ta shaida mata ta iso lafiya.
Ajiye wayan tayi ta shiga bathroom danyin wanka, tana fitowa ta saka kaya marasa nauyi, ta fito donyi hira da auntynfa fa'iza."Jafar" cewar umar cikin muryansa mai sanyi.
"Yess sir"
"ka had'a kayanka da nawa gobe zamu wuce abuja, mu biyu kawai zamu, inyaso mayi amfani da soldiers d'in can"
"Okey sir". Jafar ya tafi yana murnar Ogansa shima zashi, don bayason yace wurin taronnan shi kad'ai, babu mamaki shugaban 'kasane ya ro'kesa akan ya daure yaje". haka Jafar dai ya tafi yanata fama mamakin yadda Ogan gidansa ya amince zashi abujannan."Aunty Fa'iza" cewar Phaty.
"na'am yar gidam auntyna",
"Wlh Mom dakyar ta barni nazofa, da magiya da ban ha'kuri ta barni".
Dariya fa'iza tayi kice halin anty dai har yanzu yana nan?, to mai yasa baki fad'a mata gaskiya ba bikin 'kawarki zaki?""Eyye ince mata bikin 'kawa zani ai wlh aunty fa'iza saita kusan kasheni da duka ta6"
Dariya fa'iza ta kumayi, tace lallai ma ba aso ana takurama yaran yanzu wlh, batasan ALLAH bane mai karewa ba, ba wayanta ko dabararta bane zaisa ku natsu, wai yaushene bikinma?"
"Wlh aunty gobene, kumafa nice zan mata babbar 'kawa kinga in banzo ba akwai damuwa wlh"
Aunty fa'iza tace, "babbar damuwa ma dan bazataji dad'i ba wlh ko kad'an"
_Niko nace aunty fa'iza? aradu gidogaki kema Phaty tayi, ba wani biki party zata?_
*To jama'a ga Umar zai taho abuja, koya abun zai kaya oho dai. FATEE DA UMAR a ABJ?*
YOU ARE READING
PHATEENJIDDAH
ActionYana maganane akan yara guda biyu Wanda suka kasance tagwaye, gashi Allah yayi musu rashin basajin magana ko kadan, sannan kuma ina gargadin iyaye da su runka jan 'yayansu a jiki basu wancakalar dasu ba akan wani dalili nasu na daban,👭