page 41

94 5 0
                                    

Security din tunda yaga hankalin ogansa ya tashi yayi maza ya garzaya asbiti dan kiran likita ayi musu taimakon gaggawa, yana zuwa ya shaida musu aka gunguro gado akazo aka saka Phaty a ciko, direct emergency room aka nufa da ita, Umar kuwa sai faman zirga zirga yake, a cikin zuciyarsa fadi yake _"Please Phaty karki tafi ki barni kamar yadda ummanta ta tafi ta barni, kamar yadda kanwata itama ta tafi ta barni, pleaseeee, ALLAH ya tashi kafadunki, inkika mutu bansan inda zan saka raina ba, bazan taba yafewa kaina hakan fa"_ runtse idanuwansa yayi saiga hawaye mai dumi ya sauka daga kan kuncinsa, sharewa yayi yama leken Phaty da yaga likitoci sun dukufa akanta dan ceto ranta sosai suke bakin kokarinsu dansu daidaita numfashinta amma abun yaci tura, wani likitane ya fito yana sharce gumi Umar yayi maza yaje inda yake yace "Doctor please yaya jikin nata?"

Doctor din kallansa yayi yace "Ka dage kawai da addu'a dan a halin da muke ciki yanzu mun kasa daidaita numfashinta, amma insha ALLAHU zamuyi kokarin mun daidaita, zuciyartace ta buga da karfi ALLAH yasa ma bata mutu ba, amma zamuyi kokarinmu yadda ya dace"

Umar kallansa kawai yake amma shi kansa baisan inda hankalinsa yake ba, dagamai kai kawai yayi ya bashi hanya ya wuce, zaman yan bori yayi yana ta faman addu'o'i, runtse idanuwansa kawai yayi ya rasa meke masa dadi a duniya, wata nurse ce yaga ta fitoo da gudu tana kiran doctor din daya fita tana cewa "Doctor kamar fa numfashin nata ya dauke dif dan babu komai da yake motsi a jikinta"

Cikin azama doctor din yabi bayanta yana bada sallahu a kawo masa abunda yazo dauka, tunda Umar yaji ance kamar bata motsi yayi wuf ya shiga cikin dakin tana nan kwance babu alamun numfashi ko kadan ajikinta, cikin sanyin jiki ya karasa wajan, yayi da wasu sauran nurses din sukai masa caa akab ya fita, doctor dinne ya dakatar dasu ta hanyar cewa a barsa, Umar kuwa baima san sunayi ba dan hankalinsa gabaki daya yana kan Phaty, kujerar kusa da gadon ya zauna, ya ruko hannunta sai yajishi ya saki ga sanyi a tattare dashi, addu'o'i kawai yakeyi daga cikin zuciyarsa, cikin sanyin murya yacrma doctor din "Dan ALLAH ka kara dubata ko akwai sauran numfashi tattare da ita" dan harga ALLAH zuciyarsa ta gama shaida masa da mutuwarta.

Doctor din ya karaso saitin kirjin Phaty danyaji ko zai samu bugun zuciyarta amma yaji shiru, hannunta ya kamo yana duba tsintsinyar hannunta nan ma yaji kamar ba alamun numfashi tattare da ita, doctor din kallansa yayi yace "Let me come, zan dauko wai abu da zai gasgatamin da zargina, kallan nurses din yayi yace zaku iya tafiya, dukanninsu suka fito a tare sai Umar kadai a dakin, hannunta na ruke da nashi, a hankali ya fara magana saitin kunnanta yana cewa "Bansan maiya faru dake ba Phatyna amma nasan koma menene ba karamin abu bane, ki saka haka a ranki wannan ce kaddarar taki kuma ki godema ALLAH datazo maki a haka, insha ALLAHU komai zai daidaita nai miki alkawarin haka, kinsan ina kaunarki, kauna wacca bazan iya misilta maki ba harsai munkai ga cin burunmu na mallakar juna, please Phaty ki daure ki tashi dan ALLAH ba danni ba, ina sanki a duk yanayin da kikr ciki, ki tai maki marayan ALLAH, inaji ajikina idan na rasaki tamkar na rasa wani jigona na rayuwanane, karki manta kinmin alkawarin twins masu kama dake, ki daurema zuciyarki ki manta da komi ki dauka wannan jarabawace daga ubangijinmu" kallanta yayi yaga babu alamun motsi tattare da ita, jijjiga hannunta yayi yaji shiru, baisan lokacin daya sakin wani marayan kuka ba, tabbas duk wanda yaga Umar a  wannan lokacin saiya baka tausayi, kamar ba Unar dan gayu ba, kamar ba Umar din da yan mata ke tururuwa a kanshi ba, kanshi yasa a gefen gado yanajin zafi a cikin zuciyarsa, shikenan a haka zai gama tasa rayuwar kenan dan baya tunanin zai iya soyayya da wata bayan Phaty, kamar a mafarki yaji an kara damkar hannunsa sai bai ankara ba ya ji gaba da tunani barkatai, dagowa yayi a firgice yana kallanta, inbai manta ba dazu kamar ta damka hannunsa, a hankali ya furta cewar "Fatima" Phaty kara damko hannunsa tayi, hawaye da dariya ne suka ziyarceshi lokaci guda, da gudu ya tashi zai kira doctor, yana kokarin fita saiga doctor din ya shigo, ruko hannunsa yayi yace "Doctor ta farka, wlh ta farka ta dankanmin hannuna, please doctor kaje ka dubamin ita"

PHATEENJIDDAHWhere stories live. Discover now