page 50

124 11 3
                                    

Ran Umar ya gama baci yadda mai karatu baya tsammani, kukan kura yayi zaije yaci uban Dija, Phaty tayi saurin dakatar dashi ta hanyar kissa da kisisina tace "A haba sweetheart me kuma zakai mata?, tayamu farin ciki fa tazoyi ba komai ba, karka damu ka kyaleta kawai"

Umar ranshi kara tafasa yakeyi ya kalli Phaty yace "In banda dabbace ita jaka da ita mai zai kawota a wannan lokacin, ki duba tym fa kigani sha biyu saura, nifa saita fitarmin daga gidannan, wallahi nafita karyar hauka, dan taga ina sarara mata shine har raini zai shiga tsakanin mu, wacece ita dahar zatazo tace zata kawomin wargi, please ki barni na nada mata na jaki gobe ko hanyar gidannan aka nuna mata akace tazo bazata tako ba"

Phaty wani irin kallo ta jefa Umar dashi tace "Kar damu, kaga dare yayi ka barta zuwa gobe saita tafi gida, kai mata uziri mana bakaga batada lafiya bane, kasani kanta ya bugu koka manta yau aka sallamesu?, ba'a gama tantance cewar ta warke gaba daya ko bata warke ba, ka kyaleta ynx kawai ta tashi ta gyara mana gadonmu ka nuna mata inda zannuwan gado suke ta shinfida mana shi" wani sexy kallo Phaty ta jefa Umar dashi tacemai "Burunka zan cika maka taree da mafarkinka, ka fiso muyi tarayyar aure a wannan dakin shiyasa zamu zauna amma da badan hakaba wani dakin zamuje mu kwanta, ka bata umarni akan ta gyara inyaso sai innuna mata dakin tmda zata kwanta kaji ko"

Umar tuni ya burkicema Phaty saboda wani irin sakonni take turamai da hannayanta masu taushi da santsi, kallanta yayi duk yanayinsa ya canza, kara matseta yayi a kirjinshi suka zauna akan wata kujera oneseater romancing dinta yakeyi tamkar wani mayunwacin zaki, dama ya dade da zare mata hijab dinta, sosai yake romancing dinta yadda mai karatu baya tsammani, Phaty kokarin kwace kanta tayi ta girgiza mai kai tare da yatsa daya ta wani irin salo tace "A'ah karfa mu aikata haram garin neman lada, koka manta bamu kadai bane a dakin?, yaka mata ka sakata aikinta ta kama kanta ta fice"

Runtse idanuwansa yayi wa 'yanda suka fara sauya kala yacema Dija "Keeee"

Dija shiru tayi zuciyarta na tafarfasa ranta na suya hawaye masu dumi suna gangaro mata a cikin zuciyarta fadi take _"Lallai na yadda kazantar da baka gani ba tsafta ce, wannan wani irin cin mutunci yau Umar yakemin, agabana yake latsa wata yake mata duk abunda yaso ya taba na jikinta abunda take mafarki haka ta kasance tare da ita dashi amma tana ganin mafarkinta bazai zama zahiri ba"_ share hawayan idonta tayi ta kara rufe kanta da blanket din.

Umar daka mata tsawa ya kumayi yace "Wallahi kika bari nazo inda kike to saina lahira yafiiki jin dadi kinji na rantse miki"

Dija jikinta sai bari yake dan tasan wannan kadan daga cikin aikin Umar dan baya da mutunci barinma idan allurar sojojinsa ta motsa gwanda ta rufama kanta asiri ta tashi kafin ya ballata a gidannan kuma ya balla banza.

Tashi tayi kanta a kasa ba tare data kalla inda suke ba, tana kokarin fita yace mata "Oya koma ki canza mana bedsheet kafin ki fita"

Ba musu ta tafi ta canza sai faman ruwan hawaye takeyi saboda takaici akan ita zama ta shimfida musu zanin gadon da zasu kwanta suyi iskancinsu akai san ransu, tana gama shinfidawa ta raba ta gabansu ta wuce ba tare data kalla dayansu ba tace mai "Na gaama"

Umar bai bata ansaba tana ficewa ya sakama kofar key ya ciccibi Phaty yana mata dariya bai direta ba sai akan gado, dariyar kuwa har tsakiyar ran Dija, dan ba karamin kular da ita tayi ba.

Umar tunda ya dire Phaty akan gado ya zare jallabiyarsa shima ya hayo gadon, ai Phaty tunda taga su biyune a dakin sai gabanta yahau lugude, tsoro da fargaba suka taru suka saukar mata, Umar dukya lura da yanayinta a kirjinsa ya saka kanta yace "Nasan kinajin tsoron wannan ranar amma dan ALLAH kiyi hakuri ki bani hadin kai Phaty please, kiji yadda zuciyata ke bugu ni nasan bazan iya daga miki kafa yau ba kimin afuwa ki bani hakkina ba tare da kinmim gardama ba" dagoda fuskarta yayi yace "Pleaseeeee dan kaunar da mukema junanmu"

PHATEENJIDDAHWhere stories live. Discover now