"Yawwa anan zaka saukeni mai adaidaita" Phafy ta fada hakan, yayi da akazo kofar gidansu, gabanta sai kara tsananta faduwa yake, cikin karfin hali ta dosa get din gidan tana knocking mai gadi yazo ya bude get din yana ganinta yace "Ranki ya dade kece haka da sanyin safiyarnan?"
Phaty murmushi tayi wanda baikai zuci ba tace "Eh nice baba, amma dan ALLAH karka fadama kowa cewar ba agidan na kwana ba"
Baba mai gadi kada kansa yayi alamun yaji ya bude mata kofar ta shigo, cikin sanda take tafiyar kasancewar gari bai gama wayewa ba, ta bayan garden ta shiga cikin gidan yayi da Jiddah ita kuna ta fito ta babbar kofa da kaya niki-niki a hannunta, tana tafiya tana sharce hawayenta, tana tunanin maganar Mom dinta na cewr ta tafi gidan Aunty Fa'iza komai ya lafa zata dawo insha ALLAHU, fita tayi daga gidan tana tafiya tana waigensa tana danasanin rayuwar da suka dauko tun a baya.
Phaty kuwa tana zuwa ta kofar baya ta shiga dakin, tana dubawa taga Jiddah bata ciki, duk a tunaninta ko tana kitchen ne tana hadama kanta break fast, kwanciya tayi ta rufe jikinta ta bargo tana hamdala babu wanda ya ga dawowarta tasan Jiddah ta ruga tasan ba agida ta kwana ba kuma tana da tabbacin zata rufa mata asiri kamar yadda ta saba, Phaty kwanciyarta tayi hankalinta kwance saboda jiya bata samu damar yin bacci da wuri ba, baccine mai dadi ya dauketa, tare da mafarkai masu saka mutum nishadi.
"A gaskiya Alhaji bazan taba lamunta ba wlh, yaya zakace ka yafesu kabarma duniya to wallahi baka isaba idan harkai ka barma duniya toni wlh banbarma duniya ba, inasan 'yayana ina kaunarsu karkai tunanin na hofintar dasune, wlh ina matukar kaunarsu, na yadda kai musu hukunci da yadace dasu amma bazai taba yuwuwa kace kai ka yafema duniyasu ba, yaran sukenan gaba da baya kace zakai musu baki wallahi bazan yadda ba saidai ko nima nabarma gidan naka, baka tsaya kayi bincikeba amma ka kama ka yanke wannan muguwar shawara, ina bazai yuwu ba wallahi, jiya fa da daddare ina kallan mugun dukan da kaima Mai Jidda amma kaji nace wani abune?, saboda naga ta cancanci dukan amma bazai yuwu kace suda gidannan har abada ba wallahi, kuma kana fadin cewar zaka maida kudin auransu dankai bazaka zama wakilinsu ba to ka maida amma ina da tabbacin nan gaba wallahi saikafi kowa nadamar yin haka, a tunaninka inka mayar bazasu bincika maiya hassada hakan ba?, kana so ka tonamin asiri ka tonama yaranka asiri sannan ka tonama kanka, wlh Alhaji ba......"
Runtse idanuwansa yayi yace "Kije ki bisu duk inda zaki, dama ina zargin dasa hannunki a cikin lalacewar yarannan, dan haka duk inda zasu kuje amma ba agidana ba, babuni babasu dan haka zabi ya rage maki kibi 'yayanki ko ki tsaya wajan mijinki ki nemi aljannata"
Hajiya Amina kallansa ta tsaya yi gatsetse, hawayan da suka makale mata suka gangaro, bayan hannunta ta saka ta gogesu tace "Shikenan, kamar yadda ka bani zabi na zaba ko 'yayana ko kai, to kasani na zaba 'yayana, dan kuwa duk duniya babu yadda zan canzasu, miji kuwa ana canzashi duk lokacin da ALLAH ya nufa, ga gidankanan mun barsa, kuma ina maka tabbacin na saka kafa na fita daga gidannan banga mai maidoni cikinsa ba wallahi tallahi kuwa kaji na rantse, zanje na rungumi kaddarar data samemu mu dasu, kuma nayi imani da ALLAH twins bazasu taba aikata zina ba nai musu wannan shaidar saboda nayi imani wannan jarabawace ta afka musu saboda yadda suke da tsoron ALLAH da kamun kai nayi mamakin haka daga garesu, saidai yanzu ba'a shaidan dan yau" tashi tayi daga durkuson datayi ta shiga cikin bedroom dinta dan hada kayanta a akwati, tana hadawa tana goge hawayenta da tafin hannunta, tana tunanin data kara bata rayuwar 'yayanta gwanda taje ta rungumesu ko ALLAH zaisa su gane hanya, amma tasan tabbas ta rabu da Alhaji Abdul-aziz tayi imani bazata kuma samun nagartaccan namiji ba gwarzon namiji, kuma bazata taba samun namijin daya sota tsakaninshi da ALLAH ba, amma ya zatai gwanda taje ta rungumi 'yayanta suke nan mata a duniya, dan idanshi ya yacewa duniyasu to ita bata yafe suba saboda tana kaunar 'yayanta.
Alhaji Abdul-aziz tsayawa yayi yana tunanin tabbas yasan Hajiya Amina kaifi dayace, tunda tace inhar tasaka kafarta tabar gidannan babu mai dawo da ita yasan tabbas zata aikata hakan saboda gashima ta hada harda rantsu, samun mata kamar Amina a wannan zamanin ba abu bane mai sauki dan yayi imani yanzu duk wacca zai nema bazata taba sanshi tsakaninta da ALLAH ba saidan dukiyarsa, Amina kuwa tun baida komai yake tare da jta ya zama dole ya dakatar da ita daga fitar da zatai, key ya dauko ya kulle bedroom dinta dashi yabar key din a jiki gudun kartasa wani key din kofar ta bude ta fice.
YOU ARE READING
PHATEENJIDDAH
ActionYana maganane akan yara guda biyu Wanda suka kasance tagwaye, gashi Allah yayi musu rashin basajin magana ko kadan, sannan kuma ina gargadin iyaye da su runka jan 'yayansu a jiki basu wancakalar dasu ba akan wani dalili nasu na daban,👭