*PHTEENJIDDAH*
*MALLAKAR*
*_Ƴar Gafai_*
*(Mum Irfaan)**WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
*Please Subscribe My Channel*https://www.youtube.com/channel/UCWyfuDW1EWCBqzOrwaCnq3Q
Domin kawu muku Audion littattafan Hausa
7Yau take juma'a ranar datayi dai-dai da birthday din Amin's, Phaty tayi shirinta tsaf kamar mai zuwa gidan biki, atamfa ta saka, kayan sunyi matuk'ar ansanta, sun mata kyau over, atamfar tai mata kyau yadda mai karatu baya tsammani, k'ananan kayanta ta saka a cikin hand bag d'inta, ta d'au key din motarta ta fito daga d'akinta, bata zarce ko inaba sai downstair, aunty Fa'iza tagani ta mik'e k'afafu ta zauna a tsak'iyan d'akin, dariya tayi tace,
"Kai Aunty Fa'iza wannan zama haka ko haihuwar tazone nazo na kar6a?". Aunty Fa'iza tace,"Idan zan yadda kowa ya kar6a haihuwata zan yadda ke ki kar6i haihuwatane, God forbid". Dariya Phaty tayi tace shikenan ALLAH yasa nak'udar tazo kafin na tafi ko kallonki bazan yiba keda mijinki har d'akina zakuzo kuna rok'ona na kar6a haihuwar, kinga a lokacin saina tuna miki da abunda kika fad'amin".
"hmmm". Kawai aunty Fa'iza tace, tace, "wannan kyau haka, sai gidan bikin kenan?""wlh kuwa Aunty Fa'iza, nayi kyau kuwa?". Aunty Fa'iza tace,
"kinyi kyau overr, wannan wankan duk namijin daya ganki saiya d'asa"
"da gaske Aunty Fa'iza?"
"Ina miki wasane wlh kinyi kyau sai kin dawo please ki kula da kanki kinga bakisan gari ba""Insha ALLAHU Auntyna, aitamin kwatancen wurin kuma bazai ban wahala ba insha ALLAHU, Aunty Fa'iza na tafi". Ta saka kai ta fice, Aunty Fa'iza tace, "sai kin dawo".
Phaty tana shiga mota ta kira Amin's, tace, "Beb na fito a ina kikace zan sameki?, owk saina taho ganinan zuwa nama fito".
Haka Phaty ta kama hanyarta ta zuwa inda amin's take, ta saka waka a cikin motarta sai rerawa take a hankali, tafiya take tana 'kara kallon garin abuja, sosai takejin nishad'i a cikin ranta, tafiyarta take hankali kwance tanata faman zabga wak'arta, batasan lokacin data saka wani wawan burki ba ji kake _kiiiiiii_ motar ta tsaya wani ashar data mulmula ita kanta batasan ta iya irinsa ba, d'aga kan da zatayi taga sojoji sun kashee hanya, saboda Ogansu zai wuce, "mtswww wa 'yannan kuma lafiya sukazo sunata fama tsare mana hanya", k'wafa tayi, ta samu ta shiga gaban sahun sauran motocin, Sosai sojojin suka gyara hanya suna jiran Ogansu ya wuce, agogon hannunta ta duba, taga lokaci sai tafiya yake domin kuwa hak'urinta yakusan k'arewa, zuge glass d'in mota tayi, taga wani mai taxi, tace, "bawan ALLAH sai yaushe za abamu hanya mu wucene?"
"Ranki ya dad'e idan kin bincikama ko tahowa baiba suka hanamu tafiya, babu mamaki zai d'au kusan awa guda bai wuce ba"
"What??... Shanya sukayi da suke jira ta bushe?"
"Ai kadan kika gani inhar akan major umar ne"
"mtsww kai ka sanshi, ta rufe glass din motarta, sai faman zabga ruwan tijara take". k'wafa tayi tace, "wlh minti goma naba koma wanene yazo ya wuce inba haka ba wlh wucewata zanyi "
Shiru-shiru major umar baizo ya wuce ba, Phaty in ranta yakai dubu to duka sun gama 6aci, tada motarta tayi, ta saka kai atitin, sunajin mota zata wuce, kowa yayi kanta, ita kuwa tuni ta kama kanta, na gabantane suka tsaya a gabanta, taso ta take hofi amma tasan ko tayi hakan itama wahala zatasha, taka burgi tayi ta tsaya, amma tak'i fitowa don tasan rashin mutunci zasuyi mata bad'an kad'an ba, wani inyamuri mai d'an banzan masifaa da tijara yazo, masifa yake akan ta fito, amma Phaty tak'i budewa barema ta fito, wani abu ya samu ya fasa mata glass d'in motarta, ji kake tarasss ya fashe, bude kofar yayi ya fisgota, dai-dai lokacin da mak'arraban major umar suka taho, dashi gogan, sauran kad'an ta fad'i, saboda fisga yayi mata bata wasa ba, kafin tayi wata-wata ya d'auketa da mari, kafin ya aje hannunshi, itama ta d'aukesa da mari, nan take umar ya juyo yaga mai yake faruwa, d'aga kansa da zaiyi sai yayi tozali da sanyi idaniyarsa, nan take sojoji sukayo kanta, dakatar dasu tayi, kaamar sokaye kuwa suka tsaya, tace,
"me zakuyimin wlh duk wanda ya k'ara gigin ta6ani saina nuna maku ba ko wace mace ake ta6awa a zauna lafiya ba, kun kama kun shanya mutane sai kace kun shanya wanki, anan guri kowafa yana da uzirinsa, kai kuma ta nuna wannan inyamurin tace wlh baka mareni a banza ba, karkai tunanin na rama, hakan bayana nufin na kyaleka bane, motace ka fasamin ko, kaje da ita kaine matsiyacin mota."
Motar ta bud'e tad'au abubuwan dazata buk'ata tabar masu motar a wurin, tafiya take kawai amma ita kanta batasan inda take dosa ba, ranta yayi mummunan 6aci, major umar yasha zagi bana wasa ba a gurinta, dan gani take shiya ja mata wannan cin mutunci.
Umar kuwa tunda yaji tace acikin soja wani ya mareta, nan take k'wak'walwarsa ta daina aiki nad'an wasu dak'k'ai, be ankara ba yaga Phaty ta d'anyi mashi nisa kad'an, tana ta tafiya, driver dinsa yayi ma magana shida jaafar "Ku sauka", ko kad'an basu gane abunda yake nufi ba, sai sukai kamar basu jishiba, wata uwar tsawa ya sakin masu, _ni kaina saida na razana_ "nace ku sauka koku kurmayene?, jafar, koma wanene ya mari waccar yarinyar, a fad'a masa yaje gida andakatar tashi".
To kawai jafar yace, yayi gaggawar sauka domin kuwa yaga ran oganshi a 6ace yake, suna sauka umar yaja motar a guje, bai tsaya a ko ina ba sai gun Phaty, parking yayi ya fito yazo inda take, tafiya kawai takeyi, gabanta yasha ya tsaya, kokad'an batamasan anyi parking ba balle hartasa ran akwai mutum, mutum kawai tagani agabanta, d'aga kai tayi taga wani santalelen saurayi agabanta, atunaninta gamo tayi kawai saita maida kanta k'asa, acikin zuciyarta tace _"lallai inason film dinnan da yawa, yanzu har gizo omer ya fara yimin"_Sallamar da yayi matane ta dawo daga dogon tunaninta, kallansa tayi sama da k'asa k'ananun kayane a jikinsa, sunyi matuk'ar yimishi kyau, banza tayi dashi ta ra6a ta gefenshi zata wuce, nan ma ya tare "please dan ALLAH ki saurareni," banza tayi dashi, ta k'ara ra6a wata hanyar zata wuce, nanma karewa yayi, yace,
"dan ALLAH ki tsaya dan kaunar da kikema twins sis d'inki ki tsaya,"
Cak ta tsaya, koma wanene wannan ya sanni, to a ina?, nida ba zuwa abuja nakeyi ba sosai.
"Nasan kina da tambayoyi akaina amma dan ALLAH shiga mota zamuyi maganane". Ba musu, ya bud'e mata baya ta shiga, shima ya shiga baya, zama yayi gabda ita sosai dan har yana gogan jikinta, matsawa tad'anyi, tace, "inajinka kayi sauri dan inada abunyi".
Kallanta yake cike da shauk'in so da k'auna, murmushi bayyane a fuskanshi, shirun dataji yayi yawane yasata d'agowa, gabantane yayi mummunar fad'uwa saboda yanayin yadda yake kallonta, daurewa tayi tace,
"dan ALLAH idan ba abunda zakacemin zan sauka". Kallonta yayi dakyau yace,
"maiya had'aki da sojojin can?"Kukan da batayi ba d'azu, shine ta fara, kuka kawai takeyi, umar tsayawa kallanta yayi, domin kuwa yasan abunda ciwo, gani yayi batada alamun dainawa, hannunta ya ruk'o, tuni ta fizge ta cigaba da rera kukanta, kusa da ita ya matsa yad'an rungumota, gaba dayansu wani shock sukaji, turesa tayi da k'arfi, tace "Kaga malam dakata"
YOU ARE READING
PHATEENJIDDAH
ActionYana maganane akan yara guda biyu Wanda suka kasance tagwaye, gashi Allah yayi musu rashin basajin magana ko kadan, sannan kuma ina gargadin iyaye da su runka jan 'yayansu a jiki basu wancakalar dasu ba akan wani dalili nasu na daban,👭