page 12

136 7 3
                                    

*PHTEENJIDDAH*

*MALLAKAR*
*_Ƴar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
 
   *Please Subscribe My Channel*

https://www.youtube.com/channel/UCWyfuDW1EWCBqzOrwaCnq3Q
  Domin kawu muku Audion littattafan Hausa

     
                             12

*MARASA COMMENTS INA GODIYA, AIKO ZAN DAINA POSTING 2 PAGES TUNDA NAGA KAMAR NOVEL DIN BAI MUKU BA*

Tana cikin tunanin ne Umar ya kirata, jiki a sanyaye ta d'au wayar ta kara a kunnanta, sallama tayi tare da gaisheshi, ansawa yayi cike da annashuwa, yanayin yadda taimai maganane yagane akwai abunda ke damunta, "Phaty" ya kira sunanta a hankali, ansawa tayi, yace mata, "Meke damunki?". Murmushi tayi masa tace "maika gani?, nidai gaskiya ba abunda ke damuna", Umar yace "Kin manta a cikin abotarmu babu 6oye komai", ajiyar zuciya tayi tace, "Friend gobe insha ALLAHU zan tafi gida, coz hankalin Sister na ya tashi, tace lallai na koma gida saboda batajin dad'in zaman gidan"

Umar yace "dama akan wannanne kike nema ki tayarmin da hankali?", "Uhmmm" kawai Phaty tace, yace "badamuwa k'arfe nawa zaki tafi goben?, kinga saimu jera tare, dama nima gobe nakeson barin garinnan"

"Kasan inda zanine kake cewa, kaima gobe zaka tafi?"

"Yess of coz, ainima haifaffan d'an kaduna ne". Sosai maganarshi ta bata mamaki, dama yasan garin da take,  "Yadai naji kinyi shirune, karkice mamaki kike don nasan garinmu". Bonewa Phaty tayi tace "A'a, tayaya zanyi mamakin dan kasan mahaifarka".

"Uhmm Phaty kina da wayo sosai, bari na barki haka zan d'anyi wani aikine kafin zuwa gobe na gama, ki shirya kamar k'arfe goma na safe haka, take care byee". Yayi hanging phone d'in, lumshe idanuwa kawai Phaty tayi, sosai take matuk'ar son muryan umar, "komai yasa hakan oho dai", cewar Phaty smilling kawai take idan ta tuna dramar da sukayi jiya, "You are my best Friend" ta fad'a tana k'ok'arin mik'ewa, bathroom ta shiga tayi brush sannan ta canza kaya ta fito, ba wani makeup tayi ba amma tayi kyau sosai, sauka downstair tayi, taga Aunty fa'iza da mijinta sai kuma yaransu, kasancewar yau weekend, taku take tamkar wata hawainiya, bata tsaya a ko inaba sai a wurin dinning table, kujera d'aya taja ta zauna, ta gaidasu, suka ansa ko wannansu fuskarsa a sake, turo baki Phaty tayi tace,
 
    "Naga alama kora da hali akeemin a gidannan, kowa ya tashi,amma ni ank'i tashina ta cikinku kawai kuke". Harararta Aunty Fa'iza tayi taace

"To hamshak'iya, wani irin tashi zan maki, bacin uban buga k'ofar danai maki, ko alamun motsi banji ba balle nasa ran za atashi". gyaran murya mijin Fa'iza yayi, yana k'ok'arin guntse dariyarsa, sannan yace, "Uhumm kun fara ai, banga lokacin da Phaty zatazo gidannan ba bakuyi fad'a ba sai kace ba uwa da 'ya ba"

Aunty Fa'iza tace "Wlh Abban Aarif yarinyaarnan ta rainani sai kace ba uwarta ba, tama maidani wata mate d'inta, wlh ki kiyayeni". Sosai Phaty ta shak'a, shiru kawai tayi, jujjuya abincin kawai take amma takasaci saboda ranta ya6aci, Auntynta ta yarfata, Phaty kallan Fa'iza tayi tace "ALLAH ya baki hak'uri ni ban fad'a da wata manufaba kawai wasa nake maki". Harararta Aunty Fa'iza ta sakeyi tace, "Dole kiyi wasa dani, tunda ni sa'arkice, ki kiyayeni wlh"

Phaty tace "kiyi hak'uri inma kin kwantar da hankalinki gobe iyanzu bazama ki ganni a gidanki ba, inacan na kama hanyar zuwa wurin uwa da uba", tuni Phaty ta tashi domin kuwa sauran kad'an ta fashe, hawa upstair take tana ruwan hawaye, wai Aunty Fa'iza ta yarfata

_Niko nace Ohh su Phaty dama abun kuka bai maki wahala_

Mijin Fa'iza yace mata, "Ba ruwana wlh kin 6atama 'yar gwal d'inki rai, kuma nasan tunda tace gobe zata tafi, to goben fa zaki nemeta ki rasa inma kinci sa'a tai maki sallama"

"Rabu da ita Abban Aarif yau rigima kawai takeji, kuma nasan ta fad'ane ba inda zata saitaimin sati gudan datace"

Girgiza kanshi kawai yayi yace "lallai har yanzu bakisan wannan rigimammiyar 'yar taki ba naga alama, yaka mata ki kai mata break fast d'inta bana tunanin tamaci"

"barta kawai kasan mutuniyar tawa bata fushi da abinci, komai akai mata"
       "Ta huta" cewar Abban Aarif, mik'ewa yayi yace "toni zan fita"

"sai ka dawo ALLAH ya tsaremin kai" cewar Fa'iza. "Amin matata ALLAH ya barmin ke" kiss yayi mata a gefen kumatunta, sannan ta rakasa har bakin motarsa, tare da hugging d'insa da kalamai masu dad'in gaske taimai, Phaty kuwa tana hangosu tace dole Abban Aarif inga baida niyyar k'ara aure alhalin a k'a'idar gidansu daga mai mata uku sai hud'u, shiko anyi-anyi ya k'ara d'aya yak'i, har suna jifan Auntyna da mugayan kalamai, waita asircesa, ashe soyayya take zuba masa da shagwa6a, ga kuma ladabi da biyayya, uwa uba ga iya girki da tsabta, yaushe ko zaiyi marmarin k'aro aure baisan wacca zai aura ba, ajiyar zuciya Phaty tayi tace, "ALLAH ya barku tare ya kareku daga sharrin mak'iya da mahassadanku" juyawa tayi ta koma cikin dak'inta dan d'auko wayarta data keta faman ruri, dubawa tayi taga umar ne, _"yaushe muka gama wayar"_ cewar zuciyarta, d'auka tayi, tai sallama, "Nak'i na ansa sallamar da bazaki d'au wayanba kenan, ina damunki ko"

"please ka daina cewa haka ya za ai nace kana damuna, kafi k'arfin haka a wurina, bana kusa da wayarne kawai"

"Kin tashi lafiya?, d'azu bamu gaisa ba"

"Lafiya k'alau, ya kake?"
   "Ni kamar yadda kike haka nake, ina fatan kinyi break fast"

"Uhmm" kawai tace mai, "kinyi shiru fad'amin abunda kikaci"
   Kamar zatayi kuka tace, " Ni ba abunda naci kuma yunwa nakeji". Sosai hankalin Umar ya tashi, yama rasa mai zaice mata "Wait, mai yasa har yanzu bakici abinci ba, kinason ulcer ta kamaki ne, please ki daina wasa da abinci kije kici yanzu ina jiranki, kinji" magana yake amma duk yabi ya rud'e. "Ni bazanci ba" cewar Phaty, "Mai yasa", duk abunda Aunty Fa'iza tai mata saida ta kwashe ta fad'ama Umar shi tass. Sosai abun ya bashi dariya amma yasan rigimar Phaty, yace,

"Bar auntynnan yau ta 6ata maana rai, me kikeson kici naje na siyo maki?

"Ayya kayi hak'uri ba ko wani abincin restaurant nake ciba ka barshi kawai"

"Uhmm nak'i na barshi bari na dafo maki, saina kawo maki, karfa kici komai, zan kawo maki delicious girkina kiji kona iya girki"

Sosai maganarshi ta bata dariya, tace, "Ina kai ina iya girki, ai girki sai mata,"

"Oh haka kikace you will suprised, bani 1hour kawai, zakisha mamaki" katse wayan yayi, ita kuwa Phaty harga ALLAH tad'au abun da wasa, Jafar kuwa kasancewar yana kusa da Umar yace "tashin hankali yau akwai babban aiki a gidannan, Oga fa ya fad'a makauniyar soyayya, yau zanga girkin 'yan maza a gidannan sosai' abun yaba Jafar mamaki da dariya yau Ogane zai shiga kitchen da kanshi, bama shi zai girkama kanshi ba, mace zaima, Juyawar da Umar zaiyi yaga Jafar nata faman guntsa dariya, had'e rai yayi kamar yana filin daga, yace "Jafar kaje ka siyomin kayan miya yanzu," Jafar ya kasa danne dariyarsa haka ya saketa, yace "Oga ai akwai sauran kayan miya wanda cooker ya siyo rannan, konazo na tayaka girkinne?"

Nannad'e hannun rigarsa yayi yace "bansaka ba ya shiga kitchen". Jafar ya dad'e yana mamaki yau Ogansane da soyayya, "ALLAH yasa ta zame masa tagari, ALLAH yasa ta wanke masa bak'in cikin dayayi shekaru a cikin zuciyarsa, ALLAH yasa tana sonshi kamar yadda yake sonta".
Addu'o'i sosai Jafar yaketa jerowa Ogansa, Umar kuwa a cikin minti talatin ya gama had'a mata break fast, k'amshine kawai ke tashi acikin kitchen d'in, indomie ya dafa mata sai kwai da wani had'in shayi mai d'an banzan dad'i da k'ara lafiya, bud'e cikin fridge yayi ya d'auko mata cake, sannan ya saka a basket food, sannan ya koma d'aki yayi wanka ya shirya ya fito, kallan Jafar yayi yace "bari naje na dawo",
   "Adawo lafiya" cewar Jafar

Tuk'i yake cike da annashuwa, saida yazo daidai bakin get d'in gidansu Fa'iza, sannan yad'au waya ya kirata, yace "Hello, ki fito ina k'ofar gida", yana fadin haka ya kashe wayar, Phaty dai bata yadda cewar yazo ba, amma tace barina lek'a dai ingani, hijab mai hannu ta zura ta saka takalmanta, ta fita, tana bud'e k'ofar gidan sai taga Umar acikin mota, sosai tayi mamakin ganinsa dan ita a iya saninta baisan gidan datake ba, waya ya d'auka, ya kirata, yace mata "ki k'araso mana," ba musu ta k'arasa wurin motar ta bud'e ta shiga cikin motar

PHATEENJIDDAHWhere stories live. Discover now