page 20

100 6 0
                                    

Phaty tsayawa tayi tana kallan wayar, tana cikin kallantane taga sak'o ya shigo, tana dubawa sai taga address d'in Umar, Sosai ta tsaya tana nazari, tana tunanin anya inje kuwa, karfa naje wani abu ya faru nazo ina dana sani, wata zuciyar kuma tace mata, Umar bazai miki komai ba, kawai taimakonki yake nema coz yasan ke likitace, ke kikasan wani irin tablet zai dace dashi a halin yanzu, a zahiri tace "Kai bazan iya zuwa gidan wani namiji ba, duk abunda ya faru dani babu wanda bazaimin ALLAH ya k'ara ba, sannan kuma za acemin dama can haka nake, mutane ba'a iya masu", Jidda da taji abunda Phaty take fad'a tace "Sis keda waye haka?"
    Juyowa tayi ta kalli Jidda sannan Phaty tace "Kinsan bak'on da yazo d'azu ko?"

Jidda ta kalleta tace "Uhumm inajinki, koba Umar ba?

Phaty tace "yawwa shi" duk abunda ya faru tsakaninta da Umar tun daga ranar da suka had'u har zuwa yanzu Phaty ta kwashe ta fad'ama Jiddah.

Ajiyar zuciya Jidda tayi sannan tace "Sis yanzu ya za ai"

Phaty shiru tayi sannan ta mik'a mata wayar tace "Kinga address d'in daya turomin ma, na kira wayarsa yanzu kuma akashe, bansan mai yake nufi dani ba Jiddah"

Shiru Jidda tayi nad'an wasu dak'ik'ai tace "Bari naje na had'a mashi shayi wanda zaiji lemun tsami, ina ganin hakan zai tai maka masa waje ragemai rad'adi, daganan ki duba cikin box aid d'ina ki ciremin wannan tablet d'in nasan zai tai maka masa, zanje coz bansan meke faruwa yanzu , nai mamaki da bai kira Mom d'insa ba, ya kirani, bari nai sauri dan da alama yanashan wahala" cewar Phaty.

Jiddah tace "Shikenan Sister amma dan ALLAH ki kula da kanki, dukda naga alamun yanada kamun kai but kinga a yanayin condition d'in da yake, komai kan iya faruwa dake, kuma kinsan bazanso hakan ba, kuma kinsan nasan koke wacece, shiyasa nake tsoron zuwanki Sis kina da rauni da yawa dan ALLAH ki kiyaye kanki plz"

Dariya Phaty tayi tace "Sis karki damu kanki, komai zai zo da sauki insha ALLAHU, kinji, karki damu ba abunda zai sameni da yardar ALLAH"

Haka Phaty taje ta shirya komai a cikin flask, ta d'au key d'in motarta, ta tafi, Sosai Jidda ta k'ara jaddada mata ta kula da kanta, tace Insha ALLAHU, address d'in taitabi har ALLAH ya kawota gidan, parking motarta tai awaje, sannan ta shiga gidan, shaidawa mai gadi tayi ita bak'uwar Umar ce, sannan ta nemi daya nuna mata part d'insa har k'ofar d'akinshi mai gadi ya kaita, sannan taimai godiya.

Sam Phaty bata lura da Dija ba, wacca har ta gaji da buga k'ofa ta tsugunna, kanta acikin cinyoyinta, Phaty d'aga wayarta tayi ta kirashi sai akaci sa'a ya kunna wayar "Gani ak'ofar d'akinka kazo ka bud'emin" cewar Phaty.

Cikin sassarfa Umar yazo ya bud'e mata, Dija sam hankalinta baya jikinta saida taji an bud'e k'ofa hankalinta ya dawo jikinta, kafin tai wani yunk'urin tashi har Phaty ta shiga Umar ya rufe k'ofar

tashi tayi da k'arfinta ta murd'a k'ofar ta jita gam, batasan lokacin datace "Kutumar uba, tashin hankali wlh bazai yuwuba, dama k'asurgumin d'an iskane, banda labari?, lallai biri yayi kama da mutum, naga alamun duk wanda suke nuna mata basa gabansu ashe sun aje masu kashe masu k'wark'watan idone, kuma wlh bazai yuwu ba, zangani" buga k'ofar ta farayi da k'arfinta, tana kiran a bud'e, kasancewar cikin d'akin akwai tazara mai yawan gaske bama sa juyota.

Umar kuwa tunda yaga Phaty yayi saurin rungumeta, jikinsa sai k'yarma yake, zazza6i mai zafin gaskene ya rufesa, Phaty tanason k'wace kanta amma ba dama, muryarta nad'an rawa tace "Dan ALLAH Umar ka sakeni, magani zan baka"

Idanunsa na runtse yace "plzz ki barni a haka, banajin dad'i ko kad'an cikina kemin ciwo Phaty, cikina da marata"

Sosai Umar yaba Phaty tausayi, tace "To yaka mata mu zauna, bana iya jurar tsayuwa"

Shiru yayi mata sannan yayi mata magana a hankali yace "Mu shiga cikin bedroom"

Phaty kallansa tayi still idanunsa a rufe gabanta ya fara fad'uwa saboda abubuwan da Umar yake mata, cikin rawar murya tace "A'a mu zauna anan, dan ALLAH ka dainamin haka"

Umar bai saurareta ba ya kaita cikin bedroom, jikin Phaty rawa kawai yake tace "Please Umar kaimin alk'awari, dan ALLAH ka bari, ka tsaya ka saurareni"
 
Sosai jikinta ke k'yarma yanayin voice d'inta da yajine ya tsaya, idanunsa suna rufe, zaunar da ita yayi akan gadon sannan shi kuma ya zauna akan cinyoyinta, Sosai yakejin azaba a mararsa, shiru yayi yanata faman cije baki yake, tashi tayi ya runk'o hannunta cikin wata irin kasalalliyar murya yace mata "Ina zakije?"

Kallansa tayi tace "zanje na d'auko maka maganine, na manta dashi a falo"

Umar yace "Noo ki barshi kawai"

Phaty kallansa tayi sosai ya bata tausayi tace "Tayaya zan barshi alhalin kana cikin wannan yanayin?, ka bari na d'auko maka insha ALLAHU zakaji sauk'insa"
zare hannuwanta tayi taje ta d'auko maganin ta dawo, zaunawa tayi akan wata kujera dake kusa da gadon, yace "ki dawo ki zauna anan dan ALLAH"

Jiki ba k'wari Phaty ta tashi ta koma kusa dashi, shayin ta zuba mashi a kofi sannan ta 6allo maganin ta bashi, a hankali tace mai "katashi kasha"

Umar yace "tai makeni, bazan iya tashi ba"

Phaty tallabo kanshi tayi ta bashi maganin, yasha sannan ta bashi shayin shima yasha, sosai yakejin azaba, sannu kawai Phaty take cemai, d'aga mata kai kawai yake
Kwanciya yayi akan cinyarta still baijin yana samun sauk'i, daurewa kawai yayi, a hankali yace ma Phaty "please kimin abunda zan runk'a jin sauk'in ciwona"

Phaty cikin rawar murya tace "Wlh bansani ba, bansan abunda zan maka kaji sauk'i ba, aiba lokaci d'aya ake samun sauk'i ba, ahankali zai sauka........"

Bata k'arashe abunda zata fad'amai ba kawai taji bakinta acikin nashi, Sosai Phaty ta tsorata, hot romance kawai Umar yake mata, jikin Phaty ba k'aramin sanyi yayi ba, ba k'aramin sak'onni Umar yake mata ba, Phaty shiru kawai tayi, amma gabanta ba k'aramin fad'uwa yake ba, shiru kawai tayi, tana ansan sak'onni Umar, a hankali Umar yayima Phaty rad'a yace "Please Phaty"

Muryarta na rawa tace "Umar kar kayi haka, ba haka mukai ba, kasan ahalin yanzu bazan iya hanaka ba coz kasan koni wacece amma dan ALLAH kayi controlling d'in kanka, karka 6atamin rayuwata, bazan yafe maka ba haka kazalika bazan yafewa kaina ba, dan ALLAH Umar"

Sosai muryoyinsa ya jigata, Umar runtse idanuwansa kawai yake, a hankali ya bud'e idanuwansa ba k'aramin ja sukai ba, kallan Phaty yayi yaga itama idanunta sun  sauya kala, a hankali ya bud'e baki yace mata "Ina kaunarki Phaty, karki damu ba abunda zan miki kinji"

"Uhmm" kawai Phaty tacemai, k'ara had'e bakinsa yayi da nata, alokacin Phaty bata hanashi ba, nan take bacci yayi awan gaba dashi, itama batasan lokacin da bacci ya d'auketa ba.

Dija kuwa sai buga k'ofar take har hannunta na zafi amma taji shiru, dad'ewar dataji yayi yawane hankalinta ya tashi, ranta yayi mummunar 6aci, tace "wannan wani irin cin fuska ne da rashin mutunci, yanzu ba abun na fad'awa hajiya ba tace dama na saba irin wannan sakacin, hasalima rufeni zatai da fad'a tace na sata tai asarar kud'inta, dan nasan ba k'aramin kud'i ta saba akan maganinnan, wlh ina nan sai naga wacca tsinanniyarce ta shiga d'akinnan, dama halinsane bin mata bamu sani ba, yau ALLAH ya toni asirinsa........

PHATEENJIDDAHWhere stories live. Discover now