Karanta sak'on yayi, sannan ya rufe wayan, wani k'amshine yaji yana fuzganshi, sosai k'amshin yayi mashi dad'i, bud'e d'akin yayi, yaga ko ina na d'akin fes-fes, yayi mamaki matuk'a dayaga d'akin agyare, dan rabonsa da d'akin yafi wata biyu, ko kad'an ba k'ura acikinsa, bai zarce ko inaba sai cikin bedroom d'insa, kwantawa kawai yayi, da alamun ya gaji sosai, amma har yanzu k'amshin yana fizgansa, k'arar saukar ruwa ya jiyo a bayinshi, nan take ya tashi, a k'ofar bayin ya tsaya yana sauraro, _"tabbas akwai mutum a bayinnan"_ ya fad'a acikin zuciyarsa, murya ya d'aga yadda wanda ke cikin bayin zaiji yace "Waye a bayinnan?"
Cikin barikanci da wani irin salo Dija ta fito daga bayin, ba laifi tayi kyau matuk'a, k'ananan kayane a jikinta sai kuma, gajeran wando, wanda zaka hango har cinyoyinta da sukasha dabbare-dabbare na bleaching, fitowa tayi tana yarfe hannuwa tace "Laaaah yayana saukar yaushe?, wlh d'akinkane naga yayi k'ura shine nace bari nazo na gyara maka kafin ALLAH yasa ka dawo, ashema kana hanya, ai banji motsin mutum ba kwata-kwata, wlh bayi nake wankewa ma"
Kallanta yayi irin kallan kinma rainama kanki wayo, had'e girar sama data k'asa yayi yace "Ubanwa ya baki izinin ki bud'emin d'aki?, bana hanaki yimin wannan uban shishshigin ba?, Khadija ki kiyayeni fa, Oya zoki wuce ki fitarmin daga d'aki kafin na nad'a miki na jaki" Nuna mata hanyar fita yayi da hannunsa
Idanun Dija har sun fara tsiyayan hawaye cikin murya wacce takesonyi kuka tace "Haba yaya mai yasa kakemin irin wannan abunne, dan ALLAH?, daga dawowarka zaka faramin fad'a, aiko ba komai ka nuna kaji dad'in gyaran d'akin danai maka, shine har kana korata akan na shigoma d'aki, dan kaga kullum ina cikin bauta maka, kasan yadda zuciyata ke azabtuwa da sanka amma baka ta6a nunamin kulawa ba ko yayane" share hawayan idanunta tayi tace "Ba komai, aiba laifina bane da nake k'aunarka ALLAH ne ya jarabceni, kuma bai wuce kan kowa ba, amma dan ALLAH duk abunda nai maka ba dai-dai ba kayi hak'uri"
Kallanta Umar yayi nad'an wani lokaci, acikin zuciyarsa fad'i yake _"nasan yarinyarnan tana k'aunata tun tana k'aramarta, na lura tun ba yanzu ba, amma ko kad'an zuciyata bata ta6a santaba koda na mintu biyune, bansan haka so yakeba saida na fad'a cikinsa, na tausaya mata, abu d'aya ke had'ani da ita batada kamunkai ko kad'an ga shegen bin maza kamar karya, sallahma ba wai tadamu da ita bane, takanyi dabi'u tamkar christian, shiyasa jinina da nata bai had'u ba, dukta tafi waccar munafukar yayarta"_
Dija tace "Kayi hak'uri, bansan bakason ina shiga d'akinka ba, amma dan ALLAH ka bari na k'arashe maka wankin bayin please"
Banza yayi da ita ya koma ya kwanta, ita kuwa murna fal cikin ranta hakan yana nufin taje ta k'arashen wankin bayin kenan, kwanciya yayi ya lumshe idanuwa, yana tunanin abar k'aunarsa, Dija kuwa tana wanke bayi tanajin farin ciki, tana da tabbacin yau zata cika burinta, acikin zuciyarta fad'i take, "ko had'a jiki nai dashi aina huta", na samu virgin a bati, Sosai take aiyana irin yanayin da zata ganta tare da Umar, tana gama wanke bayin ta fito, falo taje ta k'ara zuba wannan humra d'in ajikinta, abincin ta d'auko ta zuba wannan maganin a ciki, komawa cikin bedroon d'in ta kumayi, yana nan inda ta barshi, dan ko takalmi bai cireba, ajiye abincin tayi a saman stool, tazo gabdashi zata ciremai takalmi, da sauri ya kauda k'afanshi, yana mata wani irin kallo, yace mata "lafiya?"Cikin in-ina tace "dama naga ka kwanta da takalmi ne, kuma naga bakyau shine nace bari na cire maka"
Harara ya maka mata yace " to alarammiya, nunamin yadda zanyi"
"Kayi hak'uri" ta fad'a cikin muryar ban tausayi, tace "Yaya ga abinci na kawo maka, nasan bai zama dole Aunty ta kawo maka ba, shiyasa nace bari na girka maka best food d'inka"
Umar yace "Na koshi" Sosai turaren jikinta yake kashe mai jiki, amma bai bari ta gane ba.
Dija acikin zuciyarta tace _"tirk'ashi, wlh baka isaba"_
cikin muryarta ta yaudara tace "dan ALLAH yaya kaci, wlh Aunty ta ganni na dawo bakaci ba ta runk'a yimin ALLAH ya k'ara da habaici acikin gidannan, dama tace gwaleni zakai inhar kaine, yanzuma da zanzo yadamin da magana kawai take, dan ALLAH kaci koda spoon gome ne ya wadatar"Tashi yayi daga kwancen da yake yace "Khadija! bazan 6oye miki ba kina takuramin, ke kanki kinsan banason hayaniya, kije kawai zanci koda anjimane"
Dija tace "Yaya dan ALLAH kaci nasan inhar bakaci yanzu ba kona tafi bazakaci ba wlh, nafasan halinka"
Umar yace "Naji mik'omin inci, inba hakaba bazaki bari nai bacci ba"
Cikin zumud'i Dija ta tashi ta d'auko abincin ta mik'a masa, farin cikine fal cikin zuciyarta, tana ganin ya faraci acikin zuciyarta tace, _"aikin gama ya ruga ya gama, aure ba fashi nida kai, kuma har video zanyiwa wacca kakeso tagani, kaga kuwa duk son datake maka dolene ta rabu dakai"_
Sosai Umar yaji abinci yayi mishi dad'i, ci kawai yake baisan lokacin daya cinye gabaki d'aya ba, ruwa yasha, ya kalli Dija daa gaba d'aya idanunta suna kanshi yace "Kinga na cinye, abincin yayimin dad'i sosai , k'anwata nagode ALLAH yabar zumunci"
Dija farin ciki kamar zata shid'e, acikin zuciyarta tace _"Wat a suprise, yau ni yake kira da k'anwarsa, da alamun komai zaiyi dai-dai, kai ALLAH nagode maka daka nunamin wannan rana"_
Magani ya fara yima Umar aiki, dan kuwa shi kad'ai yasan abunda yakeji acikin jikinsa, dak'yar ya kalli Dija yace mata "dan ALLAH kwashe kayannan kikai kitchen, inajiranki kinji"Cikin tafiyarta ta 'yan duniya taje ta tsugunna ta d'iba kayan, yana hango boobs d'inta yayi saurin runtsa ido, ko wacca irin addu'a tazo bakinsa yi yake, yana fatan ALLAH ya rabasa da aikataa zina, Sosai tsigar jikinsa ta tashi da yaga boobs d'inta, yana ganin ta fita a daddafe ya tashi ya sakama d'akinsa key, ya dawo yayi rufda ciki, Sosai mararsa ke ciwo, ya ilahi kawai yace yana runtse idanuwansa saboda azabar dayakeji.
Dija kuwa tana fita waje ta daka tsalle tace komai zaizomin da sauk'i, d'aga wayanta tayi ta kira hajiya ta shaida mata duk abunda ya faru, sannan ta d'ora da cewa "Hajiya wannan magani emergency ne, kinga yadda ya faramai aiki kuwa, yanzu coolern abincin zan aje na koma, nasan komai zai zama daidai, nanda wasu kwanaki na zama matar Major Umar"
Dariya dukaninsu sukai sannan suka aje wayan, cikin sauri ta aje cooler d'in sannan ta koma hanyar d'akin cikin zumud'i ta tafi, tana murd'a k'ofar tajita gam "tashin hankali" ta fad'a da k'arfi, nan fa ta fara buga k'ofar fad'i takee "Yaya kazo ka bud'emin na dawo"
Umar yanajinta yayi banzaa da ita, dan kuwa inhar ya bud'e mata k'ofar akwai matsala, Dija kuwa sai bugu take kamar wata mahaukaciya, Wata zuciya ta Umar hartace kaje ka bud'e mata mana, dama ba 'yar tasha bace, ba wanda zaisan hakan ya faru inhar ka kwa6eta, Umar harya tashi zaije ya bud'e mata sai kuma ya fasa, amma fa ba k'aramin wahala yakesha ba, yana cikin yanayinne Phaty ta kirashi, dak'yar yake iya gani saboda dishi-dishi kawai yake gani, baima san ko waye ba d'agawa kawai yayi, yanajin muryar Phaty yace "Please Phaty ki tai makeni zan mutu, wlh zan mutu" Sosai muryarsa ke rawa, kanajin maganarma kasan ta wahalace
Sosai Phaty ta rud'e tambayarsa take tace "please friend ka natsu ka fad'amin abunda ke damunka"
Sk Umar ya wahala sosai, yace mata "Inajin feelings ne sosai, kuma ban ta6a jin irin yanayinnan ba, Sosai nakejii kamar zan mutu, please Phaty"
Phaty shiru tayi tana nazari tace "Kasha desire tablet ne?
Shiru kawai Umar yayi nad'an wasu dak'ik'ai yace mata "bansha komi ba wlh, ki ije tambayoyinnan please zan turo maki da address d'in dan ALLAH karki k'i zuwa please Phaty"
Kashe wayar yayi ya tura mata da address d'in ya kashe wayar gaba d'aya........
YOU ARE READING
PHATEENJIDDAH
ActionYana maganane akan yara guda biyu Wanda suka kasance tagwaye, gashi Allah yayi musu rashin basajin magana ko kadan, sannan kuma ina gargadin iyaye da su runka jan 'yayansu a jiki basu wancakalar dasu ba akan wani dalili nasu na daban,👭