page 30

111 8 1
                                    

*PHTEENJIDDAH*

*MALLAKAR*
*_Ƴar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
 
 

     
                             30

Umar kallanta yayi sai kuma ya kasa ce mata komai, tashi yayi sannan yace mata "Am sorry, ki shirya kayanki dan yau zamu tafi" fita daga d'akin yayi yaje d'akinsa sallah yayi sannan ya zauna akan gado, tunani kawai yake ya haka ta faru, tayaya ma ya kwanta tare da Phaty ba tare daya sani ba?, ajiyar zuciya yayi yace "ALLAH nagode maka daka kareni daga sharrin shaitan, ALLAH ka k'ara kareni daga sharrinsa" tashi yayi ya fara harhad'a kayansa, yanata tunanin zuci _"Waima Phaty me take nufi dashine dahar take tambayarsa me yayi mata?, ita ala dole nai mata wani abu ko, murmushi yayi yace aida nai miki wani abu da ko motsi baza ki iyaba, ashe har yanzu kee yarinyace bakisan komai ba sai iskancin abaki"_ had'a kayansa kawai yakee idan ya tuna wani abun kuma saiyayi dariya ko murmushi.

Phaty kuwa kalmar da Umar ya fad'a matane ta tsaya mata a zuciya, "To me yake nufi dani dahar zai cemin sorry, kar abunda nake zargi akansa hakane" matse k'afanta tayi tace "kai hakan bazai yuwu ba aida zanji zafi ko yayane" mikewa tayi tanata faman mita "Wallahi Umar saiyasan yayimin rashin mutunci ni zai kartawawa ko, dan yaga na biyosa shine yayimin wannan cin kashin ko" haka dai Phaty taita zabga ruwan tijara ba tare da sanin Umar ba.

Karfe sha biyu daidai jirginsu ya d'aga sai kaduna, suna sauka Phaty taima Jiddah waya cewar tana airpot, Umar ma kiran driver d'insa yayi dan yazo ya tafi dashi, tsakanin Phaty da Umar kuwa babu mai cewa kowa uffan, Umar saidai ya saci kallanta ta gefen idonsa, ita kuwa Phaty sai wani shan k'amshi take.

Basu wani d'au lokaci ba saiga Jiddah tazo, Phaty kuwa tana hango Jiddah tayi sauri zata k'arasa inda take, da sauri Umar ya cafko hannunta yace "Haba Phaty kome nai miki ai baika mata kimin haka ba, tunda muka taho inatai miki magana amma kinyi banza dani, yanzu ma tafiya zakiyi ba sallama?"

Kallansa tayi da idanunta mai matukar rikitashi tace "Naji, yaka mata ka sakinmin hannun karka manta a wajan jama'a muke, koko saika nunawa duniya irin halin naka?"

Umar kallanta yayi yace mata "Shikenan sai munyi waya, please ki kulamin da kanki kuma dan ALLAH karki fad'awa Jidda komai"

Phaty tace "Shikenan, naji, yaka mata ka tafi dan driver d'inka yana kallon duk abunda kakeyi, yaka mata ka kiyaye nan gaba"

Umar sakin hannunta yayi yana mata murmushi mai tsadan gaske yace "Aini inhar akanki ne to kisani komai zan iya, byee and i love you" kiss blowing yayi mata tare da waving yana mata wani irin kallo.

Phaty saita tsinta kanta da rashin jin dad'in rabuwa dashi, kallansa tayi sai taji sanshi yana k'ara ruruwan mata a cikin zuciyarta, murmushi taimai itama ta fara takawa inda Jiddah take, Sosai Phaty taji babu dad'i rabuwarta da Umar, tana zuwa wurin Jidda tayi hugging d'inta itama Jiddah hugging d'inta tayi tana dariya, tace "Mutanan lagos, to ina tawa tsarabar?"

Phaty d'an bugunta tayi a hannu tana cewa "Wani tsaraba, nida kwanana d'aya kawai acan, saidai lagos d'in ta had'u yadda bakya tsammani fa Sis"

Dariya Jidda tayi tace "Wallahi ban yadda ba, wannan ai salon rowane, zamu had'u da Umar d'in shine ya gudu bai tsaya yaban tsarabata bako"

Murmushi Phaty tayi tace "Ke kuma gaki uwar kwad'ayi ko, ni matsa na shiga na zauna dan wallahi na gaji" Phaty tana shiga tana zama sai ta hango Umar yana kallanta tace "Kai dama wannan gayan bai tafi ba?, tome yake jira?"

Jidda itama shigowa tayi tace "Sis kedawa haka?"

Phaty tace "Kalla can, ashe Umar yana nan bai tafi ba"

PHATEENJIDDAHWhere stories live. Discover now