page 51

212 13 6
                                    

*THE END BY THE GOD WILLING*

Dija safiya nayi ta kama kanta a guje tana tafia tana sharbar kuka a haka ta karasa gidansu  ko parking motar batai ba ta fito a guje tana sharbar kuka, bata zarce ko ina ba sai dakin Hajiya Aina'u, babu abunda Dija ta furta sai "Innalillahi wa inna ilayyirraju'un, Aunty me zan gani haka, please ki tashi mana, ki maida harshanki ba a wasa da irin wannan fh, please ki daina irin wasannan" Dija sai sambatu kawai takeyi ganin yadda Auntynta ta canza halitta yanayinta kamar ba nata ba, sautin kukanta ya karu ba abunda Dija take furtawa sai innalillahi wa inna ilayyir raju'un, kuka take tamkar wanda akaima ake da mutuwa, Hajiya Aina'u kuwa tanan nan tamkar wata karya haka ta koma harshenta dukya zazzabo idanunta sun canza kala kamar na mujiya, Dija kuka kawai take nan take ta dau waya ta kira bokansu tuni aka shaida mata ALLAH yayi mai rasuwa, Dija wani sabon kukane yazo mata tana fadin "Shikenan mun shiga uku mun lalace haba duniya yaya zaki mana haka, yaya zaki kwace mana jin dadi a lokacin da mukafi kowa bukatarki wayyoni na shiga uku ni khadija na lalace wayyo ALLAH na, na shiga uku" Haka Dija taita faman ihu da kururuwa, tuni Alhaji ya fado mata babu shiri ta dau wayarta ta kirasa ta shaida masa abunda ke faruwa, cikin tashin hakali ya shaida mata gashinan zuwa.

Jiddah ce kwance a kirjin Dausayi ta lafe sai faman sadda kanta kasa take yayinda shi kuma sai faman zolayarta yake, sosai Jiddah takejin kunyar Dausayi dalilin abunda ya afku tsakaninta dashi, mikar da ita yayi ya dauko break fast dinsu wanda mamansa ta aiko musu dashi ya fara bata a baki cikin so da kaunar juna.

Phaty bude idonta tayi tana hamma taga karfe daya na rana tuni ta tashi tana sallallami tare da saukowa daga kan gadon, kitchen ta dosa dan hada musu lunch, tsayawaa tayi cikin so da kauna tana kallansa yayinda ya dukufa wajan hada musu lafiyayyan lunch, takowa tayi a hankali tai hugging dinsa ta baya tare da manna mai kiss tace "I really lovr yhu my man, love yhu so much ALLAH yabarmu tare"

Juyo da ita gabanshi yayi yaana mata wani tsadaddan kallo yace "Bazan iya biyanki ba, nasan kinmin halacci, dan haka ki sani ni Umar Faruk bazan taba rabuwa dake ba, ina sanki, ina kaunarki, take note"

Tsadaddan murmushi tayi ta manna masa light kiss a kumatunsa tace "Me kake shirya manane?"

Umar ya kalleta kallan so da kauna yace "Ina girkama gimbiyata abunda tafi so da kaunane"

"Uhmm" kawai Phaty tace ta tsaya tana kallon ikon ALLAH.

Kowa shiru yayi yanajin jawabin Dija sbd ance dole saita fada abunda tasani game da Hajiya Aina'u,  Babu wanda yakai Alhaji tashin hankali dan harya fara fita hayyacinsa, dafashi Alhaji Abdul'aziz yayi yace "Cool down, please ka zama namiji, kar hakan yayi tasiri da zuciyarka da lafiyarka, kuma ya zama dole Umar ya kasance a wannan wajan dan al'amarin ya hada hardashi"

Girgiza kai yayi yace mai "Karka kirashi dan ALLAH nida naji shikenan amma dan ALLAH kar a fada mai"

Kawun Alhaji ne ya dafashi yace "Ya zama dole ya sani man, tunda hakkinsa yafi yawa a wannan lamarin kira manashi kace ana son ganinshi da gaggawa"

Ba musu Alhaji ya dau waya ya kira Umar ya shaida masa yazo ana nemansa da gaggawa, nan take Umar ya amsa da gashinan zuwa.

Kallan Phaty yayi wacca take kwance a cinyarsa yace "Bari naje gida na dawo ana kirana"

Marairaice fuska tayi tace "Yanzu tafia zakayi ka barni ni kadai?"

Murmushi yayi yace "Bazan dade ba yanzu zan dawo bansan wabi irin kira akemin ba"

Daga kanta tayi alamun to tace "Please karka dade kaji"

Mikewa yayi yana duba agogon hannunsa yace "Karki damu insha ALLAHU da wuri zan dawo" keys dinsa ya diba ya fice daga gidan, bai tsaya a ko'ina ba sai a harabar gidansu, kai tsaye main palour ya nufa yaga mutane cirko-cirko a dakin, nan take gabanshi yayi mugun faduwa, tsayawa yayi a kofar dakin daddyn Phaty yace "Karaso mana"

PHATEENJIDDAHWhere stories live. Discover now