*PHTEENJIDDAH*
*MALLAKAR*
*_Ƴar Gafai_*
*(Mum Irfaan)**WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
*Please Subscribe My Channel*https://www.youtube.com/channel/UCWyfuDW1EWCBqzOrwaCnq3Q
Domin kawu muku Audion littattafan Hausa
10Usman ne yazo kamar yadda jafar yace mai, ya shiga cikin hotel d'in amma baiga Phaty ba, domin kuwa shima zai ganeta, d'aga wayarsa yayi ya kira Jafar, "Hello ka fad'ama Oga na duba ban ganta ba wlh, kuma har kwatancan inda ake casu anmin amma na dubata babu", Jafar yace, "okey ba damuwa bari na sanarma da Oga d'in". Kashe wayar Jafar yayi, ya shiga cikin bedroom d'in da Ogansa ke kwance yace, "Sorry sir, Usman yace ya duba bai ganta ba haar inda aka shaida mai ana birthday ya duba ba ita". Kwatancan k'ananan kayanta yayi yace ya dubata zai ganta dasu, Jafar d'aukan wayarsa yayi ya kira Usman dan shaida masa abunda Ogansa yace, Haka Usman yayi ta faman shawagi a cikin hotel d'in amma bai ganta ba, haka dai ya k'ara kiran Jafar dan shaida masa shifa baiga wacca sukace mai ba, "Hello", "inajinka" cewar Jafar, "wlh ban gantaba nayi neman duniyarnan amma ban ganta ba, babu mamaki ta tafi gidane, amma tabbas babu ita ba alamunta anan". "Ba damuwa bari na sanarwa da Oga," haka Jafar ya k'ara kutsa kai cikin d'akin ya shaidama Ogansa abunda Usman yace, zumbur ya tashi, yace,
"To ina ta tafi haka Jafar dare fa yayi, kuma gashi yace ba agama partyn ba, batada mota a hannunta, karta fita batasan gari ba wani ya saceta, please kiramin Usman kace ya dawo kawai gani nan zuwa yanzu".
Duk yana maganarne a rud'e, Jafar ne ya dakatar dashi, Oga please kayi hak'uri ka zauna insha ALLAHU ba abunda zai sameta, bari naje da kaina indubata, kaga kai baka da lafiya, ka kwanta kawai bari inje in dawo, wani kallo Umar yayima Jafar yace, "kama rainamin wayo nine akace maka banda lafiya?, ka zauna kai kawai yanzu zan dawo nima ba dad'ewa zanyi ba". 'Daukan key d'in mota kawai yayi, Jafar haryace "Oga amm...", dakatar dashi Umar yayi da hannu "saina dawo" kawai yace mashi ya tada motar, tafiya kawai yake yana tunanin ina heart desire d'insa ta shiga a wannan daren, duba agogon wayarsa yayi yaga k'arfe tara da rabi, furzar da iskan bakinsa yayi yace, "ALLAH yasa tana nan", da tunani kala-kala ya shiga harabar hotel d'in, yana zuwa Usman ya mik'a mashi makullin d'ayar motar yace mai "Zaka iya tafiya".
Tunani kawai yake ta ina zai fara nemanta a wannan dank'areren hotel d'in. Magana yajiyo k'asa-k'asa, har zai tafi kawai saiya juyo yaji wake magana a cikin wannan gurin da daddarennan, kasancewar tana cikin garden, hangota yayi zaune tana waya, amma daka ganta kasan ba wata wadatar lafiyace da ita ba, ajiyar zuciya ya saki mai k'arfin gaske, tare da tsantsan mamakin yadda yaganta a wurin ba a filin rawa ba, kayan jikintane na d'azu, hakanna nufin ko wurin partyn bata jeba, ajiyar zuciya ya k'arayi akaro na biyu yace,
"ALLAH ka shiryamin ita, ALLAH yasa ta fara gane hanyar gaskiya kenan"A hankali yake tafiyarsa kamar bayason taka k'asa, zaunawa yayi kusa da ita, zumbur ta mik'e domin kuwa ba k'aramin razanata yayi ba, zaunar da ita yayi yace, "To matsoraciya zauna nine, naje gun partyn naga bakya nan, na d'auka kinacan kina hutawane da new boyfriend d'inki, in badamuwa yaka mata kizo mu shiga ciki mud'an taka mana".
Kallansa tayi da idanunta kamar maijin bacci, tace "Banda lokacinka yanzu"."Please mana, ki tashi muje mana na d'auka till down zakuyi mana".
Kallansa ta k'arayi tace "bawan ALLAH wai mai yasa kai bakama mutum k'yak'yk'yawan zato ne, please ka daina haka, babu kyau, ka fad'i alkhairin mutum inko akasin haka zaka fad'a to kai shiru kawai, nasan kasan da haka", muskutawa tayi ta gyara zamanta, Umar kuwa kafeta yayi da manyan idanuwansa, sosai yake nazari akanta,
_"tana da 6oyayyan al'amari acikin rayuwarta"_ ya fad'a acikin zuciyarsa, murmushi yayi mata, yace "to maiya kawoki nan?, alhalin acikin gurincan zan ganki amma saikii zauna ke kad'ai""banajin dad'ine", abunda kawai tacemai, sai Umar ya tsinta kanshi da rashinjin dad'in abunda yace mata, matsawa kusa da ita ya k'arayi, ita kuma ta k'ara matsawa, tace
"dan ALLAH ka fad'amin abunda zaka fad'amin batare da kamatso kusa dani ba"
Kallanta yayi sosai yana tunanin acikin zuciyarsa _"anya Phaty batada raunin sha'awa kuwa, wani 6angaran na zuciyarsa yace kai aida tanada raunin sha'awa da tuni tasan maza saboda tana ganinsu kala-kala, wani 6angaran yace aiba abun mamaki bane dan tanada raunin sha'awa ta zama 'yar iska, inhar zata runk'a kare kanta, wani 6angaran na zuciyarsa kuwa cewa yayi ai kuma idan ka lura bata cika mu'amala da maza ba, kodan tanada raunin sha'awane batason yawan kulasu, tabbas kuwa, kawai yace"_ ya dawo daga duniyar tunaninsa Phaty kuwa ta koma gefe ta zauna, tana tunani _"wai mai wannan guy d'in ya d'aukenine haka?, 'yar iska?, kome, inhar zamu had'u burunsa kawai ya ta6ani, ni kaina nasan inada rauni wurin sha'awa banaso yayi galaba akaina, na dad'e ina ajema wanda zan aura pride d'ina, ALLAH kabani ikon kaiwa gidan aurena batare da wani ya6atani ba, ba dan halina ba."_
Tana cikin wannan tunaninne Umar yace _"bari nagwadata ingani da gaskene tanada raunin"_. Kusa da ita ya matsa, lokacin Phaty tanacan ta shiga duniyar tunani hannunta ya ruk'o tana k'ok'arin k'wacewa takasa saboda ruk'one bana wasa ba, murza mata hannun ya fara tare da rungumota sosai yake raftaka mata sak'onni, tuni Phaty ta mik'e jikinta yad'au rawa tace, "wai baka da k'annene?, zakaji dad'i idan akace maka yau k'anwarka akema haka?, wlh tun muna mu biyu kabar gurinnan kafin na tara maka jama'a, kasan jama'a ba wuyan taruwa zasuyi anan ba" Sosai jikinta ke rawa, acikin zuciyarta kuwa fad'i take _"ALLAH gani gareka, ALLAH ka kareni daga sharrinsa a gareni badan halina ba"_ sosai ta tsorata da abunda yayi mata,Umar kuwa kallanta yayi sosai, acikin zuciyarsa yace, _"lallai dole na dakatar da Phaty zuwa irin wurinnan, duk randa akasan tanada raunin sha'awa to za abi hanyar da za a6ata mata rayuwarta"_.Kwantar da muryarsa yayi, yace mata, "kiyi hak'uri wasa fa nake maki wlh, ni harga ALLAH bada wata niyya nai maki hakaba, wasa nake maki, kin manta ni best friend d'inki ne kinsan bazan maki abunda bakyaso ba"
Kallansa tayi shek'ek'e tace "k'aryane wlh akwai wata manufarka atattare dani, kuma ALLAH ya fika"
"Wlh da gaske nake maki wasa nake yi miki, harga ALLAH"
"Tace oho dai kama rantse in k'aryama kakemin kama kanka, kuma banason irin wannan wasa, wasa iskancine, inba hakaba zamu raba jaha, kaji dai na fad'a maka"
"ALLAH ya huci zuciyarki ranki ya dad'e, gashi," ya mik'a mata key d'in motarta da wata zungureriyar letter, tace "wannan kuma menene?".
"Cewa akai na baki key d'in motarkice da kuma apology letter, tun d'azu naga wani soja na nemanki nace ya bani zan baki coz ke sister d'inace"
Tsaki taja tace, "na d'auka ai tsiyar motar suke shiyasa nabar masu" k'wafa tayi tace "wlh da zan kama inyamurinnan na lahira saiya fishi jin dad'i"
Dariya yayi mata yace "me zakima inyamurin haka?", tace masa "sai kaji"
Sosai suka fara hira kamar ba itaba acikin zuciyarsa yace _" she's so simple kamar ban mata laifi ba ALLAH sarki harta manta"_,
"Yadai naji kayi shirune?"
"yaka mata fa kizo ki tafi gida dare nayi"
"To shikenan, nasan aunty fa'iza saitamin fad'a nakai dare"
"aiya kamatama ta zanemin ke wlh"
Dariya taimai tace "aiko dakazo jinya", haka sukatafi sunata hira kamar ba abunda ya had'asu, har inda motarta yake ya rakata, bud'e mota yayi ta shiga, yace "ki kulamin da auntynmu, inkin koma gida mayi waya, kuma inanan zuwa"
Murmushi tayi tace "nagode sai munyi wayar, thanks alot"
Haka tatada motarta yana mata waving harta 6acema ganinsa, shima motarsa ya shiga cike da nishad'i.
YOU ARE READING
PHATEENJIDDAH
ActionYana maganane akan yara guda biyu Wanda suka kasance tagwaye, gashi Allah yayi musu rashin basajin magana ko kadan, sannan kuma ina gargadin iyaye da su runka jan 'yayansu a jiki basu wancakalar dasu ba akan wani dalili nasu na daban,👭