Dausayi kallan Jidda kawai yake cikin so da k'auna, sunzo inda yake, da sauri suka had'a baki wurin gaishehi "Yaya ina kwana?"
Murmushi yayi sannan yace "lafiya qalau"
K'ok'arin shiga ciki suka fara sai Dausayi yace "Phaty d'an tsaya mana"
Cak Phaty ta tsaya dan ta tabbata har yanzu Dausayi bai gane wacce yakeso ba, Jiddah kuwa dariya ta guntse tana k'ok'arin shiga cikin falo d'in, Dausayi kallan Jidda yayi yaga tana k'ok'arin shiga ciki, yace "dake fa nake"
Jidda ko kad'an bama tasan da ita yake ba, itadai tanacan tanama Phaty ALLAH ya k'ara, muryar Phaty ce ta doki dodon kunnan Jidda tace "Ke dalla ana maki magana kina banza da mutune ko, to dake yaya yake manta sunan yayi, yace miki Phaty, Oya dawo nan ku zanta" Phaty ta k'arashe maganar tamkar wacca akai mata bushara da gidan Aljannah,
Jidda tsayawa tayi sororo kamar zatai kuka, tace "tsakani da ALLAH bani bace Phaty bafa, ni sunana Jidda Sis ki fad'a masa mana" kallan Phaty tayi tana sauraran ta bashi amsa, katsesu yayi ta hanyar cewa "To dawa mukayi hira jiya?"
caraf Phaty tace "Wlh da itane"
Jiddah kallan Phaty tayi tace "Sis haka zamuyi dake?, na rufa maki asiri amma kina k'ok'arin tonamin nawa ko?"
Kallan Dausayi tayi, taga ya kafeta da manyan idanuwansa, sosa k'eya tayi tace "wlh yaya nice amma dan ALLAH kayi hak'uri wlh bak'o tayi, kuma nasan idan Mom taji labari zatai mata fad'a sosai shiyasa" ta k'arashe maganar tana sunkuyar da kanta kamar mara gaskiya,
Murmushi Dausayi yayi yace "Phaty jeki abunki, ansamu akasine"
da sauri Phaty tace "Nagode yaya ALLAH ya saka da alkhairi, ALLAH ya barka da jiddo" da biyu Phaty ta fad'a dan ta k'ara shak'awa Jidda.Jidda kallan Dausayi tayi idanunta sun ciko da k'walla tace "Dan ALLAH yaya kayi hak'uri wlh danasan hakane da ban fito ba, amma nai maka alk'awari wlh nabar yi maka shishshigi"
Dariya Dausayi yayi, wadda ta k'ara bayyana k'yawunsa, sannna yace "Karki damu, wlh damacan ke nake nufi ba Phaty ba, ni dama kwatancanki nayi, babu mamaki su Momy basu gane bane shiyasa sukacemin Phaty nima na d'auka a Phatynce, amma harga ALLAH ke nake k'auna, ina fatan zaki kar6eni hannu bibbiyu" ya k'arashe magabar yana fad'ad'a Murmushinsa.Kallansa Jidda tayi kamar zatayi kuka, muryarta na rawa tace masa "dan ALLAH yaya kayi hak'uri da abunda zance maka, amma gaskiya ni yanzu babu soyayya araina, kuma bana tunanin zan kar6eta lokaci guda, ina fatan ban 6ata maka raiba, inna 6ata maka ma dan .
ALLAH kayi hak'uri ka gafarceni."
Kan Jidda a k'asa take maganar dan takasa had'a ido dashi.Murmushi mai ciwo Dausayi yayi sannan yace mata "bai kamata ki yanke hukunci lokaci guda ba, amma kije na baki lokaci duk yadda kika yanke kya sanarmin" juyawa yayi ya shiga ciki yabar Jiddah a wurin, Sosai jikin Jiddah yayi sanyi koba komai Dausayi yana da matuk'ar kirki.
da wannan tunane-tunanenne ta shiga ciki, tana ganin hajiyarsu Dausayi ta tsugunna har k'asa ta gaisheta, sannan tace "Hajiya ina Phaty ta shigane?"
Hajiya tace mata "Tana tare da mufyda, ina Momyn taku?"
Jiddah tace "tanama gaishe dake, gama sak'o tace na kawo maki"
Ansa Hajiyar tayi tace "oh'oh Hajiya Amina bata gajiya dai, dan ALLAH in kunje kuyi mata godiya, sannan kice a satinnan insha ALLAHU ina nan zuwa"
Jiddah tace "To Hajiya, bari na shiga daga ciki",Jidda shiga d'akinsu mufyda tayi tagansu sai hira suke, sallama tayi musu, kawai sai taga Phaty nata zabga mata dariya, tsaki tayi sannan ta zauna tace "Kanki akeji", mufyda kallanta tayi tace "Amaryar big brother, ina kwana?", Harara Jidda ta maka mata sannan tace wlh mufyda zanci k'aniyarki a gidannan, duk wanda ya fad'a maki haka to ki sani shirgagaki kawai yayi" kwantawa tayi, sannan ta cema Phaty "Yawwa Sis in zamu tafi ki d'an tasheni wlh bacci nakeji"
Phaty kallanta tayi tace "Amma wlh Sis baki da kunya a gidan surukan naki zaki kwanta kiyi bacci?"
Banza da ita Jidda tayi, kwanciyarta ta gyara ta kwanta, ba'a d'au lokaci ba bacci yayi awan gaba da ita.Umar sai faman zabga tsaki yake adalilin kiran numbern Phaty da yakeyi not reachable, a hankali ya furta cewar "gashi banda numbern Jidda nasan da zan iya samun rabin raina" anan ya tuna yana da numbern Aunty Fa'iza, bai 6ata lokaci ba ya kirata, gaisawa sukayi, kasancewar yakan kirata su gaisa shiyasa ta gane kowaye, Umar yace ma Aunty Fa'iza "Amm Auntynmu dama numbern Jidda nakeson ki bani, inata kiran numbern Phaty amma bata shiga tun jiya"
Murmushi Fa'iza tayi tace "Shikenan bari in turo maka, daganan kace ma Phaty ba fad'a maiya kawo gaba, tunda ta tafi ba kira"
Umar da sauri yace "Insha ALLAHU, ina jiran numbern"
Tana kashe wayar ba'a jimaba umar yaji k'arar shigowar sak'o hakan ya tabbatar masa da ta turo mishi da numbern, da sauri ya duba , bai 6ata lokaci ba kuwa ya dannawa Jidda kira, wayar na hannun Phaty kasancewar Jiddah tayi bacci, data ga numbern ba suna sai bata d'auka ba, harsai da Umar yayi mata 4misseds calls, ana biyar d'inne ta d'auka tare da sallama, Ajiyar zuciya Umar ya sauke yacema Phaty "nagode, ninasan ba k'yasona, tunda muka rabu jiya baki k'ara nemana ba, na kira wayanki yak'i shiga kwata-kwata"
Lumshe idanuwa Phaty tayi tacemai "I miss you so much, wlh nayi missing d'in sweet voice d'inka, ai tunda muka rabu na kashe wayana gaba d'aya har yanzu ban kunna ba, saboda amins tacemin tana cikin kaduna, so banaso tacemin sai mun had'u shiyasa na kashe wayana, amma dan ALLAH kayi hak'uri kaji sweetheart"
"Uhmm" Umar yace, coz yadda Phaty take kashe masa murya yasa jikinsa yin sanyi, a hankali Umar yace ma Phaty "Baki missing d'ina ba, da kinyi missing d'ina aida zaki nemeni aduk inda nake, yanzu kina ina?"
Phaty tacemai "wlh Momy ta aikemu gidan wata k'awarta but bazamu dad'e ba zamu dawo, akwai labarine?"
Murmushi Umar yayi yace mata "ba wani labari, dama zan fad'a mikine anjima zan hau flight d'in k'arfe Uku inaso na wuce lagos, wlh bansan da tafiyar ba emergency call ne kuma daga gwamnan lagos d'in, kuma muna goodtime dashi, shiyasa nakeson zuwa kuma dama nemansa nake"
Shiru Phaty tayi na wani d'an lokaci, muryarta kamar wacca zatai kuka tace "Yanzu dan ALLAH tafiya zakai ka barni?, ni wlh banaso kanayin nisa, yanzu ka tafi bansan ranar dawowarka ba wlh, kuma sai yanzu ma zaka fad'amin zaka tafi" Sosai muryar Phaty ke, rawa k'iris ya rage ta fashe mai da kuka.
Umar dafe kanshi yayi yace "Nafa fad'a maki cewar wlh tun jiya nake neman numbernki bata shiga, kuma fa bazan dad'e ba, kafin na tafi ai zanzo muyi ban kwana ko"
Turo baki tayi kamar tana gabanshi tace "Shikenan saina ganka" kashe wayan ko wannansu yayi tareda kewar junansu.
Sosai Phaty da mufyda suketa hirarsu, sai wuraren k'arfe d'aya Phaty ta shirya, sannan ta tashi Jiddah "Ke kasa, dalla tashi, kin wani kwanta gidan surukai ko kunya babu"
Tashi Jiddah tayi tana galla mata harara tace "Wlh naga alamun kwana biyunnan ba kekad'ai bace, sai wani sambatu kike, madam saiki jirani na shirya ko"Dukanninsu suka shirya suka fito a falo suka tarad da Dausayi da kuma Hajiya, kan Jiddah a k'asa tace "Hajiya mu mun tafi", kamar ance ta d'aga ido sukayi 4eyes da Dausayi da sauri ta sadda kanta k'asa, suka fita daga falon, sosai Hajiyar take basu sallahun su gaida Momy d'insu sannan suyi mata godiya.
Tafiya kawai sukeyi Phaty sai tsokanan Jiddah takeyi, Jiddah kuwa ta cika ta batse jira kawai take ta fashe, burki kawai naga Phaty taja da k'arfin gaske, Jiddah kuwa har saida kanta ya bugu kad'an. Phaty Ashar ta saki ta kalli titin, mota ta gani ta sha gabansu, Phaty tace "Wannan wani shahararranne haka muna tafiya za'asha gabanmu?"
_to jama'a zanso naga wani shahararranne ta bakin ta Phaty yasha gabansu, to ALLAH yasa ba 'yan kidnapping bane_
YOU ARE READING
PHATEENJIDDAH
ActionYana maganane akan yara guda biyu Wanda suka kasance tagwaye, gashi Allah yayi musu rashin basajin magana ko kadan, sannan kuma ina gargadin iyaye da su runka jan 'yayansu a jiki basu wancakalar dasu ba akan wani dalili nasu na daban,👭